Citation: Maikwari, H.U. & Sani, A. (2020). Tahamisin Waƙaƙƙen Ƙa’idojin Rubutun Hausa. Zaria: Ahmadu Bello University Press Ltd.
Gabatarwa
365. To fa! Ko a yanzu babbar
magana ce,
Ka da ka saki taho mu je ƙarshen
zance,
Ilimin ka haɗe ga ƙa’idojin ka
gwanance,
Bi ni
da hankali da kyau kar ka ɗimauce,
Ka ji ƙari ga mai rubutu
na haɗewa.
366. Masana sun ka ce rubutu nasararsa,
Ta dogara ne ga
wanda shi ke tsara sa,
Wanda ka rattaba
shi, tare da dokarsa,
Shi masani a
kodayaushe hikimarsa,
Gane abin da mai rubutu ke cewa.
367. Suka
ce day yawa akan kai ga wurare,
Wanda suke da
tarnaƙi, sai da kwarare,
In an ɓata da wag ga doka ta burare,
Sai ma’ana ta jagule, sai ta zurare
Da
tunanin mutum yake son rikicewa.
368. Ga
abu daf faɗi awar dai a raba
su,
To kuma babu
shawara dole haɗa su,
Doka ce ta ba da
damar a game su,
Ba a raba su ko faɗin ya nuna su,
In kuma an raba abin sai kwaɓewa.
369. Ga
tsarinsu nan idan za a kiyaye,
Ga shi ƙwata-ƙwato a fili bai ɓoye,
A bi doka a zo a zauna kai waye,
Ga rubutu a sanya ƙa’ida kar a kuranye,
Za a fahimci kowane ba ruɗaswa.
370. Mun
ware su ne daban don gane su,
Ba makawa ga ɗalibai sai su tsare su,
Su bi doka, su kyautata ga ribar su,
Sa natsuwa ka gane duk mun ware su,
Don
tawagarsu ce muhimmi ga kulawa.
No comments:
Post a Comment
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.