Ticker

6/recent/ticker-posts

Jini Ya Zo Min Kamar Na Haila

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam Inada tambaya Inada ciki Kusan wata ɗaya sai kwana huɗu da suka wuce sai jini ya zoman kamar na haila Toh a tunani dai may be nasamu miscarriage ne shin zan cigaba da ibada nane koh kuma zan tsaya Har sai ya tafi, Na gode

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullah.

Mutukar dai kin tabbatar jinin ɓari ne, to wannan ba zai hanaki sallah ko azumi ba, tunda cikin bai kai abusa masa rai ba, kuma bai fito da siffar Ɗan Adam ba. Wato bai wuce gudan jini ba.

Malaman Fiqhu na Mazhabin Malikiyyah sun tafi akan cewa mace mai ciki tana iya yin haila amma idan cikin yakai watanni uku kamar yadda yazo acikin littafin "ATTAJU WAL IKLEEL 'ALA MUKHTASARI KHALEEL" (Juzu'i na ɗaya shafi na 543). Da kuma AL MISKUL AZFARIY shafi na 160.

To amma naki bai kai watanni uku ɗin ba, don haka jinin rashin lafiya ne, mutukar dai kin tabbatar kina da cikin  to wannan alamar ɓarewarsa ne.

Duk da cewa Malamai sunyi saɓani game da hukuncin jinin ɓarin da bai kai watanni uku ba, to amma wannan ita ce fatawar da tafi Qarfi. Wato za'a ɗauki wannan jinin amatsayin jinin Istihadha kenan.

Kuma Matar dake cikin jinin rashin lafiya, hukuncinta kamar hukincin mai yoyon fitsari ne. Idan lokacin sallah yayi zaki je ki wanke jikinki sannan ki canza Kunzugu kiyi alwala kiyi sallah.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat.whatsapp.com/Du5LNx31U9hDi6RƘbbrzgW

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments