Ticker

6/recent/ticker-posts

Tsinannun Mata

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Wai waɗanne mata ne Allaah ya tsine musu bayan masu aske gashin gira (shaving)_ da masu ƙarin gashi (attachment)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

 Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh._

Al-Imaam Al-Bukhaariy (5934) ya riwaito daga A’ishah Ummul-Mu’mineen (Radiyal Laahu Anhaa) ta ce: Wata budurwa ce daga cikin Ansaar ta yi aure, sai kuma ta yi rashin lafiya har gashinta ya kakkaɓe, sai suka yi nufin sada mata da wani, sai suka tambayi Annabi (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam), sai ya ce:

« لَعَنَ اللَّهُ الْوَاصِلَةَ وَالْمُسْتَوْصِلَةَ »

Abin da Allah Ya sanya shi ganĩma ga ManzonSa dagamutãnen ƙauyukan nan, to, na Allah ne, kuma na ManzonSa ne kuma na mãsu dangantaka da mãrayu da miskĩnai da ɗan hanya(1) ( matafiyi) ne dõmin kada ya kasance abin shãwãgi a tsakãnin mawadãta daga cikinku kuma abin da Manzo ya bã ku, to, ku kama shi, kuma abin da ya hane ku, to, ku bar shi. Kuma ku bi Allah da taƙawa. Lalle, Allah, Mai tsananin uƙũba ne.

Allaah ya tsine wa mai sadar da gashi, da mai neman a sada mata.

Al-Imaam Muslim (5695) kuma ya riwaito daga Abdullaah Bn Mas’uud (Radiyal Laahu Anhu) cewa, shi ya ce:

« لَعَنَ اللَّهُ الْوَاشِمَاتِ وَالْمُسْتَوْشِمَاتِ وَالنَّامِصَاتِ وَالْمُتَنَمِّصَاتِ وَالْمُتَفَلِّجَاتِ لِلْحُسْنِ الْمُغَيِّرَاتِ خَلْقَ اللَّهِ »

Allaah ya tsine wa masu yin zane a fatar jiki, da masu neman a yi mata zanen; da masu aikin aske gashin fuska da masu neman a aske musu; da masu yi wushirya domin ƙara kyau, masu sauya halittar Allaah.

Da labarin ya kai ga wata mace a cikin ƙabilar Banu-Asad mai suna Ummu-Ya’quub wacce makaranciyar Alqur’ani ce, sai ta zo wurinsa ta ce: Wane labari ne nake ji wai kai ka tsine wa masu yin zane a fatar jiki, da masu neman a yi masu zanen; da masu aikin aske gashin fuska da masu neman a aske musu; da masu yi wushirya domin ƙara kyau, masu sauya halittar Allaah.

Sai Abdullaah ya ce: Me zai hana ni in tsine wa wadda Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa Sallam) ya tsine wa, alhali kuma yana cikin Littafin Allaah?

Sai matar ta ce: Haƙiƙa! Na karanta abin da ke tsakanin bango biyu na Alqur’anin amma ban gan shi ba!

Sai ya ce: Idan dai har kin kasance kina karanta shi, to tabbas da kin same shi. Allaah Mabuwayi Mai Girma ya ce:

 ۚ وَمَا آتَاكُمُ الرَّسُولُ فَخُذُوهُ وَمَا نَهَاكُمْ عَنْهُ فَانْتَهُوا ۚ

Kuma duk abin da Manzon ya ba ku sai ku karɓe shi, kuma duk abin da ya hane ku sai ku hanu. (Surah Al-Hashr: 7)

Sai matar ta ce: Amma ai yanzun nan na ga matarka da wani abu irin wannan!

Ya ce: Tafi ki duba dai.

Sai ta shiga wurin matar Abdullaah amma ba ta ga komai ba, sai ta dawo ta ce: Ban ga komai ba.

Abdullaah ya ce:

أَمَا لَوْ كَانَ ذَلِكِ لَمْ نُجَامِعْهَا

Amma in da akwai wannan abin ai da ba mu zauna da ita ba.

A taƙaice dai waɗanda aka tsine wa daga cikin waɗannan hadisan su ne:

(i) Masu sana’ar sadar da wani abu a gashin kai.

(ii) Masu nema a sada musu wani abu a cikin gashin kansu.

(iii) Masu sana’ar yin zane a fatar jiki (tattooing).

(iv) Masu neman a yi musu zane a fatar jikinsu.

(v) Masu aikin aske gashin fuska.

(vi) Masu neman a aske musu gashin fuskarsu.

(vii) Masu neman a yi musu wushirya.

MALAMAI SUKA CE:

(i) Ma’anar Tsinuwa ita ce: Nisanta daga samun Rahamar Ubangiji a duniya da Lahira. Wannan kuma dalili ne a kan cewa wannan aikin haram ne, shi ya sa aka siffata mai aikatawa da tsinuwar Allaah.

(ii) Daga maganarsa cewa: ‘domin ƙara kyau ana fahimtar cewa abin ƙi kawai shi ne ga wadda ta aikata hakan saboda neman ƙarin kyau. Amma idan ta buƙatu ga hakan ne, kamar domin magani misali, to ya halatta.

(iii) Kuma maganarsa: ‘Masu sauya halittar Allaah’ wannan siffa ce ta dukkan masu aikata kowanne ɗaya daga cikin ayyukan: Sada gashi, zane a fatar jiki, aske gashin fuska. Ba wai masu yin wushirya kaɗai ba.

(iv) A cikin As-Silsilah As-Saheehah (2792) ya kawo maganar Al-Imaam At-Tabariy (10/377) cewa:

 ‘Bai halatta ga wata mace ta sauya duk wani abu daga cikin halittar da Allaah ya halicce ta da shi ba, ta hanyar yin ƙari ko ragi don neman ƙarin kyau, ko da domin miji ne ko kuma ma wanda ba miji ba. Kamar wacce gashin giranta guda biyu suka haɗe, sai ta yi ƙoƙarin gusar da abin da ke a tsakaninsu. Ko wacce take da goyo a haƙoranta ko take da haƙori mai tsawo, sai ta je ta cire shi. Ko mai gashin gemu ko gashin baki ko gashin haɓa, sai ta je ta tsittsige ko ta aske shi. Haka ko wacce take da gajeren gashi sai ta je ta tsawaita shi, ko mai gashi mara kyau sai ta je ta sauya shi. Duk waɗannan sun shiga cikin hanin da ya zo a cikin wannan hadisin, kuma sun shiga cikin masu sauya halittar Allaah Ta’aala. Sai dai daga cikin wannan ɗin an togace (watau an cire) duk abin da ke janyo cutarwa ko takurawa, kamar wadda take da haƙori mai goyo ko mai tsawo wanda kuma yake takura mata a wurin cin abinci.’

Duk wannan ya nuna yadda musulunci ya damu da wannan al’amarin na kwalliyar mata, saɓanin yadda waɗansu musulmi a yau suke yin sako-sako da shi, kuma suke ɗaukar shi ba da muhimmancin da ya cancance shi ba.

Allaah ya ƙara mana shiriya gaba-ɗaya.

 WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments