Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsakanin Maza Da Mata Suwa Suka Fi Kishi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Aslm Malam Khamis da fatan ka tashi lafiya. Dan Allah malam tambaya nakeyi Tsakanin maza da mata wa yafi kishi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus salam Warahmatallahi Wabarkatahu.

Da farko dai kishi wani yanayi ne na so da kauna da burin kare abun da ake son daga kamuwa da cuta. Ana kishin kasa kuma ana kishin sana’a da abokan zama. Duk inda akwai kishi mutane na ganin cewa akwai so, har ma wasu kan ce “kishi so ne”. Duk ɗan Adam bai cika mutum ba sai ya kasance yana da kishi. Ko dai ya kasance yana kishin kansa, kishin iyalinsa da dai makamantansu.

Shi kishi akwai shi a musulunci, don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce Allah na fushi da wanda ba ya kishin iyalinsa.

Nana A'isha tana cewa : "Ban taɓa yin wani kishi ba, irin kishin da na yiwa Khadijah, duk da cewa ban taɓa ganinta ba, saboda yadda na ji Annabi Sallallahu Alaihi Wasallam yana ambatonta" Bukhari 1388

Hausawa na cewa “kishi kumallon mata.” Amma a zahiri ba mata kaɗai ke da kishi ba, har mazan ma suna da shi. Mutane da dama na ganin cewa maza sun fi mata kishi, kawai dai matan sun fi nunawa ne. Wannan abu ne da za a iya muhawara a kai. In har hakan ne, akwai abubuwa da dama da ke silar hakan.

Tabbas Azahiri Mata Sunfi Maza Kishi Sabida Su Akafi Sani Da Bayyana Shi Dakuma Aikata Shi Amma Kuma Idan Mukabi Wasu Hanyoyi Na Karkashin kasa Zamuga Cewa Maza Sunfi Mata Kishi Nesa Ba Kusa Ba Dalilaina Sune

1. Duk Wata Mace Namiji Ɗaya Take Aure Kuma Dashi Take Rayuwarta Amma Namiji Zai Auri Mace Huɗu Kuma Ya Haɗasu Guri Ɗaya Kuma Su Rayu Tare. To dan'uwa Ka Kiyasta Aranka Da Ace Macece Ke iya Auran Namiji Huɗu Shikuma Ya Auri Mata Ɗaya Yaya Zakayi Da Sauran Mazajen Matar Taka?

2. Amatsayin Mace Na Matar Aure Bata Damuwa Da Duk Matar Da Zatai Alaka Da Mijinta Matukar Ance Sunada Alaka Ta Yan Uwantaka Ko Da Kuwa Ta Kakannine Ko Dangi Ɗaya Saɓanin Namiji Da Baya Iya Jure Alakar Matarsa Da Duk Wani Namiji Matukar Ba Uwa Ɗaya Uba Daya Sukeba Saidai Inya Zama Dole Bashi Da Mafita.

3. Duk Namijin Da Yafito Unguwa Da Budurwarsa Ko Matarsa Idan Wani Ya Kalleta Sai Kaji Yace Wannan Yafiya Kallo Amma Da Wata Zata Kalleshi Saidai Ta Kauda Kanta.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments