Ticker

6/recent/ticker-posts

Dalilin Da Ya Sa Ake Son Musulmi Ya Canza Hanyar Tafiya Masallachin Idi ?

TAMBAYA (92)

Me ya sa ake son musulmi ya canza hanyar tafiya masallachin idi

AMSA

Alhamdulillah

Tun muna kananan yara, iyayenmu suke ce mana mu daina dawowa ta hanyar da muka bi yayin zuwa masallachin idi, karancin ilimi yasa bamusan hikimar aiwatarda hakanba

An karbo hadisi daga Jabir Ibn Abdullah RTA yace: A ranar idi, Annabi SAW ya kasance yana canza hanyarsa ta zuwa masallachi (Duba hadisin a cikin Sahihul Bukhari mai lambata 986)

Ulama'u magada Annabawa sunce dalilan hakan sune

Domin firta zikirin "Allahu Akbar ! Allahu ! Allahu Akbar ! La'ilaha illallahu Allah Akbar ! Allahu Akbar walillahil hamd" ta yanda munafukai da yahudawa zasuyi bakin ciki sannan kuma hakan zai sa su tsorata silar ganin dandazon adadin yawan musulmai masu halartar sallar idi domin bautawa Allah SWT

Sannan kuma dalili na biyu, domin taimakon mabuqata idan ka sauya hanyar dawowa ka iya haduwa dasu ka taimaka musu, ka koyardasu sunnar ma'aiki SAW sannan kuma ka ziyarci yan uwa da abokan arziqi wanda hakan zai kara danqon zumuncinku

Dalili na uku shine, domin kasar da muke takawa tayi mana shaida a ranar tashin alqiyama cewar mun bi ta kanta yayin sallatar idi saboda a ranar lahira, kasar da muke takawa zata yi shaida akan wajen da muke zuwa, ko dai wajen sabawa Allah ko kuma wajen bautawa Allah, kamar yanda Allah ya fada a cikin Suratu Az-zalzala

( إِذَا زُلْزِلَتِ الْأَرْضُ زِلْزَالَهَا ) (1)

Idan aka girgiza ƙasa, girgizawarta

( وَأَخْرَجَتِ الْأَرْضُ أَثْقَالَهَا ) (2)

Kuma ƙasa ta fitar da kayanta, masu nauyi

( وَقَالَ الْإِنسَانُ مَا لَهَا ) (3)

Kuma mutum ya ce "M neya same ta?"

( يَوْمَئِذٍ تُحَدِّثُ أَخْبَارَهَا ) (4)

A rãnar nan, zã ta faɗi lãbãrinta

( يَوْمَئِذٍ يَصْدُرُ النَّاسُ أَشْتَاتًا لِّيُرَوْا أَعْمَالَهُمْ ) (6)

A rãnar nan mutane za su fito dabam-dabam domin a nuna musu ayyukansu

( فَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ خَيْرًا يَرَهُ ) (7)

To, wanda ya aikata (wani aiki) gwargwadon nauyin zarra, na alheri, zai gan shi

( وَمَن يَعْمَلْ مِثْقَالَ ذَرَّةٍ شَرًّا يَرَهُ )

 (8)

Kuma wanda ya aikata gwargwadon nauyin zarra na sharri, zai gan shi

Allahu Akbar ! Duk abinda Manzon Allah SAW ya koyar to tabbas da akwai hikima saidai ko dai ilimin mu bai zo wajenba ko kuma bamu bincika ba

Imam Ahmad bin Hanbal, At-tirmidhi, Abu Abdurrahman, Nisa'i duk sun rawaito hadisi daga Abu Hurairata RTA (A ruwayar An-Nisa'i) yace: Annabi SAW yace: "a ranar nan, za ta fadi labarinta", sai yace: ko kunsan menene labarinta, sai (sahabbai) sukace: Allah da manzonsa ne mafi sani, sai yace: "labarinta shine, zata gasgata kowanne namiji da mace, akan abinda sukayi bisa doronta. Kasar zatace wane yayi kaza da kaza a ranar kaza da kaza. To wannan shine labarinta" Tirmidhi yace: wannan hadisin Sahihi ne Gharib (Tafsir Imam Ibn Khathir, Rahimahullah)

A cikin yayan Annabi Adam AS samada biliyan 7, da a qiyasce suke a raye a duniyarnan ta Ard, Allah ya qaddara kana cikin musulmai biliyan 2, wadanda su ka kammala Ramadanan 1445, kuma suke sa ran ganin karamar sallah da rai da lafiya. Ina tayaka/ki murnar samun yalwataccen lokacin istigfari la'akarida wasu basu ga wannan ranar ba. Taqabbalallahu minna waminkum. Ya Allah ka yafe mana zunubbanmu ka maimaita mana sannan ka amshi ibadunmu

Turawa yan uwa musulmai domin mu amfana da ladan tunatarwan baki daya

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa

Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

 https://t.me/TambayaDaAnsa

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments