𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum Malam. Inada Ɗan'uwa Wanda yaka sance mai naci akan soyayya. Amma kuma duk
wacce ya tunkara saita ce ba ta sonsa tanada Wanda takeso alhalin kuma tsakani
da Allah shi yake sonta. Shi ne Malam nace koh akwai wata Yar bayani akan hakan
koh wata addu'a da za a bamu. Na gode malam..
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus
salam.. Abun da zai yi shi ne:
1. Ya kasance
mai addini da kuma dabi'u nagari; ya kyautata tsakaninsa da mahaliccinsa da
kyau.
2. Ya kasance
yana da abun yi wato yana da sana'a ko aiki wanda aqallah zai iya daukar nauyin
kansa da kuma ita wadda zai kawon. Kada ya zamo ɗan
zaman kashe wando.
3. Ya kasance
mai tsafta daidai gwargwado. Bafa gaye nake nufi ba, a'a mai tsafta.
4. Ya tabbatar
ya tashi yin auren. Iyaye da magabatan yarinya suna dubawa su gani shin wanda
keson 'yarsu shin tabbas ya tashi aure kuwa; suna duba sa'ana, aiki, muhalli
etc. Wannan matsalar tana ɗaya
daga cikin matsalolin da mu matasa muke fuskanta wajen neman aure kuma mune ke
jefa kanmu a ciki da kanmu, za ka ga mutum yaje ya nemi 'yar mutane alhali ya
san bai shiryawa auren ba, yai ta wahalhalu da ita shekaru da dama, sai kaga
lokaci guda wanda ya fi shi shiryawa ko wanda ya fi shi kuɗi ya zo ya kwace masa ita
sai kaga ta aje shi gefe ta kama wancan. Ko kuma kaga har yarinya ta cika sosai
ta isa aure matuka har iyayen yarinyar su fara gajiya da ganinta hakan su gaya
masa ya shirya alhali gashi bai shirya ba, sai kaga an watse lamari sai kuma ya
fara ganin laifinsu (iyayen yarinyar). To dama tun farko an kaucewa shari'ah ai
dole a samu matsala.
5. Sai kuma ya
cire ruwan ido, ya daina zuwa wajen wadanda ya san sun fi qarfinsa, ya dinga
zuwa wajen daidai level ɗinsa.
Eh! Kowa ya san akwai daidai da shi wajen aure. Gaskiya 'yan uwa samari wasu
lokuta muke jawa kanmu raini da wulaqanci saboda wata kai da kanka kasan tafi
qarfinka amma kuma sai ka ce kai ita kake so. za ka ga irin wannan auren koda
iyayen yarinyar sun tilastawa yarinyar sun ba saurayin, to koda anyi auren idan
yarinyar ba ta cire abin da ke ranta ba sai kaga mijin ba zai ji wani daɗin auren ba kwata-kwata
wato in har ma auren ya dore bai wargaje ba ke nan.
To in shaa
Allahu idan mutum ya cika waɗannan
sharuɗɗan da ke a
sama kuma ya je wajen daidai da shi to lallai yarinyar za ta aminta da shi da
yardar Allah. Gaskiya ba mai son ba mutum maras addini da maras abin yi 'yarsa
ko qanwarsa. Sauran sharuɗɗan
kuma na yarinyar ne saboda kaima na san baka son qazama, kucaka, ko wadda kake
ganin ba level ɗinka
ba ce.
WATA 'YAR
FADAKARWA:
Gaskiya matasa
mu tashi zuwa neman ilmi na addini dana boko gaba ɗayansu, sa'annan kuma mu tashi zuwa neman kuɗi ta hanyar sana'o'i da
sauran ayuka. Ɗan'uwa ka sani a zamaninnan ba wai kai kaje ka fara gayawa
yarinya kana sonta ba, ko ita da kanta ta ganka ta ji tana sonka aka fara
tafiya sai daga baya ta gano cewa baka cika waɗancan
sharuɗɗan ba
musamman ilimi da kuma harkar yi to za ta jefar da kai. Saboda haka mu tashi
zuwa neman ilimi da sana'a. Ka sani idan baka da abinyi to ka rufawa kanka
asiri kada ka tunkari maganar aure da 'yar mutane sai kasan ka fara sana'a.
Allah ya ba matasanmu sana'o'i da ayuka masu albarka. Ya kuma sanyawa bidarmu
albarka.
WALLAHU A'ALAM
Zauren Fatawoyi
Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.