Ticker

6/recent/ticker-posts

Bazan Iya Zama Da Kishiya Ba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum..Don Allah ina da tambaya ne. Shin Idan nace ma mijina ya sakeni saboda ya yi aure ni kuma bazan iya zama da matar ba domin ni inada kishi. shin inada laifi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Karin aure, wani abu ne wanda Allah ya halastashi bisa bayinsa maza muminai, bisa sharuɗɗa guda biyu. Wato mutukar mutum zai iya yin adalci atsakanin matansa, kuma mutukar zai iya daukar dawainiyarsu ta ɓangaren saduwa da kuma abin da rayuwar yau da kullum take bukata.

Kamar yadda Allah ya yi isharah Qarara acikin Alqur'ani :

فَانْكِحُوا مَا طَابَ لَكُمْ مِنَ النِّسَاءِ مَثْنَىٰ وَثُلَاثَ وَرُبَاعَ ۖ فَإِنْ خِفْتُمْ أَلَّا تَعْدِلُوا فَوَاحِدَةً أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُكُمْ ۚ ذَٰلِكَ أَدْنَىٰ أَلَّا تَعُولُوا

ku auri abin da ya yi muku dãɗi daga mãtã; biyu-biyu, da uku-uku, da huɗu-huɗu. Sa'annan idan kun ji tsõron bã zã ku yi ãdalci ba, to, (ku auri) guda ko kuwa abin da hannayenku na dama suka mallaka. (Wato kuyangi) Wannan shi ne mafi kusantar zama ba ku wuce haddi ba. (Suratun Nisa'i ayah ta 3).

Don haka Manzon Allah ya Qara aure, Sahabbansa ma mafiya yawansu ba su zauna da mace guda kacal ba. Don haka ki kwantar da hankalinki ki yi hakuri kibi mijinki yadda zaku samu zaman lafiya da albarkar aure.

Abu ne sananne cewa ku mata kuna da tsananin kishi akan abubuwa da dama, amma babu kamar akan mazajenku. Wannan ba laifi bane tun da hali ne wanda yake gine azuciyar Ɗan Adam. Kuma an riwaito halaye na kishi daga wasu da yawa daga Salihan mataye tun daga kan matayen Fiyayyen Halitta har zuwa na Sahabbansa da tabi'ai. To amma wannan kishin bai kaisu zuwa ga neman sakin aurensu ko neman hana faruwar abin da tun tuni Allah ya Qaddarashi kuma ya halastashi ba.

Ya kamata kiji tsoron Allah ki yi hakuri ki zauna da Maigidanki Kasancewar rabuwarki da shi za ta iya janyo illoli ga rayuwarki ko rayuwar yaranku da kuka haifa dashi. Kuma zama da kishiya tamkar taimakekeniya ne wajen aikata aikin alkhairi (wato shi ne kulawa da maigida) kamar yadda Allah ya yi umurni :

...وَتَعَاوَنُوا عَلَى الْبِرِّ وَالتَّقْوَىٰ ۖ وَلَا تَعَاوَنُوا عَلَى الْإِثْمِ وَالْعُدْوَانِ ۚ وَاتَّقُوا اللَّهَ ۖ إِنَّ اللَّهَ شَدِيدُ الْعِقَابِ

Kuma ku taimaki juna kan ayyukan alheri da ƙarin taqawa, kuma kar ku taimaki juna a kan zunubi da ƙetare haddi, kuma ku ji tsoron Allaah; haƙiƙa Allaah Mai Tsananin Uƙuba ne. (Suratul má’idah aya ta 2)

Kuma maimakon ki samu labarin cewa maigidanki yana neman matan banza, ai gara ki samu labarin cewa zai Qara aure ɗin.

Kiyi hakuri ki ba shi haɗin kai, ki taimaka masa wajen kulawa da iyalansa har da ke aciki. Amma idan har kinga cewar ba zaki iya yin hakuri ki jure ba, babu laifi ki nemi khul'i daga gareshi. Wato ki ba shi sadaqin da zai isheshi ya auri wata matar, tare da dukkan abin da ya kashe alokacin da ya aureki. (Amma wannan agaban alqali ake warwarewa).

Amma dai ki sani cewar hadisi ya inganta daga Sayyiduna Thawban (rta) baran Manzon Allah yana cewa "Lallai Manzon Allah ya ce "DUK MATAR DA TA NEMI SAKI DAGA GUN MIJINTA BA TARE DA WANI LAIFI BA, (WATO BA TARE DA LAIFIN DA GIRMANSA YAKAI HAKAN BA) TO QAMSHIN ALJANNAH YA HARAMTA GARETA"

(Imam Abu Dawud ne ya ruwaitoshi).

Anan nake Qara baki shawarar cewa ki yi hakuri ki zauna lafiya da mijinki da kuma abokiyar zamanki. Hakika Allah yana tare da masu hakuri. Kuma yana bayar da lada mai yawa ga duk wanda ya yi hakuri ya jure musiba dominsa. Amma tabbas idan har kika matsa wa mijinki akan sai ya sakeki domin ba zaki iya zama da kishiya ba, to fa Allah yana iya jarrabarki kuma bayan kin bar gidan.

Jarrabawar nan tana iya zuwa miki ta kowanne ɓangare (ba fata nakeyi miki ba, amma abu ne da yakan faru). Kodai Allah ya jarrabeki da tsananin baqin jini, ki kasa samun wanda ma zaizo gidanku yakce yana sonki, ko kuma duk wanda zaizo sai kiga bai kai koda rabin matsayin mijinki na baya ba. Ko kuma duk wanda zaizo wajenki sai kiga shi ma yana da mata ɗaya ko biyu ko uku. Su ɗinma masu zafin kishi irinki. Kinga idan hakan ta faru, keda kanki zaki gwammace gara ma gidan mijinki gidan Uban 'ya'yanki. Shi kuma watakila sannan ya sake Qara wani auren, kuma hankalinsa ya kwanta, zai ce ba ya bukatar ki dawo gidansa. Kinga daga nan kuma rayuwarki za ta shiga wani sabon salo maras daɗi.

Kiyi hakuri ki jure ki zauna ki riƙe yaranki. Kina da wasu darajoji agun mijinki wanda ita amaryar ba ta dasu. Misali :

- Kin rigata shiga gidan, kin rigata zama dashi. Kinfi ta sanin halayensa, don haka zaki fi ta sanin yadda zaki zauna da shi lafiya. Kece uwargidansa kuma 'ya'yansa. Ita kuwa ba ta da kowa agidan. Kin rigata aure. Don haka watakila kinfi ta iya girke-girke kala-kala. Kinfi ta sanin 'yan uwan miji, da makobta da abokansa da dukkan jama'arsa. Don haka ki yi kokari ki fita tsafta, kwalliya, hakuri, kulawa da bukatun maigida, da sanin hanyoyin tattali da zama da shi lafiya.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments