Ticker

6/recent/ticker-posts

Dafaffen Dankali Da Sauce Din Kwai

Dafaffen Dankali Da Sauce Din Kwai

 Fitattun Kayan Haɗi

* Dankali

* Kayan Miya

* Man Gyaɗa

* Albasa

* Kayan Ɗanɗano

* Kayan Ƙamshi

Lura: Waɗannan fitattu ne kawai daga cikin kayan haɗin. Ana iya samun sauye-sauye (daɗi ko ragi), wanda hakan ya danganta ga salo da ra'ayin mai girki.

1- Za ki dafa dankalinki daban ki ajiye a gefe bayan ya dahu.

2. Ki ɗora tukunya a kan wuta ki saka mangyaɗa, ki saka ginger and garlic da albasa har sai sun fara kamshi, ki kawo jajjagen tattasai da albasa da attarugu ki saka,ki saka magi daidai ki saka thyme da curry, ki saka gishiri ɗan kaɗan. ki gauraya ki rufe su soyu, sai ki kawo ƙwai da kika fasa  kika yanka tumatur kaɗan a ciki ki zuba a ciki ki rufe sai ya dahu sai ki gauraya shi sosai ya kama ko ina, ki kawo dankalinki ki zuba a ciki ki gauraya sosai ya hade, ki ba shi kamar minti ɗaya sai ki sauƙe. shikenan.

A ci daɗi lafiya.

Daga:

Ummu Amatulqahhar Kitchen 
(Humaira'u)


Post a Comment

0 Comments