Takardar da aka tura wa Biram Journal Of Contemporary Research In Hausa Studies, Sule Lamiɗo University, Kafin Hausa, Jigawa State, Nigeria.
ZUGA TUBALIN GINA SIYASA: TSOKACI DAGA WAƘOƘIN SIYASAR ZAMANI
Daga:
ALIYU RABI’U ƊANGULBI
JAMI’AR TARAYYA GUSAU
GSM NO. 07032567689
0R 07088233390
EMAIL: aliyurabiu83@gmail.com
TSAKURE
Waƙa aba ce mai muhimmancin gaske a fagen isar da saƙo cikin hanzari ga al’umma. Ana amfani da ita wajen yaɗa manufofi na kowane fanni na rayuwar
yau da kullum, cikinsu har da harkokin siyasa. Wannan maƙala mai take, ’
Zuga Tubalin Gina Siyasa: Tsokaci daga waƙokin siyasar
zamani, ’za ta tattauna a kan gudummawar da zuga
a cikin waƙokin siyasa yake takawa ga gina siyasa
a Nijeriya. Mawaƙan siyasar zamani mutane ne da ke
amfani da damarsu wajen yaɗa manufofin jam’iyyun siyasa da ‘yan
takara domin faɗakar da al’umma a kan muhimmancin zaɓen shugabanni nagari. Zaɓen mutanen kirki
shi ne tubalin gina siyasa a tsarin mulkin farar hula, wato siyasa. Salon zuga da
mawaƙa ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu, wata dabara ce ta jawo hankalin ‘yan siyasa da sauran al’ummar ƙasa baki ɗaya, su fahimci irin tasirin da shugabanci nagari ke yi ga gina siyasa mai ɗorewa a ƙasa. Shugabanci nagari, wanda shi ne tushen samun zaman
lafiya da ci gaban tattalin arziki da adalci tsakanin masu mulki da waɗanda ake mulka. Wato,
zuga dabara ce da mawaƙan siyasa ke amfani da ita domin su
harzuka ‘yan siyasa su nemi tsayawa takarar kowace kujera ta siyasa; don a
fafata da su ko da kuwa ba su cancanta ba. Saboda haka, wannan takarda za ta
mai da hankali ne ga nazarin gudmmawar da zuga ke bayarwa wajen kambama ‘yan
siyasa da shugabanci da jam’iyyun siyasa da ‘yan takara da hana maguɗin zaɓe da ha’inci ko
cin hanci da rashawa da ke yi wa siyasar zamani barazana a Nijeriya. Wato, takardar
za ta tattauna a kan muhimmanci kyawawan ɗabi’u da gaskiya da riƙon amana waɗanda ke haifar da samuwar mulkin adalci
da gina siyasa ɗorarriya a ƙasa.
1. 0 Gabatarwa
Kyawawan ɗabi’u da nagarta
su ne abubuwan da suke ƙoƙarin zama tarihi a
siyasar Najeriya. Wannan dalili ne ya sa ‘yan siyasar zamani suke kutsa kansu a
siyasa ba tare da sun kyautata halaye da ɗabi’unsu ba. Dangane da haka ne, sai
mawaƙan siyasa suka sami damar yin amfani da
salon zuga domin su kambama kowane ɗan siyasa da ya nuna ra’ayinsa ga
tsayawa takara, ko da kuwa ba shi da ɗabi’u nagari; matumƙar dai yana da abin hannunsa, (Ɗangulbi: 2003). Yin haka ya saɓa wa tsarin siyasa ta gina ƙasa. Saboda haka matuƙar ana son siyasa ta gina ƙasa, dole mawaƙan siyasa su mai da hankali wajen Zuga mutane masu ɗabi’u nagari domin
su tsaya takara don a sami kyakkyawan mulkin siyasa. Don haka, zuga wani salon
kambamawa ne, ko ingiza ‘yan siyasa su yi gogayya da shahararrun ‘yan siyasa a
fagen neman kowane muƙami na siyasa. Mawaƙan siyasar zamani suna amfani da shi domin su cusa wa matasan
‘yan siyasa son shugabanci. Mawaƙan siyasa suna
amfani da zuga domin su jawo hankalin ‘yan siyasa da sauran al’umma su zaɓi mutanen da za su
iya kawo wa ƙasa ci gaba a siyasance.
1. 1 Manufar Bincike
Gurin wannan maƙala shi ne ta faɗakar da al’umma game da gudummawar da
zuga yake bayarwa wajen gina siyasa mai ɗorewa a Nijeriya. Manufar gudanar da
wannan bincike ita ce, a nazarci yadda zuga da mawaƙan siyasar zamani ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu yake da muhimmanci wajen wayar da
kan al’umma. Saboda da haka ƙudurin wannan muƙala sun haɗa da :
a. Gudummawar da zuga ke bayarwa wajen
jawo hankalin ‘yan siyasa su kasance masu gaskiya da riƙon amana.
b. Yadda zuga yake taimakawa wajen
tallata manufofi da aƙidun kowane dan takara cikin waƙoƙin siyasar zamani.
c. Harzuƙa ‘yan siyasa su jajirce wajen fuskantar
kowane irin kalubalen siyasa da ka iya yi masu barazana ga siyasarsu.
d. Nazarin saƙon da zuga yake ɗauke da shi cikin waƙoƙin siyasar zamani da nufin fito da
tasirinsa wajen gina siyasa mai ɗorewa.
1. 2 Tambayoyin Bincike
A tsarin gudanar da kowane irin bincike, ana tsara
tambayoyi ne domin su zama jagora ga mai bincike wajen samar da ingatattun
bayanai da suke da alaƙa da wannan binciken. Daga cikin
tambayoyin wannan bincike akwai:
a. Wace gudummawa ce zuga yake bayarwa
wajen gina kyakyawar siyasa. ?
b. Ko zuga ya taimaka wajen tallata
kyawawan ɗabi’un ‘yan siyasa da manufofinsu?
c. Ko zuga ya taimaka wajen harzuƙa ‘yan siyasa wajen tsayawa takara?
d. Wane muhimmin saƙo ne zuga yake ɗauke da shi zuwa ga al’umma dangane da
gina siyasa mai ɗorewa?
1. 3 Ma’anar Zuga
Zuga wata magana ce, wadda mawaƙan Hausa na baka ko rubutacciya ke amfani da shi domin su
ingiza ko harzuƙa wani mutum ya aikata wani abu wanda
ba zai iya yin sa ba, idan yana cikin hankalinsa. Wani lokacin kuma, zuga yana
nufin kambama wani mutum ya ji cewa ba wani mutum da ya kai shi ƙarfi ko hazaka ko dukiya ko daraja ko kyauta a duniya. Zuga
ya samo asali daga zuga-zugi da makeran gargajiya ke amfani da su wajen hura
wuta a maƙera, domin su gasa ƙarfe ya yi ja da laushi kafin a sarrafa shi zuwa wani
abin amfani. Ana sarrafa baƙin ƙarfe zuwa wasu abubuwan amfani da suka haɗa da kwashe, da wuƙa da galma da sauran kayan amfanin gida da gona. Yadda
ake amfani da zuga-zugi a hura wuta a maƙera har ruru ta
gasa ƙarfe ya yi ja, haka zuga da ake yi wa mutum
kan harzuƙa wanda aka yi wa, ya kumbura ya aikata
wani abin bajinta ko akasin haka.
1. 4 Asalin Kalmar Zuga
Kalmar zuga ta samo asali daga
zuga-zugi da maƙeran gargajiya suke amfani da su wajen
hura wuta, su gasa karfe ya yi ja, kafin su sarrafa shi zuwa wani abin amfani
kamar kwashe ko galma ko wuƙa da sauransu. An
sami wannan bayani daga Salisu Zakari, (sarkin maƙera Bagega), ƙaramar hukumar mulki ta Anka, jihar
Zamfara. Ya ƙara da cewa zuga-zugi wasu fatun awaki
ne da ake jemewa a ɗinka su kamar jikuna da baki wanda ake
liƙa masu kwarkwaron ƙarfe domin ya ba da iska kai tsaye ga ramin maƙera. Hausawa sun aro wannan kalma daga waɗannan fatun awaki
da ake kira zuga-zugi, suka riƙa amfani da ita a
cikin maganganunsu na yau da kullum. Haka kuma a cikin waƙoƙin Hausa ana amfani da kalmar domin a
harzuƙa mutum ya aikata wani abin bajinta ko
wani abin alheri ko akasin haka.
Mawakan Hausa, musamman na siyasa suna
amfani da zuga a cikin wakokinsu domin su kambama ‘yan siyasa su ji cewa sun fi
sauran mutane kwarjini. Wato, zuga wani salo ne da mawaƙan Hausa ke amfani da shi wajen jawo hankalin mutane su fahimci wani saƙon da ake son su sani game da wanda ake zugawa. Masana da
manazarta sun tofa albarkacin bakinsu wajen bayyana ma’anar kalmar zuga. Bergery,
(1934), da Oxford Dictionary (9th edition) da Bunza (2009), dukkansu sun yi
ittifaƙi da cewa, zuga wata magana ce da ake
furtaw domin a harzuƙa ko a kambama wani mutum ya aikata
wani abu da ba zai iya aikatawa ba, idan yana cikin hayyacinsa. Bunza ya ƙara da cewa, zuga da kirari tamkar ɗan juma ne da ɗan jumai wajen
taka muhimmiyar rawa a fagen isar da saƙo. Ya ƙara da cewa, idan zuga ya amshi sunansa, dole ne a ji
amon kalmomin yabo a cikinsa, domin zuga wata dabara ce da mawaka ke amfani da ita
a cikin waka ta hanyar ambaton wasu kyawawan ɗabi’u da ayyukan
bajinta da iyaye da kakanni suka aikata domin su isar da saƙo ga masu sauraren waƙoƙinsu.
A taƙaice zuga wata magana ce, wadda ake furtawa zuwa ga wani mutum domin a
harzuƙashi ya aikata wani abu da ba zai iya
aikata shi ba, matuƙar yana cikin hankalinsa. Mawaƙan siyasa suna amfani da zuga a cikin waƙoƙinsu wajen kambama ‘yan syasa su ji cewa suna iya fafatawa da kowane mutum a
fagen neman muƙaami. Wato, zuga wata dabara ce ta
harzuƙa ‘yan siyasa su sadaukar da duk abin da suke da shi, don haɓɓaka jam’iyyunsu da
tsayawa takarar muƙamai daban daban, ko da ba su dace da
muƙaman da suke nema ba.
1. 5 Zuga Tubalin Gina Siyasa
A jamhuriyoyin da suka gabata, wato
jamhuriya ta farko da ta biyu, mawaƙan siyasa sun taka
muhimmiyar rawa wajen yin amfani da zuga don gina siyasa a Nijeriya. Misali, a
jamhuriya ta farko mawaka sun yi amfani da zuga , inda suka kambama jam’iyyunsu
da manyan ‘yan siyasa har suka samu karɓuwa ga jama’ar ƙasa. A jam’iyyar NEPU, mawaƙa irin su Mudi
Sipikin da Lawal Maiturare da Sa’adu Zungur da Aƙilu Aliyu, sun yi amfani da zuga wajen
kambama al’ummar Nijeriya su zama cikin shiri domin su ƙwato wa Arewa da sauran al’ummar ƙasa ‘yancinsu. Misali, Mudi Sipikin a
cikin waƙarsa ta nasiha ga ‘yan siyasa, yana cewa:
‘Yan
siyasar gari gari,
Duk
ku zo kan batun shiri,
Cikin
nasiha da hanƙuri,
Inda
dai babu tunzuri,
Sai batun masu
gaskiya.
(Mudi Sipikin: Waƙar nasiha ga ‘yan siyasa).
Malamin ya yi kira ga jama’ar Nijeriya,
musamman ‘yan siyasar Arewa da kudancin Nijeriya na kowane lungu, wato, gari
gari da su zo ƙwansu da kwarkwatarsu domin a shirya
yadda za a haɗa kai a ƙwato wa Nijeriya‘yanci daga hannun ‘yan
mulkin mallaka. Mawaƙin ya zuga mutane da “su zo”, a zauna
cikin kwanciyar hankali da haƙuri domin a
tattauna ba tare da an tada jijijyar wuya ba, a fito da hanyar da za a ƙwato wa Nijeriya ‘yancinta. Ya ƙara da kira ga jama’ar ƙasa ta hanyar zuga
su, su yi ƙoƙari tare da yin haƙuri domin ana buƙatar a haɗa kai cikin
hanzari, a yi aiki na gaskiya domin a cimma biyan buƙatar samun ‘yancin kai. Malamin yana cewa:
Duk mu tayar da ƙoƙari,
A kasar nan a zam shiri,
Ana buƙatar fa hanzari,
Sai mu ƙara da hanƙuri,
Mu yi aiki gaba ɗaya.
(Mudi Sipikin: Nasiha ga ‘yan siyasa).
Saboda haka, mawaƙin ya yi kira ga ‘yan siyasar gari
gari da su haɗa kai su goya wa shirin siyasa baya don a kai ga nasarar samun ‘’yancin kai
a Nijeriya.
Haka a jamhuriya ta biyu, mawaƙa irin su Garba Gashuwa da Muhammadu Auwalu Isah Bunguɗu, suna daga cikin
mawaƙan da suka ba da gudummawa wajen amfani
da zuga domin su harzuƙa ‘yan siyasa da jam’iyun siyasa; domin su jawo hankalinsu su jajirce wajen neman ‘yanci domin ganin
siyasa ta kafu da gindinta a Nijeriya. A cikin waƙarsa ta P. R. P. . Auwalu Isah Bunguɗu yana cewa:
Talakawa kar a burge ku,
Wata naira kar ta ruɗa ku,
Ku tsare girman mutuncinku,
Ku tsaya ku fito da ‘yancinku,
Ku ba bayin mutum ne ba.
(Auwal Isah Bunguɗu: P. PP, maganin zamba ta ɗaya).
Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin zuga da suka haɗa da ‘kar a burge
ku’, da ‘ku tsare’ , ‘ku tsaya’ da ‘ku fito’ domin ya harzuƙa talakawa su dage ba tare jin tsoro ko karɓar kuɗi ba su sayar da
mutuncinsu. Domin idan har za ruɗi mutane da kuɗi don a hana masu
gudanar da ƙudurinsu na neman ‘yanci, to babu shakka gwagwarmayar neman ‘yanci ta sami matsala. Saboda haka ne mawaƙin ya zuga talakawa da tsaya su dage su kare mutuncinsu
ta hanyar ƙin karɓar kuɗi, wanda yin haka
shi zai sa ba za acimma nasarar abin da ake nufi ba.
Shi kuma Garba Gashuwa a cikin waƙarsa da ya yi wa malam Aminu Kano, mai take, Aminu Nurul
zamani. Mawaƙin ya zuga mutane ‘ya’yan jam’iyyar P. R.
P. su jajirce su rungumi jam’iyyar P. R. P wadda ya sifantata da mai ƙirjin ƙarfi. Wato ƙarfinta ya zarce na sauran jam’iyyun P. P. P da G. N. P. P. , da sauransu. Malamin yana
cewa:
Jama’a ku kamo P. R. P.
Nasara ga mai ƙirjin ƙarfi,
Wadda ta buge ɗan P. P. P.
Ko Borno ba G. N. P. P,
Sai shehu Nurul Zamani.
(Garba Gashuwa: Waƙar Aminu Kano).
1. 6. Zuga Jam’iyya
A wannan jamhuriya ta huɗu da muke ciki, mawaƙan siyasa sun taka muhimmiyar rawa wajen gina siyasa har
aka sami nasara ta zauna da gindinta. Idan muka lura da yadda mawaƙan siyasar zamani suka tallata jamiyyunsu da ‘yan siyasarsu, sai mu ga cewa, haƙa ta cimma ruwa wajen gina siyasa mai ɗorewa a wannan
jamhuriya ta hudu. Misali, mawaƙan siyasa daban
daban sun yi amfani da dabarar zuga domin su kambama ‘yan takara da jam’iyyun siyasa domin jawo hankalin al’umma su zaɓi mutanen da suka cancanta su jagoranci al’umma. Waɗannan mawaƙa sun ba da gudummawa wajen harzuƙa ‘yan siyasa na kowace jam’iyya domin su tallata su ga jama’a su aminta da su.
Misali, a jamiyyar APP, mawaƙa sun taimaka wajen kambama jam’iyyar domin su ƙara ɗaga darajarta ga mutanen Nijeriya. A
cikin waƙarsa Ibrahim Aminu Ɗandago ya kambama jam’iyyar inda yake cewa:
Hantar kura a gun
kare ta fi ta lasuwa,
Ɓarin gari ba a yi a kwashe tsab ɗan’uwa,
Ba a dukan Uba a
ce an yi da mantuwa,
Dashen Allah ba
dashen mutum ba dashen kainuwa,
Hukuncin Alllah a
bi shi, shi ya fi da hayaniya.
(Aminu Ɗandago: Waƙar A. P. P. ).
Mawaƙin ya kambama jam’iyyar A. P. P. , inda
ya kamanta darajarta da ta kura, wadda kowa ya san cewa kura dabba ce mai kwarjini
da ke bai wa kare tsoro. Domin har shi kansa karen yana mugun tsoron haɗuwa da kura ga
azaliya. Saboda haka, hantar kura ba ta lasuwa ga kare ko ta mutu, balle tana
raye; domin ta fi ƙarfinsa. Don haka, duk wata jam’iyyar
da ba A. P. P. ba, dole ta bi bayanta. Mawaƙin ya kamanta darajar A. P. P. da sauran jam’iyyu, wadda ya ce ta fi sauran jam’iyyu. Har wa yau ya nuna cewa, ita jam’iyyar A. P. P. Allah
ne ya dasa ta ba wai mutum ba, abin nufi Allah ya ba ta kwarjin da kowa ke
sha’awar ta. Saboda haka duk wanda Allah ya ɗaukaka, to a bi
shi shi ne masalaha. Mawaƙin ya yi amfani da
salon karin magana domin ya isar da saƙonsa cikin hikima
da kuma samar da nishaɗi ga masu sauraro ta yadda za su
fahimci saƙon cikin hamzari. Misali, ‘Hantar kura
a gun kare ta fi ta lasuwa’. Wannan wata dabara ce ta isar da saƙo ga al’umma cikin hikima tare da samar da nishaɗi.
Shi ma Garba Gashuwa ya yi irin wannan
kambamawar ga jamiyyar A. P. P. , a cikin waƙarsa da ya raɗa wa suna, ‘Munafurcin Karen Ruwa’. yana cewa:
A. P. P. ta mamaye ƙasa,
Tun da ta ɗauke jiga-jigan ƙasa,
Ta ko gama da na nesa har kusa,
Kar ka shigo mana
mai munaƙisa,
Ka hautsina al’umma
gaba ɗaya.
(Garba Gashuwa: Waƙar A. P. P. )
Malamin ya nuna wa jama’a cewa
jam’iyyar A. P. P. ta samu karɓuwa a duk faɗin Nijeriya, inda
har ta ɗauke manya-mayan jiga-jigan ‘yan Nijeriya. Wato a siyasance, duk jam’iyyar
da ta kama mayan masu kuɗin ƙasa, wani lokacin har da sarakuna da manyan ma’aikatan gwamnati, to babu shaka jayayya da ita sai an
shirya. Wannan dalili ne ya ya sa mawaƙin ya kambama jam’iyyar ta A. P. P. domin ya bai wa sauran jam’iyyu tsoro. Wannan salon zuga da mawaƙin ya yi amfani da shi, ya ƙara jawo wa jam’iyyar A. P. P. kwarjini
ga al’ummar Nijeriya baki ɗaya.
Shi kuwa Shu’aibu ‘Yar Medi a waƙarsa ta jam’iyyar P. D. P. ya nuna wa duniya cewa a Nijeriya, P. D. P, ba wata
jam’iyyar da ta dace ta mulkin jama’a sai ita. Ya tallata jam’iyyar inda ya
kambama ta, yadda har mai saurare zai zaci cewa P. DP. wata hamshaƙiyar mayaƙiya ce da ta
gagari abokan gaba. Malamin yana cewa:
Ga jirgin zuwa
bahrul Aswad Tekun gabas waccan,
Ba zan hau kwami
ya kife ba da ni ‘yar ƙorama kui can,
P. D. P. nake so jam’iyya
ba na cikin waccan,
Duk mai son ƙasa ya fito a yi P. D. P. mazanmu da mata.
(Shu’aibu: Waƙar P. D. P).
Da yake tofa albarkacin bakinsa dangane
da kambama jam’iyyar P. D. P. , Kabiru Yahaya Kilasik yana cewa:
Ɗaukar rigimata sai party marinjayi,
Ko kare ya kai
gwarzo ai ba ya cin tayi,
Lema ni ka so don
ita kowa yake yayi,
Ban barin ɗiya in tahi don
tambaɗa boya.
(Kabiru Kilasik: Waƙar Bello matawalle).
Kabiru Kilasik mawaƙi ne, kuma ɗan siyasa mai aƙida. Duk ɗan siyasa da ke da aƙida, ba zai taɓa yarda da yaudara
da ruɗin masu siyasar, ‘duk inda ta fi maiƙo can muka mai da
kayanmu’. Mawaƙin riƙaƙƙen ɗan jam’iyyar P. D.
P. ne, wanda aƙidarsa ta kai shi ga nasarar tsayawa
takarar kujerar ɗan majalisar wakilai ta ƙasa har ya samu
nasarar lashe zaɓe a shekarar 2015. Saboda haka mawaƙin yana wayar wa
jama’a kansu tare da faɗakar da dukkan al’umma game da amfanin
siyasar aƙida; wadda da ita ake samun kafa mulikn
siyasa na cigaban ƙasa. Saboda haka sai ya ƙara kambama jam’iyyarsa ta P. D. P. domin ya nuna wa jama’a cewa idan kai ɗan aƙidar siyasa ne, to tarin dukiya ko matsayin wasu ‘yan siyasa ba zai ruɗe ka, ka bar
jam’iyyar da ke da manufar gina ƙasa ba. Yana cewa:
Komi za a yi man P. D. P. nake ƙauna,
Babbar jam’iyata ita ma tana so na,
Ko tana gudu na ita za ni sa kaina,
Bello inda amana ɓota ba ta ƙin hauya.
(Kabiru Kilasik: Waƙar Bello matawalle ta P. D. P. ).
1. 7. Zuga ɗan Takara
Mawaƙan siyasar zamani suna amfani da zuga domin su kambama ɗan takara ya ji ƙarfin karawa da kowane mutum da ya fito neman kujerar da
yake takara a kanta. Wato, mawaƙan siyasa suna
ingiza ko harzuƙa ɗan takara ta
hanyar sa sabulu su wanke laifukansa ko ɗabi’unsa waɗanda ba su da kyau,
sannan su rangaɗa masa kwalliya da wasu kyawawan halaye ko ɗabi’u domin su
tallata shi ga al’umma. Wannan zuga da mawaƙan kan yi wa ‘yan takara wata dabara ce ta jawo
hankalin masu saurare tare da faɗakar da ‘yan siyasa game da muhimmancin
kyawawan ɗabi’u ga duk mutumin da yake son mutane su so shi, kuma su zaɓe shi ga kowane
matsayi na siyasa. Misali a cikin waƙarsa da ya yi wa
Janar Muhammadu Buhari, Ibrahim Yala hayin banki, ya kambama ɗantakararsa da
cewa:
Ka zama jinjirin wata kai ne ake jira,
Rana ta fito ta riga ta gagara,
Dutse ka wuce buhu koko tokara,
Har mai gatari Muhammad zai juriya.
(Ibrahim Yala: Yau Nijeriya riƙo sai mai gaskiya).
Wannan baiti yana ɗauke da saƙo ne na kambama darajar Buhari bisa ga sauran ‘yan takara domin a nuna wa jama’a irin kwarjinin da Buhari yake da shi a cikin al’ummar Nijeriya. Mawaƙin ya yi amfani da salon kwalliya inda ya kira Buhari da ‘dutse’, wanda ya ce ya wuce a sa shi cikin buhu, ko ma a tokare shi. Wannan salon
kwalliya da mawaƙin ya yi amfani da shi, wata dabara ce
ta kambama ɗan takara domin ya fifita darajarsa da sauran ‘yan takara abokan adawarsa. Saboda
haka, zugan da Yala ya yi wa Muhammadu Buhari ya taimaka matuƙa wajen kai Buhari ga nasarar lashe zaɓen shugaban ƙasa a shekarar 2015. Amfanin zuga cikin waƙoƙin siyasa da mawaƙa ke amfani da shi, shi ne domin su wayar wa jama’a kai da kuma cusa masu son
ɗan takara a zukatansu.
Shi ma Yusuf Fasaha kano, ya yi amfani
da salon zuga domin ya kambama ko ingaza ɗan takararsa ya jajirce wajen aikin
alhairi da yake yi wa al’ummarsa. Yana cewa:
I Musa Iliyasu riƙe Allah,
Makiyanka ba za su kai ka ba,
I ka yi taka ka yi ta raggo,
Zaki mujin Amina mai ba da tallafi.
(Yusuf Fasaha: Mu bi A. P. C. , al’ummar ƙasa).
Shi ma ya yi amfani da salon kwalliya
ko kinaya, inda kai tsaye ya kira gwarzonsa da suna ‘zaki’ don ya nuna wa jama’a
irin ƙarfin da ɗan takararsa yake
da shi a cikin harkokin siyasa. Ya kuma nuna wa jama’a cewa Musa Iliyau, ba wai
ga matsalarsa kawai ya tsaya ba, a’a da zarar ya gama tasa, sai ya yi ta raggo,
wato ta mai ɗanƙarfi ke nan.
1. 8. Zuga Hana maguɗin Zaɓe
Mulkin siyasa ba ya tabbata sai da
gudanar da zaɓe, wanda ke halitta wa waɗanda aka zaɓa gudanar da
harkokin mulki kamar yadda kundin tsarin mulki ya gindaya. Talakawa su ne ƙashin bayan gudanar da kowace irin tafiya ta siyasa, domin
su ke zaɓen ‘yan takara, ta hanyar jefa ƙuri’unsu su zaɓi mutumin da ya dace ya shugabance su. A
sanadiyar haka ne, ya sa mawaƙan siyasar zamani
suke amfani da salon zuga domin su harzuƙa ‘yan siyasa da sauran talakawa su jajirce wajen tsayawa ga
akwatunan zaɓe don su hana maguɗi a lokacin kaɗa ƙuri’a. Kowace jam’iyya tana ƙoƙarin tsayar da wani mutum (Agent), wanda zai sa ido ga zaɓen da ake
gudanarwa domin su hana a yi maguɗin zaɓe. Kowace jam’iyya
tana tsayar da mutum mai kwarjini, wato, ɗan takararta mai kwarjin da riƙon amana wanda zai ƙwato wa talakawa
‘yancinsu da haƙƙoƙansu. Saboda haka
sai su nemi mawaƙan siyasa su yi amfani da salon zuga
domin su jawo hankalin masu jefa ƙuri’a su aminta da wanda jam’iyyarsu ta tsayar takara. Waɗannan mawaƙa su za su fito fili su zuga ɗan takara da
talakawa su sa ido ga yadda zaɓuɓɓuka ke gudana. Sannan, su ne, za su
zuga talakawa su tashi tsaye su ga cewa ba a yi maguɗin zaɓe ba a lokacin kaɗa ko jefa ƙuri’a. Misali, Murtala Mamsa Jos ya zuga talakawa a lokacin zaɓen da aka gabatar
a shekarar 2015, inda ya harzuƙa talakawa su sa
ido, su kasa su tsare don gudun kada a yi masu maguɗin da ‘yan
jam’iyya mai mulki suka saba yi a lokacin zaɓuɓɓukan da suka
gabata. Ya ce a yanzu kai ya waye, tsoro ya ɗebe don haka ƙarya ne a sake tafka magudin zaɓe, a zaɓe mai zuwa. Saboda
haka ko da tsiya ko da arziki sai sun hana a yi masu maguɗi domin ba su
yarda da haka ba. Misali, yana cewa:
Janar Buhari ikon
Allah ka zud da ƙwallon ‘yan Nijeriya,
Kun ci zaɓe an murɗe mana, hayaniya
za mui kai ka tsaya,
Kana hana mu mu ɗau doka a hannu
al’ummar Nijeriya,
Lokaci in ya yi
Uban kuturu kaɗan ya yi, yai mana fariya.
(Murtala Mamsa: Waƙar sabuwa ta zo, A. P. C. ).
Mawaƙin ya yi ƙoƙarin jawo hankalin
talakawa su fahimci irin shirin da ‘ya’yan jam’iyya mai mulki suka yi na tafka maguɗin zaɓe domin su ga ko
ta halin ƙaƙa sun koma ga
mulkinsu, (Tazarce). Ta hanyar zuga talakawa da mawaƙin ya yi, ta faɗar cewa, ‘in lokaci ya yi Uban kuturu
kaɗan yayi yai mana fariya’. Wato mawaƙin ya nuna wa ‘yan Nijeriya cewa a shirye talakawa suke su nema wa kansu
‘yanci ta hanyar hana maguɗin zaɓe a zaɓe da ke tafe. Wannan
harzuƙa talakawa da mawaƙin ya yi ya taimaka ainun wajen jawo hankalin masu jefa ƙuri’a su dage su ga sun hana maguɗin zaɓe; wanda haka ya
sa zaɓen Muhammadu Buhari ya samu nasara a 2015.
Haka abin ya kasance a saƙon da Ibrahim Yala ya isar wa talakawa na su jajirce a
lokacin jefa ƙuri’a su ga cewa ko ta halin ƙaƙa sun hana a yi maguɗin zaɓe, idan aka zo
jefa ƙuri’a a 2015. Malamin yana cewa:
Ku zo mu ƙara faɗa masu dai,
Yau ƙasarmu A. P. C. muka yi,
In za ai zaɓe a yi gaskiya,
Ba za mu yarda da runto ba,
Nijeriya sai baba Buhari,
Gaskiya dokin ƙarfe.
(Ibrahim Yala: Waƙar A. P. C. 2015).
Shi kuma Mudassiru Ƙasimu, ba wai yana zuga talakawa kaɗai ba, su hana
maguɗin zaɓe, a’a ko da za a ce sai talakawa sun biya kuɗi sannan su zaɓi Buhari, to a
shirye suke su yi haka, muddin dai suna da damar yin haka ɗin. Yana cewa:
Ranar zaɓe mu zaɓi Buhari,
Koko da za a ce sai an biya kuɗi,
Za mu biya mu zaɓi Buhari .
(Mudassiru : Mu amshi ruwa ma zaɓi Buhari).
A wannan baiti da ya gabata, mawaƙin ya zuga talakwa su tsaya tsayin daka, ko da sai an biya
a zaɓi Buhari, to su shirya su ga an zaɓi Buhari ba tare da an yi maguɗi ba. Sannan ya
nuna wa duniya cewa talakawan Nijeriya sun shiya tsaf su canza gwamnatin
jam’iyyar P. D. P da suka jefa ƙasa cikin
mawuyacin halin taɓarɓarewar tattalin
arzikin ƙasa da rashin aikin yi ga matasa, wanda
ya haifar da taɓarbarewar tsaro a Nijeriya.
1. 9. Zuga don hana ha’inci da cin hanci
Ha’inci da cin hanci kusan ɗan juma ne da ɗan jumai domin
dukkansu suna nufin tauye haƙƙin mai haƙƙi. Wasu suna fassara ha’inci da cin hanci da rashawa. Ko
yaudara ta hanyar danne dukiyar talakawa da shugabanni ke yi. Ƙamusun Hausa (1934), ya bayyana cewa, ha’inci yana nufin
yaudara ce ta kowane fanni na rayuwa da ya shafi rashin bai wa mai haƙƙi haƙƙinsa. Wannan
bayani ya nuna cewa, a duk lokacin da aka hana mai haƙƙi haƙƙinsa to, wannan ne
ha’inci domin akan yi amfani da ƙarfin iko ko kuɗi don a sauya akalar wani abu daga wani
bagire zuwa wani wuri na daban. Ko a yi amfani da kuɗi ko wata kyauta
don a saye wanda nauyin mutane ya rataya a kansa yayi abin da ya saɓa wa dokar ƙasa ko al’adar al’ummar da yake tare da su. Mawaƙan siyasar zamani sukan yi amfani da zuga wajen wayar wa
mutane kai, su jawo hankalinsu su fahimci duk wata badaƙala da shugabanni suke shiryawa domin su ha’inci al’ummarsu, wato talakawa. Misali, Ibrahim Yala, a cikin waƙarsa ta C. P. C 2011, ya zuga matasa su tashi tsaye su ƙwato ‘yancinsu da shugabannin Nijeriya suka ha’ince su. Ga abin da yake cewa:
Ina kuke rundanar
matasan Nijeriya,
Mu tashi mu ƙwaci ‘yanci Nijeriya,
Mata kar ku yarda
yau a yi muku murɗiya,
Sai mu zage, mu
kai Buhari mai gaskiya.
(Ibrahim Yala: Waƙar C. P. C 2011).
Mawaƙin ya zuga matasa maza da mata su jajirce su zaɓi Buhari don shi
ne zai sa su ƙwato ‘yancinsu. Ƙwatar ‘yanci yana nufin su kauce wa karɓar kuɗi a lokacin zaɓe, su daure su zaɓi mutum nagari, wanda
zai ba kowa haƙƙinsa ba tare da tauyewa ba. Wato, ba
tare da an ha’ince su ba, ko tauye masu wani kaso da ya dace su samu.
Shi ma Dauda Kahutu Rarara ya yi irin
wannan zuga ga Buhari, wanda ya ce shi mai gaskiya ne, ba ya sata, ba ya ha’inci.
Saboda haka mulkin Nijeriya sai baba Buhari. Mawaƙin yana cewa:
Tattali za a yi ba
cuwa-cuwa, sai kai baba,
Baba ka ƙara ƙwazo kana daɗa kauda cutawa.
(Dauda Rarara: Waƙar Buhari ta A. P. C. 2015).
Dauda ya yi amfani da salon kamance, inda
ya kamanta Buhari da mutaen kirki masu gaskiya da riƙon amana. Yana nuna cewa ko da ganin ɗabi’un Buhari bai yi kama da mutanen
banza waɗanda mawaƙin ya kira su da suna ‘cutawa’. Wato, duk mutumen da ya kasance maha’inci to sunansa macuci ko maha’inci domin ba shi tausayin
talakwan da ako ɗora masa alhakin jagorancinsu.
Irin waɗannan mutane ne
Yusuf Fasaha yake gargaɗin ‘yan Nijeriya da su kauce wa zaɓen su domin ba
nufinsu siyasar gina al’umma ba, sai dai aka kasa kowa ya kwashi rabonsa. Irin
wannan ɗabi’a ta wasu ‘yan siyasar Nijeriya, ta a ci wawa, a watse, shi ke hana mulkin
siyasa ya zama ɗorarre, sai dai wata masana’antar da mutum zai sai da mutuncinsa domin ya
sami abin dukiya. Zancen gina siyasa mai ta gina ƙasa da al’umma ta tashi a nan. Mawaƙin yana cewa:
Za mu kauda
rashawa, cin hanci,
Har zamba ba ma ƙyale yin ta ba.
‘Yan ƙasarmu sai mun tashi tsaye,
A kudun Arewa sannan mu kai gaci.
Mu bi A. P. C. sak ba canji,
‘yan ƙasarmu mun samu lokaci.
(Yusuf Fasaha: Mu bi A. P. C. , al’ummar ƙasa).
Mawaƙin ya yi amfani da kalmomin zuga don ya jawo hankalin mutane su fahimci
amfanin gwagwarmayar neman‘yanci ita kaɗai ce hanyar da za abi a samar da
kyakkyawan mulkin dimokuraɗiya mai ɗorewa a Nijeriya. Ya
yi amfani da kalmomin zuga da ke kiran mutane su tashi tsaye don ya harzuƙa su kamar haka;‘’yan ƙasarmu’, ‘tashi tsaye’, ‘kudun da arewa’ da sauransu. Wato tashi tsaye na
nufin zuga ‘yan ƙasa su san ‘yancinsu ta hanyar zaɓen Muhammadu
Buhari, mutumin da aka shaide shi da gaskiya da riƙon amana. Mutum wanda ba ya ha’inci ba ya karɓar rashawa, balle ya tauye haƙƙin talakawa.
Shi kuwa Shu’aibu ‘Yar Medi yana ganin
karɓar kuɗi ba ya hana a zaɓi wanda ya cancanta a waƙarsa ta jam’iyyar P. D. P. Yana cewa:
Jam’iyya a kan
manufa aka fara ba muƙami ba,
Zaɓen nan abin ra’ayi
aka faro ba da naira ba,
In an ba ka naira
hamsin sa hannu riƙe baba,
Sai ka je akwati
ka ɗau inuwar lema a gyara ƙasata.
(Shu’aibu: Waƙar P. D. P).
1. 6 Kammalawa
Babu shakka zuga wata dabarar isar da
saƙo ce da mawaƙan siyasar zamani suke amfani da shi domin su jawo hankalin masu sauraren
wakoƙinsu su fahimci saƙon da suke isarwa gare su. Mawaƙan siyasa sun yi tasirin gaske ga rayuwar
al’ummar Nijeriya musamman wajen wayar masu da kai a kan muhimmancin zaɓen mutane nagari a
muƙamin siyasa. Ta hanyar lura da irin
tasirin da siyasa take da shi a rayuwar al’umma ya sa, mawaƙan siyasa suke amfani da waƙoƙinsu domin su isar muhimman saƙonni dangane da yadda shugabanci yake tafiya. Mawaƙan suna amfani da zuga domin su harzuƙa ‘yan siyasa su riƙa bunƙasa suna taka muhimmiyar rawa wajen aiwatar da abubuwan cigaban ƙasa da kuma al’umma baki ɗaya. Yin amfani da dabarar zuga da mawaƙan siyasa ske yi, yana daga cikin hanyoyin faɗakarwa da siyasa
take shauƙin cimma nasarar da kowace jam’iyyar siyasa ke yi. Saboda haka zuga ya taimaka tuƙuru wajen haɓɓaka dimokuraɗiyya mai ɗorewa a wannan
jamhuriya ta huɗu da muke ciki.
1. 7. Sakamakon Bincike
Gwanin rawa shi ne wanda ya burge masu
kallo, inji Hausawa. Mawaƙan siyasar zamani
su ne tsane da ‘yan siyasa suke takawa su hango wuraren da za su jefa ƙafafunsu. Don haka ne suke amfani da mawaƙan siyasa domin su cimma manufofinsu na gina siyasa a duk
lokacin da aka buga gangumman siyasa. Wannan takarda ta gano irin tasirin da
zuga ya ya yi wajen faɗakarwa da wayar da kan ‘yan siyasa
dangane da alfanun zaɓen mutanen kirki a siyasance, waɗanda ke zama
gimshiƙin samar da ko kafa mulkin siyasa mai ɗorewa.
Zuga da mawaƙan siyasa ke amfani da shi cikin waƙoƙinsu ya taka rawar gani wajen gyara ɗabi’un ‘yan siyasa,
musamman waɗanda ke sha’awar tsayawa takara. Kyawawan halaye na gaskiya da eiƙon amana su ne gimshiƙin samar da shugabanci nagari a siyasance. Har wa yau, zuga ya taimaka waje
tallata kyawawan aƙidun shugabanni masu gaskiya da riƙon amana, waɗanda cigaban ƙasa da bunƙasa tallalin arzikinta da zaman lafiya,
shi ke a zukatansu.
A bangaren ‘yan siyasa su kansu, zuga
ya taimaka masu wajen gyara ɗabi’unsu da cire masu shakkun tsayawa
takara matuƙar ba su da wani mummunarn tsalmi a
rayuwarsu. Hausawa suna cewa, ‘idan baka san asalinka ba, to shiga siyasa, yanzu
za san kai kowane ne’. Wannan takarda ta gano cewa zuga ya taimaka wa ‘yan
siyasa wajen fahimtar tasirin da aiwatar da ayyukan raya ƙasa suke da shi wajen gina siaysa mai ɗorewa a ƙasa. Saboda haka, wannan takarda ta gano cewa, zuga da
mawaƙan siyasa suke amfani da shi ba waai ya
tsaya ga ƙosar da nishaɗi ga masu sauraren
waƙa kaɗai ba, a’a wani
makami ne gyara tarbiya da ɗabi’un ‘yan siyasar zamani a yau. Dalilin
amfani da zuga ya sa aka sami sauyin gwamnati a shekarar 2015, inda aka zaɓi Muhammadu Buhari
da ake yi wa lakabi da, ’gaskiya dokin ƙarfe.
1. 8 Shawarwari
Gina siyasa ta cigaban ƙasa ba ta yiwuwa sai an sami mutane masu amana da
kyawawan ɗabi’u da hazaƙa da ilimin sanin makamar aiki da ƙwarewa ga iya hulɗa da mutane. Waɗannan abubuwa da aka
ambata su ne, za su samar da kyakkyawan mulkin siyasa a ƙasa, wanda zai kawo wa al’umma hanyoyin cigaban rayuwa. Saboda haka, domin
a gina ƙasa har ta zama daidai da sauran ƙasashen da suka ci gaba ta fuskar siyasa, dole ne a sami
mutane masu gaskiya da amana su shugabanci al’umma ga mulkin siyasa. Da wannan shawara
ce, ake sa ran idan aka yi amfani da ita za a sami siyasa ta ginu bisa ga kyakkyawar
turba ta gaskiya da adalci a Nijeriya.
MANAZARTA
Bergery, G. P. (1934), Hausa-english
and english- Hausa Vocabulary. London ; Oxford University press.
Bunza A. M. (2009) Nanarambaɗa, Ibrash Islamic
Publications Centre LTD.
Bunza A. M. (2013), Makamin Dimokuraɗiyya a Falsafar
Al’ada. 1st National Conference in Languge, Literature, and Culture. Center for
Study of Nigerian Languages, B. U. K. Kano.
Bagega S. (2023), Asalin Zuga- hira da
sarkin m\ƙeran Bagega, Ƙaramar Hukumar Anka, ranar 24/03/2023.
Bunguɗu A. I. (2017), Tarken
Rubutattun Waƙokin Siyasa Na Kabiru Yahaya Kilasik. Kundin
digiri na biyu, Jami’ar Bayero, Kano.
Ɗangulbi A. R. (2003), Siyasa A Nijeriya: Gudummawar marubuta waƙoƙin siyasa na Hausa ga kafa Dimokuraɗiyya a Jamhuriya
ta huɗu, zango na farko. Kundin digiri na biyu. Sashen Harsunan Nijeriya, Jami’ar
Usmanu Ɗanfodiyo , Sokoto.
Idris Y. (2016), Jigon Bijirewa A
Rubutattun Waƙoƙin Siyasa A Ƙasar Hausa-(1903-2015). Kundin digiri na uku , Jami’ar Ahmadu Bello Zariya.
Oxford Dictionary, 9th edition.
Yahya A. B (1997) Jigon Nazarin Waka, Kaduna:
Fisbas Media Services.
Garba Gashuwa----Waƙar Aminu Kano P. R. P. 1978.
Garba Gashuwa-----Waƙar A. P. P. Munafuccin Karen Ruwa
Ibrahim Ɗandago-----Waƙar A. P. P. 1998.
Ibrahim Yala------Waƙar AP. P 2003,
Iibrahim Yala----Waƙar C. P. C. 2011
Ibrahim Yala ----Waƙar A. P. C. , 2015
Kabiru Yahaya Kilasik ---Waƙar Bello Matawalle, P. D. P.
Muhammad Auwalu Isah Bunguɗu----Waƙar P. R. P. 1978.
Mudi Sipikin-------Waƙar siyasa, nasiha ga ‘yan siyasa 1956.
Murtala Mamsa Jos----Waƙar A. PC. , sabuwa ta zo.
Shu’aibu ‘Yar Medi-----Waƙar P. D. P. 1998.
Yusuf Fasaha ----Waƙar A. P. C. , Mu bi A. P. C al’ummar ƙasa
Dauda Kahutu Rarara---Waƙar A. P. C.
Yusuf Fasaha----Wakar A. P. C. , Mu bi
A. P. C. sak ba canji.
Mudassiru Ƙasimu----Waƙar A. P. C. mu amshi ruwa mu zaɓi Buhari.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.