Jinin Al'ada Yana Min Wasa Silar Family Planning

    TAMBAYA (52)

    Assalamu alaikuma, dama tambayar tawa an yi min planing ne taxarar haihu jini kuma yana yi min wasa nayi kokarin na hakura da planing din amm hakan be yiyuwaba sakamakon cs da aka yimn 2times a ynx haka ban yi sati biyu dagama al'ada sai ga sabin jini kuma har yana bin cinyoyina mene ne matsayin wnn jini, sanna kuma ni bana al'ada 2times a wata daya

    AMSA

    Waalaikumussalam, Warahmatullahi, Wabarakatuhum. Idan kin kasance alal misali kina jinin haila na kwana 6 a farkon kowanne wata kuma yana daukewa to jinin da ya biyo baya wannan ba jinin haila bane, na istihala ne. Da hujjar hadisin Nana Aisha (RA) tace: Fatima Abi Hubaish ta tambayi Annabi (SAW): Na kasance ina zubar da jini a tsakanin jinin aladata. Zan daina sallah idan naga jinin ? Sai Annabi SAW ya ce: "A'a zaki daina sallah ne kadai a lokacinda kike jinin alada idan kin tsarkaka sai ki ci gabada sallolinki" Bukhari, Volume l, P.194, Hadith # 322

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.