𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Malam Mene ne Hukuncin muryar mace, na ji wasu na cewa Al'aura ce, wasu
Kuma suce a'a ba al'aura bace. Mene ne gaskiya? Saboda Ina so na fara yin Waka
ne.
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
A zance mafi inganci muryar mace ba al'aura ba ce, sai dai idan ta rangwada ta,
siranta ta kuma yana fitinar mutane, ta kuma tsawaita hakan. Allah Yana cewa:
. . . فَلَا تَخْضَعْنَ بِالْقَوْلِ فَيَطْمَعَ الَّذِي فِي قَلْبِهِ مَرَضٌ وَقُلْنَ قَوْلًا مَعْرُوفًا ٢٣
Kuma kar ku riƙa lanƙwasa murya da Magana, sai wanda akwai cutar
munafunci a zuciyarsa ya yi ɗammani.
Amma dai ku faɗi
magana sananniya a shari’a. (Surah Al-Ahzaab: 32).
Sana’ar waƙa dai haram ce a mafi ingancin bayanin da malaman
Sunnah suka yi, sai kuma ga shi mafi yawa a yanzu sun yawaita a zamani nan namu
suka ɗauke
shi hanyar tare dukiya. Waka ta haramta ga maza, kuma haramcin ya fi tsanani ga
mata.
Al-Imaam At-Tirmiziy (Lamba: 2373) ya riwaito hadisin Imraan Bn Husayn
(Radiyal Laahu Anhu) wanda Al-Albaaniy ya sahhaha shi cewa: Manzon Allaah
Annabi Muhammad (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya ce:
« فِى هَذِهِ الأُمَّةِ خَسْفٌ وَمَسْخٌ وَقَذْفٌ »
A cikin al’ummar nan za a samu girgizar ƙasa da shafe mutane da
jifa da duwatsu daga sama.
Da aka tambaye shi yaushe ne hakan zai auku? Sai ya ce:
« إِذَا ظَهَرَتِ الْقَيْنَاتُ وَالْمَعَازِفُ وَشُرِبَتِ الْخُمُورُ »
Idan zabiyoyi (’yan mata mawaƙa) da kayan kiɗa suka bayyana, kuma aka sha giyoyi. (Sahih
Al-Jaami’: 4273).
Waka Yana halatta ga mace alokacin bukukuwa da lokuta idi a cikin su ta yi, su ma
sai in matan ne kaɗai, da
lafuzan masu kyau waɗanda
babu gurmi a ciki.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www. facebook. com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.