Ticker

6/recent/ticker-posts

Jerantawa Wajan Ramuwar Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Idan Mutum Baiyi Sallar Azahar Ba, Sai Ya zo Yatarar Ana La'asar Jam'i, Zai Iya Binsu Da Niyyar Azahar Idan Aka Idar Sai ya yi La'asar Ɗinsa?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 الحمد لله.

Wajibine jerantawa wajan ramuwar sallar data wuce mutum amazhabar jamhur ɗin malamai.

Ibnu ƙudama Allah yajiknasa darahma acikin Almugniy ( 1/352) ya ce: Adunkule wajibine jerantawa wajan ramuwar sallolin dasuka wuce mutum.

Imamu Ahmad yafaɗi hakan agurare da dama, da naka'iy da zuhuriy da rabee'ah, da yahyal Ansary da malik, da lais da Abu hanifah, da ishaƙ.

Imamu shafi'i ya ce: Bawajibi ba ne domin ramuwar sallar data wuce ba wajibibane jerantasu, . . . . kamar azumi idan jerantawa yatabbata to wajibine jeranta azumi ko da mai yawane, Ahmad yafaɗi haka awani wajan.

Abu hanifa da malik sukace: Badole ba ne jeranta sallolin ba idan wacce takubecewa mutum sun haura sallar dare dawuni ɗaya, saboda lura dacewa abunda yakaru a kan sallolin dare dawuni zaiwa mutum wahala, zaikuma ci gaba damaimaitawa, saboda haka jerantawa tafaɗi akansa, kamar jerantawa wajan rama azumi.

jerantawa wajibine awajan jamhur ɗin Hanafiyyah da malikiyyah dahanabila, saidai Abu hanifa da malikiyyah basa wajabta jerantawa idan ramuwar sallar yakaru a kan sallolin wuni da na dare.

Yanda ake jerantawar shi ne mutum ya zo da sallar ayanda jerangiyarsu take, misali wanda azahar da la'asar suka kubuce masa, to inya zo ramasu zaifara yin azaharne sannan sai ya yi la'asar.

Saidai wajabcin jerantawa yana faɗuwa a kan mutum abisa mantuwa ko rashin sani kokuma tsoran fitar lokacin sallar da lokacinta yake bai fitaba, dakuma tsoran kubucewar jam'i abisa Zance mafi rinjaye.

Misali idan ana binka salloli biyu, azahar da la'asar saikafara yin la'asar kafin azahar abisa mantuwa korashin sani wajabcin jerantasu sallarka ta yi babu komai akanka.

Ko kuma kanajin tsoran fitar lokacin sallar la'asar muktari zaifita kafin kai azahar, zakai la'asar daka baya kai azahar ɗin.

Haka dazaka shiga masallaci katarar an tayarda jam'in sallar dalokacinta yake.

shin za ka fara sallar ramuwane ko zakabi jam'in wacce akeyi?

Imamu Ahmad awata ruwaya daka gareshi wacce shaikul Islam ibnu taimiyyah yazaba cewa jerantawa yafaɗi a kan mutum idan yana tsoran rasa jam'i.

Saidai alokacin mutum zaibi, jam'i daniyyar rama sallar wacce ake binsa, kamar wanda ake binsa sallar azahar saiyatarar ana jam'in la'asar zaibi jam'in daniyyar azahar, ban-banci niyyarsa data limaminsa ba zai masa komaiba, idan aka idar sai ya yi la'asar ɗin.

Sharhin mumti'i Ala zadul mustaƙni'i ( 2/138-144)

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam


Post a Comment

0 Comments