Ticker

6/recent/ticker-posts

Matsalar Jinin Haila

TAMBAYA (54)

Assalamu alaikumalaikum. Malam barka darana yakokari;malam ina da tambaya? Tun wancan satin ya kamata In ga jinin al'adata amma shiru haryanzu, kozan iyashan maganin da za ya zo, saboda wasu hujjoji nawa, 1. banisamun isasshen abinci 2, idan nasamu ciki ina yawan ciwo, da kuma ina son wancan bani son wancan, gashi Kuma mai gidana yanzu duk bayada halin wanna, gayaranmu wasuma, komakaranta basu samun zuwa saboda mun shiga jarabawar rayuwa, to malam yaya zanyi ke nan.

AMSA

Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum.

Alhamdulillah.

Mace zata iya shan maganin tsayarda jinin al'ada da sharuda guda biyu;

Na farko ya zama na macen bazata cutar da kanta ba saboda hujjar ayar Qur'ani,

(وَلَا تُلْقُوا بِأَيْدِيكُمْ إِلَى التَّهْلُكَةِ ۛ

البقرة (195) Al-Baqara

Kuma kada ku jefa kanku da hannayenku, zuwa ga halaka

Da kuma ayar;

(وَلَا تَقْتُلُوا أَنفُسَكُمْ ۚ )

النساء (29) An-Nisaa

Kuma kada ku kashe kãnku

Na biyu kuma idan amfani da maganin zai cutar da mijinta, to ya zama wajibi ta nemi izininsa. Misali; idan mace tana cikin Iddah kuma mijin yana kashe mata kudi (kafin ta kammala iddar) to bai halatta ta sha maganin ba saboda hakan zaisa ya kashe mata kudi dayawa, don haka sai ta nemi izininsa.

Haka kuma bazata sha ba idan tana son tsayarda haihuwa har sai ta nemi izinin mijinnata. A shawarce ba'a buqatar ta sha wannan maganin har sai bisa sharudan da aka zayyano a sama kuma sai hakan ya zama dole akanta saboda haquri da shan maganin shi yafi domin maslaha ga lafiyarta

Dangane da batun halacci ko haramci kuwa to wannan Shaikh al-Uthaymeen yace, halasne idan ya cike wadannan sharudan guda biyu;

Na farko ya zamana hakan bazai illata ibadarta ba. Misali; idan watan azumi ya kusa tsayawa sai ta sha ta yanda bazata dinga azumi ko sallah ba

Na biyu; idan zatayi amfani da maganin tsayarda haihuwa saida izinin mijinta saboda bayyanar jinin haila kan iya katange mijinnata da wadatuwa ga shigarta (mu'amalar aure), haka kuma idan an sake ta hakan zaisa mijinnata ya sauke nauyinta dake kansa saboda hakan zai janyo iddarta da wuri silar shan maganin. Ana magana ne akan sakin kome (wanda macen zata iya komawa gidan mijin)

Don haka yar uwa, a shawarce, ki samu maigidanki ku tattauna akan wannan ra'ayi naki. Idan ya amince falillahil hamd amman akasin hakan saiki hakura tunda ba wajibi bane kuma a qalla hakan zai zamo balance ga lafiyarki

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa;

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://chat. whatsapp. com/G5NSbo2TyHMD6bcoEfds5E

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments