Ticker

6/recent/ticker-posts

Ya Nemi A Biyasa Sadakinsa Don ta ce Ya Saketa Saboda Baya Haihuwa?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assslam alaika Dr don Allah a taimakamin da amsar wannan tambaya koya halatta mutum ya ce matarsa ta biyasa sadakinsa domin ta nemi ya saketa don baya haihuwa ?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

To ɗan uwa asali a shari'a anayin kul'ine ya yin da mace ta nemi mijinta ya rabu da ita ma'ana ya saketa batare da wani uzuri ba matukar mace ta nemi mijinta ya rabuda ita babu uzuri babu dalili, to yanada yan'cin da zaice a biyasa sadakinsa, domin yaje yakara wani auren wannan shi ne abin da shari'a ta ce

Amma a wannan hali matar nan tanada uzuri saboda baya haihuwa kuma daga cikin manufofin aure a shari'a shi ne asamu hayayyafa to shikuma baya haihuwa, ita kuma taga bazata iya hakuri ta zauna ta ci gaba da rayuwa da mutumin da baya haihuwa ba saita nemi ya sawwake mata ta je ta yi aure to anan ba shida yan'cin da zaice saita biyasa sadakinsa domin kuwa ya riga ya cinye sadakinsa kuma ya ci moriyarta ya amfana da ita sannan kuma tanada uzuri a shari'a sannan ko'a sharia za a iya raba wannan auren saboda tanada uzuri, don haka ya sawwake mata shikuma ya nemi wadda za ta iya hakuri da zama da shi har lokacin da Allah zai ba sa lafiya

Allah shi ne mafi sani

Amsawa

Dr Abdallah Gadon kaya

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments