Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Matar Aure Da Ta Yi Zina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wai matar aure ce wadda mijinta kan yi shekara bai sadu da ita ba saboda yanayin aikinsa na tafiye-tafiye, shi ne ta shiga ‘sex chat’ da samari har hakan ya kai ta ga yin zina da waninsu, daga baya kuma ta tuba. Sai kuma ta sake samun wani suka ci gaba da ‘romance’ amma ba da saduwa ba. Wai duk wannan saboda ita mai ƙarfin shaawa ce da har ba ta iya yin barcin dare ba tare da ta kalli blue film ba! Yanzu dai wai so ta ke ta ji hukuncinta da kuma ko wace shawara malam zai ba ta?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

[1] A fahimtata matsalar wannan baiwar Allaah ba ƙarfin shaawa ba ce, amma dai ƙarfin shaiɗan ne kawai a kanta, da kuma ƙarancin ƙarfin imani a cikin rarraunar zuciyarta. Kuma abin da ya nuna hakan shi ne:

Hirar batsa da samari ta hanyar wayoyin hannu.

Ƙulla alƙawarin haɗuwa da su a wani wuri keɓantacce.

Kaɗaita ko zama tare da waninsu a wani wuri.

Duk waɗannan sun ci karo da abin da Ubangijinmu Ta’aala ya yi hani a kansa a cikin Alqur’ani, inda ya ce:

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا

Kuma kar ku kusanci zina, haƙiƙa ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Surah Al-Israai: 32).

Don haka: Mace musulma mai aure ta ci gaba da shirya irin wannan haɗuwar da wanda ba mijinta har ya kai ta ga yin zina.

Bayan kuma ta san hukuncin da Ubangiji Ta’aala ya yanke a kan wannan laifin shi ne a kashe ta ta hanyar jefewa da duwatsu, a gaban jama’a kuma ba tare da tausayi ba.

Haka kuma ta sake samun wani saurayin a bayan wai ta tuba, domin ci gaba da wannan aikin saɓon.

Ga kuma da’awarta na kasa yin barcin dare a bayan haka, wai har sai bayan an kalli fil

m da ke nuna batsa da jima’i a fili ƙarara!

Duk waɗannan sun nuna irin mallaka da kaka-gida da munanan shaiɗanu suka yi a cikin zuciyar wannan baiwar Allaah, don haka duk ƙoƙarinta na tuba da son komawa ga hanyar Allaah, sai su kuma suke ƙara yaudararta don neman sake mayar da ita a kan hanyarsu. Kuma in ba ta yi gaggawan ɗaukar matakan da suka dace ba, to nan ba da daɗewa ba za ta sake komawa ga aikata wannan laifin na zina da wannan sabon saurayin shi ma!!

[2] Tabbas wannan irin mijin mai irin wannan ɗabi’ar bai kyauta ba:

Kana da mata mai ƙarfin shaawa irin wannan, amma ka sa kai ka yi ta tafiya abinka, ka manta da ita da buƙatarta!

Menene amfanin duk wani abin da za ka samo na alatun duniya, idan ma har ka samo shi ɗin, matuƙar matarka ba ta zama matar kirki saliha ba?!

Wajibinsa ne ya tsare matarsa, ya hana ta bin maza ta hanyar biya mata buƙatar shaawarta na saduwa da gwargwadon ikonsa da iyawarsa.

Ko shakka babu! Akwai cutarwa mai girma a ce miji ya daina kusantar matar aurensa har na tsawon shekara.

Maganin wannan matsalar sai dole ya rage irin wannan tafiyar, ko kuma ya riƙa tafiya tare da ita. In kuwa hakan ba zai yiwu ba to sai dai ya ba ta takarda, watau: Ya sake ta kawai.

[3] Amma fa dole wannan matar ta san cewa wannan mummunan halin na mijinta bai ba ta dama a shari’a ta shiga bin maza ba. Wajibi ne ta san cewa: Malamai sun saɓa wa juna game da hukuncin matar aure idan ta yi zina. Shin ko aurenta ya warware da yin hakan, ko bai warware ba?

Sahihiyar magana dai: Bai warware ba. To, amma kuma ko ya halatta mijin ya ci gaba da zama da ita?

Abin da Al-Imaam Ahmad (Rahimahul Laah) ya zaɓa a nan shi ne: Gara mijin ya sake ta kawai, in dai ba da wani dalili ba. Domin ba shi da aminci a kan watarana ba za ta samo wani ɗa daga zina kuma ta shigar da shi a cikin ’ya’yan gidansa ba. (Al-Mughnee: 6/604).

A taƙaice dai: Shawarata ga wannan baiwar Allaah ita ce:

1. Ta tuba ga Allaah tuba na gaskiya ta hanyar: Damuwa da yin kukan zuci da baƙin-ciki a kan waɗannan laifukan da ta aikata a baya.

2. Kuma ta ɗaura niyya ƙaƙƙarfa a kan cewa ba za ta sake komawa ga aikata wani saɓo makamancin wannan ba.

3. Kar ta sake kiran waya ko ɗaukar wayar duk wanda ta san shi ne ya nuna mata hanya, ko wanda ta san sun taɓa yin wannan ɓarnar da shi a baya.

4. Ta rabu da dukkan mutanen da suke zuga ta ga aikata wannan abin, ko da kuwa dangi ko abokai ko ƙawaye ne na ƙut-da-ƙut.

5. Ta ɗauki layin wayar da ta saba amfani da shi wurin hira da tattaunawa da samarin ta karairaya shi, ta sake wani sabon layi domin magana ko tattaunawa da mutanen kirki.

6. Ta share dukkan hotuna da fina-finai na batsa da makamantansu daga kan wayarta ko ko futarta ko kuma sim-card ɗin ta.

7. Ta ci gaba da yawaita istighfari da roƙon Allaah ya yafe mata laifuffukan da ta aikata.

8. Ta duƙufa wurin biyayya ga Allaah da kafewa wurin bin Sunnar Manzon Allaah (Sallal Laahu alaihi Wa Alihi Wa Sallam) da gwargwadon ikonta.

9. Ta riƙa yawaita yin azumin nafila a kan koyarwar Sunnah Sahihiya don fatar Allaah ya rage mata kaifin shaawarta na jimai.

10. Idan ta ga ba za ta iya haƙuri da mijinta mai barinta har shekara ba da saduwa ba, to ta gaya masa don ya rabu da ita, ta samu wani mijin da zai dace da ita.

WALLAHU A'ALAM

Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments