Ticker

6/recent/ticker-posts

Raba-Ƙafa A Cikin Addini (Yana Zuwa Masallaci Kuma Yana Zuwa Coci)

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salamu Alaikum, Malam, wata matsala ce da ta zama kamar ruwan-dare a wasu sassa ko yankunan ƙasar nan: Mutum ya ce ya raba-ƙafa a cikin addini, watau yana zuwa masallaci kuma yana zuwa coci, wai yana gudun kar ya zo wanda ya bi a nan ba shi ne zai haye ba a lahira! Wai shin yaya matsayin irin waɗannan mutanen?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah.

Irin waɗannan in dai ba masu taɓin-hankali ba ne, to manyan jahilai ne. Ba su fahimci komai ba a cikin addinin musulunci. Domin Kalmar shahada wacce da ita ake shiga addinin Musulunci ta fayyace komai. Shaidawar da bawan Allaah ya yi cewa: Babu abin bautawa da gaskiya sai dai Allaah shi kaɗai, ba shi da abokin tarayya, wannan abin da yake nufi shi ne: Mutum ya amince ne tun daga zuciyarsa har bakinsa zuwa ga gaɓoɓinsa cewa: Allaah Ta’aala Maƙagin halittar sammai da ƙasa, da duk abin da ke cikinsu, da abin da ke a tsakaninsu, wanda kuma yake gudanar da alamuransu, guda ɗaya ne, shi ne Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala: Ba shi da farko, ba shi da ƙarshe, kuma ba shi da iyaye, ko mata, ko ɗa, ko wani abokin tarayya. Don haka, shi kaɗai ne kaɗai abin bauta, ban da duk wanda ba shi ba daga cikin Mala’iku da Annabawa da Manzannin Allaah. Ballantana sauran halittun da ba su kai su daraja ba, daga cikin itatuwa da duwatsu da dabbobi da tsuntsaye da sauran shaiɗanun mutane da aljanu da sauransu!

Amma a cikin addinin kirista kuwa, sun ɗauki Allaah a wurinsu guda ɗaya ne amma a cikin alloli guda uku: Uba da Ɗa Ruhi mai Tsarki! Wannan kuwa wani babban zunubi ne mai Girma a mahangar addinin Musulunci. Domin Allaah bai yarda da wannan gamayyar ko haɗin-gwiwar ba, ya ƙyamace shi, kuma ya kafirta duk mai amincewa da wannan aƙidar. Allaah ya ce

لَقَدْ كَفَرَ الَّذِيْنَ قَالُوْۤا اِنَّ اللّٰهَ هُوَ الْمَسِيْحُ ابْنُ مَرْيَمَۗ وَقَالَ الْمَسِيْحُ يٰبَنِىْۤ اِسْرَاۤءِيْلَ اعْبُدُوا اللّٰهَ رَبِّىْ وَرَبَّكُمْۗ اِنَّهٗ مَنْ يُّشْرِكْ بِاللّٰهِ فَقَدْ حَرَّمَ اللّٰهُ عَلَيْهِ الْجَـنَّةَ وَمَأْوٰٮهُ النَّارُۗوَمَا لِلظّٰلِمِيْنَ مِنْ اَنْصَارٍ ٢٧۝ لَـقَدْ كَفَرَ الَّذِيْنَ قَالُوْۤا اِنَّ اللّٰهَ ثَالِثُ ثَلٰثَةٍۘوَمَا مِنْ اِلٰهٍ اِلَّاۤ اِلٰـهٌ وَّاحِدٌۗوَاِنْ لَّمْ يَنْتَهُوْا عَمَّا يَقُوْلُوْنَ لَيَمَسَّنَّ الَّذِيْنَ كَفَرُوْا مِنْهُمْ عَذَابٌ اَ لِيْمٌ ٣٧۝

Haƙiƙa! Waɗanda suka ce: Allaah shi ne Masihu Ɗan Maryam sun kafirta, kuma Masihun cewa ya yi: Ya ku Bani-Israila! Ku bauta wa Allaah Ubangijina kuma Ubangijinku. Kuma lallai duk wanda ya yi tarayya da Allaah, to tabbas! Allaah ya haramta masa Aljannah, kuma makomarsa ita ce Wuta, kuma azzalumai ba su da wasu mataimaka!

Haƙiƙa! Waɗanda suka ce: Allaah shi na-ukun alloli uku ne sun kafirta! Kuma babu wani abin bautawa sai dai abin bauta guda ɗaya (shi ne: Allaah). Kuma idan ba su ciru daga abin da suke faɗi ba, to lallai azaba mai raɗaɗi za ta shafi waɗanda suka yi kafircin daga cikinsu!

(Surah Al-Maa’idah: 72-73)

Sannan kuma jingina wa Allaah ɗa shi ne mafi munin zagi gare shi Subhaanahu Wa Ta’aala. Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya faɗa a cikin hadisin da Al-Imaam Al-Bukhaariy (4482) ya fitar daga riwayar Ibn Abbaas (Radiyal Laahu Anhumaa) cewa

 قَالَ اللَّهُ : كَذَّبَنِى ابْنُ آدَمَ وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، وَشَتَمَنِى وَلَمْ يَكُنْ لَهُ ذَلِكَ ، فَأَمَّا تَكْذِيبُهُ إِيَّاىَ فَزَعَمَ أَنِّى لاَ أَقْدِرُ أَنْ أُعِيدَهُ كَمَا كَانَ ، وَأَمَّا شَتْمُهُ إِيَّاىَ فَقَوْلُهُ لِى وَلَدٌ ، فَسُبْحَانِى أَنْ أَتَّخِذَ صَاحِبَةً أَوْ وَلَدًا

Allaah ya ce: ‘Ɗan Adam yana ƙaryata ni, kuma hakan bai kamace shi ba. Sannan kuma yana zagi na, hakan kuma bai kamace shi ba. Amma ƙaryata ni shi ne: Riyawarsa cewa wai ba ni da ikon sake mayar da halittarsa kamar yadda ya kasance kafin mutuwarsa. Zaginsa gare ni kuwa shi ne: Cewa da ya yi wai ina da ɗa! Na tsarkaka daga in riƙi mata ko kuma ɗa!’

Kai! Faɗin cewa Allaah Ta’aala yana da ɗa wata mummunar magana ce da ta kusa ta ruguza rayuwar duniyar nan! Allaah Ta’aala ya ce

تَكَادُ السَّمٰوٰتُ يَتَفَطَّرْنَ مِنْهُ وَتَـنْشَقُّ الْاَرْضُ وَتَخِرُّ الْجِبَالُ هَدًّاۙ ٠٩۝ وَمَا يَنْۢبَـغِىْ لِلرَّحْمٰنِ اَنْ يَّتَّخِذَ وَلَدًاۗ ١٩۝

Sama ta yi kusa ta kekkece saboda shi, kuma ƙasa ta tsattsage, kuma duwatsu su rididdige; saboda sun jingina ɗa ga Allaah Mai Rahama

(Surah Maryam: 90-91)

To, ta yaya wanda ya san wannan a Musulunci zai taɓa yin tunanin samun tsira a hanyar masu faɗin irin waɗannan munanan maganganun ga Allaah Tabaaraka Wa Ta’aala?!!

Don haka, abin da ya wajaba ga duk wanda ya sani shi ne: Ya karantar da irin waɗannan mutanen sahihin addinin musulunci. Kuma kar a kuskura a mayar da maganganunsu abin dariya ko raha. Domin ko kusa abin ba na dariya ko annashuwa ba ne. Laifin kan iya shafar waɗanda suka yi sakaci wurin karantar da su ma. Allaah ya kyauta.

Amma game da matsayinsu a lahira, wannan kam yana wurin Allaah Ta’aala ne Masanin ɓoye da bayyane na dukkan al’amura. Idan a haƙiƙa iyakan ilimin mai irin wannan raayin kenan, kuma tsoron Allaah ne manufarsa ga hakan, to zai iya yiwuwa Allaah ya yafe masa, kamar yadda ya yafe wa wanda ya yi wasiyya ga yayansa cewa: Bayan mutuwarsa su ƙona gawarsa, kuma su sheƙe tokar a cikin iska, don gudun kar Allaah ya kama shi!

Idan kuma shegantaka ce da sakaci wurin neman gaskiya, to wannan al’amarinsa a fili ya ke.

Allaah ya kiyaye!

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah.

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments