Yadda Masabuki Zai Ciko Sallar Da Ta Kuɓuce Masa

    𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

    Idan Mutum ya samu raka'a biyu a Sallar Ishā'i to idan zai kawo sauran raka'o'i biyun da bai samu ba tare da liman Shin a ɓoye zeyi karatunsu ko kuma abayya ne??

    𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

    Alal-Haƙiƙa Wannan wata Mas'alace da Malamai sukayi Saɓani akanta, Mazhabin Mālikiyya, da Hanafiyya, Suna ganin cewa duk abin da Masabuƙi ya riska a tare da Liman to wannan abin shi ne ƙarshen Sallarsa, danhaka ke nan idan Liman ya yi Sallama to abin da zai tashi ya kawo daga baya sukace yazama Shi ne farkon Sallarsa, danhaka ke nan kamar ramuwa ce zai tashi ya yi bawai ciko ba, Misali: idan Masabuƙi yariski raka'a 2 tare da Liman a Sallar Ishā'i to idan ya tashi zai kawo sauran raka'o'i biyun to zai karanta Fātiha da Sura ne kuma zeyi karatunsu abayyane:

    Amma wasu daga cikin Malaman kamar na Mazhabin Shāfi'iyya da Hanābila, Sukace ā'ā ciko ne zeyi ba ramuwa ba, danhaka idan Liman ya Sallame to zai tashi ne yakawo sauran raka'o'i biyun dake kansa, kuma zai karanta Fatiha ne kaɗai Sannan kuma aɓoye zeyi karatun bawai a bayyane ba,

    Alal-Haƙiƙa dukkanin waɗannan ɓangarori guda biyu na Malamai da sukayi wannan Saɓani sun kafa Hujjarsu ne dawani Hadisi na Mαɳɳ Allαh() da yake cewa:

    فما أدركتم فصلوا، وما فاتكم فأتموا،

    (رواه البخاري ومسلم)

    MA'ANA:

    Duk abin da kuka riska (tare da Liman a Sallah) to ku Sallace shi, abin da kuma yakuɓuce muku (na raka'o'i) sai ku yi cikonsa:

    Awata ruwayar kuma sai ya ce:

    وما فاتكم فاقضوا،

    (رواه أبو داود والنسائي)

    MA'ANA:

    Abin da yakuɓuce muku (na raka'o'i) sai ku ramashi:

    To su Malaman da sukace ramuwa ce za ayi sun kafa hujjarsu ne da ruwayar datace

          (فاقضوا)

    Sukuma Malaman dasuka ce a'a Ciko za ayi sunkafa hujja ne da ruwayar datace

          (فأتموا)

    Sannan kuma Su Malaman da sukace Ciko za ayi sukace ai ita ma kanta ɗaya ruwayar da ta ce ramuwa za ayi Ma'anarta shi ne ciko ake nufi da'ita bawai ramuwa ba, tun da dama akwai hakan dayawa acikin harshen larabci, kaman Faɗin Allαн():

    فإذا قضيتم مناسككم،

    (البقرة/الآية200)

    MA'ANA:

    Idan kuka Ƙare (kuka cika) aikinku na Hajji kukayi yanka:

    Da kuma inda Allαн() ya ce:

    فإذا قضيت الصلاة فانتشروا في الأرض،

    (سورة الجمعة/الآية10)

    MA'ANA:

    Yayin da kuka Ƙare (kuka cika kuka idar da) Sallah, to kuwatsu abayan Ƙasa (domin neman halal)

    Danhaka sukace ita ma Ciko ake nufi da'ita bawai ramuwa ba,

    Danhaka Malamai sukace Magana mafi inganci cikin waɗannan zantuka na Malamai shi ne cewa ciko ne kawai Mutum zeyi ba ramuwa ba, Misali: idan Mutum yasamu raka'a(2) a Sallar Isha'i idan ya tashi zai ƙarasa kawo abin da ya kuɓuce masa, to zai karanta FATIHA ne kaɗai kuma aɓoye cikin dukkan raka'o'i biyun da zai kawo, haka hukuncin yake a sallar magariba ma.

    шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

       Mυѕтαρнα Uѕмαи

        08032531505

    Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

    𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

    https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

    𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

    Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

    𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

    https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

    ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

    **************************

    Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

    Question and Answers in Islam

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.