TAMBAYA (89)❓
As salami Alaikum, malam tambayata itace mutum xai iya
karanta littafin novel kokuma babu kyau
AMSA❗
Waalaikumussalam, warahmatullahi, Wabarakatuhu
Alhamdulillah
Novel, kamar yanda turawa suka fada a dictionary, shine
abinda suke kira da kirkirarren labari wanda tsayinsa yafi gajerun labarai
Ma'ana: shi novel karyace (fictional story) da ake kirkira
don a tsara labarin da zai ja hankalin mai karatu
Yawancin malamai sunce karanta Novel bata lokaci ne musamman
la'akari da cewar labaran karya ne a ciki kuma bai dace ga cikakken musulmi mai
imani ya kyale Qur'ani da sauran littattafan addini a gefe guda sannan ya
shagala da karatun da bazai amfanar dashi ba
Idan labari kike son ji to ki karanta Qur'ani domin kuwa
kashi daya Tauhidi ne, kashi daya Shari'ah ce sannan kuma daya kason labarai ne
don su zamo darasi a garemu
Ga ladan karatu (na kowanne harafi lada 10 ga kuma sanin
ilimin dake cikinsa - wanda kowanne ilimi akwai shi a cikin Qur'ani)
A shawarce; ki maida hankali wajen karatu, fahimta da
tadabburi a cikin ayoyin Qur'ani mai girma, ki duba hadisai, ki karanta
littattafan hukunce hukuncen jinin mata (Haila, Istihada, Nifas), ki gyara
yanda zaki bautawa Ubangijinki ta hanyar karantar Siffofin yanda Annabi
Sallallahu alaihi wasallam yake sallah (Sifatus Salatin Naby na marigayi
Nasiriddin al-Albany), ki karanta littafin aqidah, ki duba littafin Hisnul
Muslim domin fa'idantuwa da addu'o'in yau da gobe
Amman yawancin Novels idan kina karantasu babu abinda zasu
kara miki sai buri da son cimma matsayin wata da ta burge ki a cikin labarin,
hakan kuma zai iya kaiwa ga rashin godewa ni'imar da Allah ya baki, kuma
yawancin littattafan Novels akwai kalaman batsa a ciki wadanda bai kamata ace
musulma tana karantawa ba tunda shi ji, gani da zuciya duk ababen tambaya ne a
ranar Alqiyama kamar yanda Allah Azzawajallah ya fada;
(إِنَّ
السَّمْعَ وَالْبَصَرَ وَالْفُؤَادَ كُلُّ أُولَٰئِكَ كَانَ عَنْهُ مَسْئُولًا
)
الإسراء
(36) Al-Israa
"...Lalle ne jĩ da gani da zũciya, dukan waɗancan (mutum) yã kasance
daga gare shi wanda ake tambaya."
Akwai wata daliba ta da na ga tana karanta Hausa Novel, ina
musu lecture ita kuma Novel yana koyar da ita, kanta a sunkuye a kasan benci,
naje na amshe littafin, na ga duk kalamai ne wadanda bai dace ta bata lokaci
tana karanta su ba. Don na nunawa sauran daliban maza da mata illar karanta
Novel din sai na ce ta fito ta karanta, kasawa tayi. Nace, wannan shine illar
karanta Novel, iyayenki sun turo ki don ki karanta Chemistry, Physics, Biology
amman kin bige da karanta Kishi kumallon mata kashi na 1, na 2 da na 3
To kema irin dai shawarar da na bawa dalibar can ta wa, ita
zan baki: kada ki kuskura ki karanta abinda zai sa kiyi da na sani a rayuwarki.
Shi lokaci tsada ne dashi
Wannan shine shawarar da zan baki a matsayinki na yar uwa ta
musulma
Wallahu ta'ala a'alam
Amsawa
Usman Danliti Mato (Usmannoor_Assalafy)
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.