𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamun alaikum. Allah ya kara lafiya, ya saka muku da mafi alkhairi. Tamabya ta anan shine game taya Christian murnar chrismas, da cin yankan su, menene matsayin hakan a Jafariyya?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Alaikas-salam wa rahmatullahi
Ta'ala wa barakatuhu wa magfiratuhu wa ridhwanuhu. Ilaahiy amiin yaa
Rabbal-aalamin shukran.
Abinda Malamai suka ce akai akan
Kirsimeti
1. Ba ya halasta yin Barka ga
Ma'abota Littafi na daga Yahudawa da Kiristoci da wasunsu, hakanan da waɗanda ba masu Littafin ba
daga Kafirai, akan Munasabobin da suke bikinsa kamar: Bikin farkon Shekara na
Haihuwar Annabi Isa, da Kirsimeti da sauransu.
2. Ba ya halasta cin nama sai
wanda aka yanka, kuma yankan baya inganta daga wanda ba Musulmi ba har wanda
yake Ahlul-kitabi koda ya kira sunan Allah abisa Ihtiyaɗi na wajibi – Ahlul-kitabi sune: Yahudawa,
Kiristoci da sauran waɗanda
aka sauko musu da littafi daga Allah – hakanan ma wanin Ahlul-Kitabi ba ya
inganta koda ya yanka da sunan Allahn kwata-kwata.
3. Naman da Ahlul-kitabi suka
yanka baya halasta a ci.
4. Halarta bikin Kirsimeti yana
halasta ne idan ya kasance babu ƙarfafa Kafiri da Fasiƙanci
da kiɗe-kiɗen da suka haramta ne a
cikinsa.
5. Idan ya kasance babu ɗaya daga cikin abubuwan da
suke katange halarta wajen taron na Kirsimeti da waninsa to wajibi ne kiyayewa
wajen kada a ci ko a sha abubuwan da suke Haramun ne a Musulunchi.
WALLAHU A'ALAM
Amsawa: Sayyid Nuru Darut-thaƙalaini
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da
Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.