Ticker

6/recent/ticker-posts

Sharhin Littafin Kashin Baki Sai Taro

Na 

ANAS MUSTAPHA

Tambaya

Ɗauki ɗaya daga cikin hanyoyin nazarin littafin zube ka yi nazarin wannan littafi “KASHIN BAƘI SAI TARO” na ɗaya da na biyu.

Gabatarwa

A cikin wannan aiki za a yi amfani da hanyar nazarin gargajiya, za a yi bayani da a kan hanyar nazarin gargajiya kana a ɗauki matakai na yin nazarin wannan hanya da suka haɗa da: gabatar da littafi, da faɗin jigon littafi, da kuma duba salon littafin da kuma duba hali da ɗabi’un taurari. Waɗannan sune abubuwa d azan tattauna a cikin wannan littafi, daga ƙarshe kamala da irin abubuwan da mu kai Magana a kai a taƙaice.

Hanyar Nazarin Gargagiya

A wannan hanya mai nazarin littafin zube kan yi amfani da kayan aikinsa na gargajiya wajen fiɗar littafin zube. Kayan sun haɗa da:

1.     Gabatar da littafi

2.     Jigon littafi

3.     Salon littafi

4.     Zubi da tsarin littafi

5.     Halayen taurarin littafi

Gabatar da Littafi

A wannan aiki zan yi nazarin littafi mai suna “KASHIN BAKI SAI TARO” marubucin littafin shi ne BASHIR AHMAD UMAR.

Dalilin Rubuta Littafi

Wannan littafin an rubuta shi ne bisa dalili na sha’awa da marubucin ke yi na rubuta littafin zube, domin a shekarar da aka rubuta wannan littafi (2012) babu wata gasa da aka sa domin yin wani aiki na rubutun zube, wannan dalili ne yasa muka ce wannan littafi an rubuta shi ne saboda sha’awa.

Jigon Littafin “KASHIN BAKI SAI TARO”

Ma’anar Jigo

Ɗangambo (1981), ya ce jigo shi ne saƙo da abin da waƙa  ta ƙunsa wato abin da waƙa ta ke magana a kai.

Abin da ake nufi da jigo shi ne manufar da littafin ya ke ɗauke da shi, wato irin saƙon da marubucin ke ƙoƙarin sadarwa ga jama’a a cikin littafin na Bashir Ahmad  Umar shi ne “Kashin Baƙi sai Taro…” yana ɗauke da jigo mai nuna tashin tashina (ta’addanci) kamar yadda aka faɗa a zahiran a shafi na 36

“Cikin mutane ya kawo masa wani naushi a ƙahon zuci kafin ka ce me har mai riƙe da jakarnan ya wujijjigata ya jiba a sama sannan kai nan take DCO Zailani ya suma…”

Sannan ya ƙara tabbatarwa a shafi na 74

“An yanke ma Buwaya shari’ar kisa tare da wasu abokansa su huɗu bayan da aka kama su da miyagun laifuka na cin amanar ƙasa”.

Sai a shafi na 78

“Kowannen mu ya san irin kisan da aka yi wa su Buwaye, ba ya tsaya a kansu kaɗai ba ne, nan gaba wajen mu zai zo”

Sannan a shafi na 78

“Ni zan iya sanya shi gidan yari har iyakar rayuwarsa, na tabbata ba zai buwaye ni ba don ko kashe shi ake buƙatar in yi, wannan ba wani abu ne a guri na”.

To idan aka duba waɗannan bayanai na sama suna nuna cewa lallai wannan littafi akwai tashin tashina wato jigon ta’addanci a cikinsa.

Salo

Ma’anar salo: Salo ya na nufin hanyar da aka bi ake isar da saƙon littafi, wato dabarun jawo hankali, da sarrafa harshen Hausa misali amfani da Hausa mai kyau da kalmomi cikin hikima da sauransu.

A cikin wannan littafi mai suna “KASHIN BAƘI SAI TARO” an yi amfani da salailai masu yawa waɗanda suka haɗa da

 

Salon Hira

Wannan littafi ya fara ne da salon hira tsakanin Rufa’i da Jelani, ga abin da suke cewa a shafi na 8

“Ai da farko na ɗauka ba zan same ka ba a gida, shi yasa ban yi saurin wucewa ɗaki ba, a nan sai suka gaisa da juna sannan suka nufi cikin ɗakin”

Salon Aron Kalmomi

A wannan littafi akwai aron kalmomi a cikinsa musamman kalmomin harshen Ingilishi, misali;

1.     D.C.O

2.     N.D.L.E.A

3.     Suzuki

4.     Cambridge

5.     Cocaine

6.     Heroine

7.     Computer

8.     Beirut

9.     Honda accord

 

Salon Zayyana

A nan za a ga inda marubucin wannan littafi ke ƙoƙarin kawo hoto a shafi na 17

“Lokacin da Jelani ya hau babur ɗin, sai Rufa’i ya tuƙa su suka nufi unguwar sabon gari da yake nan ne shiyar da gidan su Ummul Kulsum yake”   

Akwai salailai da dama waɗanda ban ambace su ba a cikin wannan littafi kamar salon ba da labari, adon magana da dai sauransu.

Zubi da Tsari

Wasu manazarta sun fi son a ƙira shi da tsari kawai, ya kuma waɗannan abubuwa kamar haka:

a.    Buɗewa da Rufewa: Wannan littafi ya fara da hira don haka marubucin ya buɗe labarin da shi a tsakanin Rufa’i da Jelani.

Ya kuma rufe littafin da godiya ga Allah inda yake cewa “Alhamdulillahi Rabbil Alamin”. Wannan shi ne ƙarshen labarin.

b.    Yawan Lambobin Littafi: wannan littafi ya na da yawan shafuka 152 in aka haɗa shafukan littafi na ɗaya da na biyu.

c.    Dabarun Ƙulla Labari: wannan marubucin littafin ya yi ƙoƙari wajen ƙulla labarinsa inda ya fara tsakanin Rufa’i da Jelani yana cikin yin hira da su ya saki ya koma kan ba da labarin kamanin Rufa’i da kuma karatun da ya yi da kuma neman aiki da yake yi, daga nan ya tafi kan zuwan wata budurwa Haizarani a ɗakin da su Rufa’i suke. Sannan ya ci gaba da ba da labarin kyawun da Haizarani ta ke da shi daga nan ya ci gaba da ƙulla labarinsa kan fataucin haramtattun miyagun ƙwayoyi da wasu ‘yan ta’adda ke yi, haka ya tafi da labarinsaa babu wani kwan gaba kwan baya. Don haka nema nake ganin wannan littafin yana ɗauke ne da miƙaƙƙen salo.

d.    Tsarin Babi-Babi: Wannan littafin marubucin ya yi amfani da tsarin babi-babi wajen rubuta shi ba kara zube kawai ya rubuta shi ba.

e.    Halaye da Ɗabi’un Taurari: Salin halin taurarin cikin littafin abu ne mai kyau domin zai taimaka wajen gane jigon littafi a cikin sauƙi. Wannan littafin yana da taurari kamar haka:

i.                   D.C.O Jelani: Shi ne babban tauraro a cikin wannan littafi kuma ya fito a matsayin jami’in hana sha da fataucin miyagun ƙwayoyi wanda ya yi gwagwarmaya da su har ya kawar da su.

ii.                 Alhaji Salisu: Ya fito a matsayin shugaban ‘yan ta’adda wato dilan ƙwayoyi da fataucin su.

iii.              Haizarana: Ta fito a matsayin budurwa wadda ba ta son Jelani amma daga ƙarshe sai da ta aure shi saboda tsabar son da ta dawo ta na yi masa.

iv.               Rumaisa’u: Ta fito a matsayin budurwa ƙawar Haizarana kuma sun yi soyayya da Jelani har ya aure ta.

v.                 Buwaya: Ya fito a matsayin babban yaron Alhaji Salisu shugaban ta’addanci.

vi.               Farancoise: Ɗan ƙasar Nemanki ne ya kasance ɗan leƙen asirin abin da Alhaji Salisu ya ke aikatawa.

vii.            Ɗan jimma: Wato ya fito a maigadin gidan su Haizarana.

viii.         Alhaji Ibrahim: Ya fito a matsayin mahaifin Haizarana.

ix.               Halen Christoper: Wato Hajiya Balkisu a yanzu wadda ta fito a matsayin matar Alhaji Ibrahim.

Kammalawa

A wannan littafi na yi amfani da hanyar gargajiya wajen yin nazarinsa wato (Traditional Approach) inda aka yi nazarin littafin zube, inda aka ɗauki littafi guda biyu wato na ɗaya da na biyu mai suna “KASHIN BAƘI SAI TARO” na Bashir Ahmad Umar inda aka yi amfani da matakai biyar (5) wajen yin nazari a kansa, sai kuma jigon littafin da salon littafin kana aka duba zubi da tsari da halayen taurarin cikin littafin. Wannan shi ne abin da aka tattauna a cikin wannan aiki.   

Manazarta

Atuwo, A. A. (2017). ALH 406: Contemporary Hausa Prose. Laccar aji wanda aka gabatar a Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar Usmanu Danfodiyo Sakkwato.

Umar, B. A. (2012). Kashin Baƙi Sai Taro 1, 2, 3. Kano: Gidan Dabino Publishers.

www.amsoshi.com

Post a Comment

0 Comments