Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Wanda Ya Takaita Sallama Zai Samu Lada Kamar Wanda Ya Yi Cikakkiyar Sallama?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu Alaikum warahmatullahi Wabarkatuh. Shin Ya halatta takaita sallama dawasu kalmomi, kamar ASLM ALKM ko SALAM ko WLSM? Shin Wanda ya takaita irin waɗannan kalmomi zai samu lada sallama kamar wanda ya yi Cikakkiyar Sallama (Assalmu Alaikum warahmatullahi Wabarkatuhu)?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh.

الحمد لله والصلاة والسلام على محمد وعلى آله وصحبه وسلم.

Musulmi yana da damar ya takaita sallama ga ɗan'uwansa musulmi da sigogi guda uku, banda su babu wata shiga da mutum zai takaita sallama da ita, mai amsa sallamar shi ma yana da damar takaitawa da kwatankwacin Abun da maiyi masa sallamar yatakaita masa dashi, ya ce "ASSALAMU ALAIKUM" ko "ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH" wannan ya fi nafarko falala ko "ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKATUHU" wannan ya fi falala da kuma alkhairi.

 

Mai Amsawa idan yakara akan abun da mai yi masa sallama yaimar da shi shiya fi saboda faɗin Allah madaukakin sarki:

وَإِذَا حُيِّيتُمْ بِتَحِيَّةٍ فَحَيُّوا بِأَحْسَنَ مِنْهَا أَوْ رُدُّوهَا ۗ إ

Idan Angaisheku da sallama to ku Amsa dawacce tafita alkhairi, ko kuma kumaida dai-dai da wacce akai muku. (Suratul Nisá'i: 86)

Ankarbo daka Abdullahi ɗan Abbas Allah yakara yarda agaresu ya ce: umar bin khaddab yaje wajen manzon Allah awani ɗaki nasa sai ya ce: ASSALAMU ALAIKA ya manzan Allah ASSALAMU ALAIKUM, umar yashigo? Abu dauda (5204) Shaeik albany ya inganta shi acikin sahihu Abu dauda.

Turmuzi ya ruwaito ahadisi mai lamba (2721) Manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce:( Idan mutum ya haɗu da ɗan'uwansa musulmi ya ce masa ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKA TUHU) Albany ya ingantashi acikin sahihul Turmuzy.

Ankarbo daka imran bin husaini Allah yakara yarda dasu ya ce: wani mutum ya zo wajan manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam sai yai masa sallama ya ce: ASSALAMU ALAIKUM sai Annabi ya Amsa masa sai yazauna, sai Annabi ya ce yasamu lada goma, sai wani ya zo ya ce: ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH, sai Annabi ya amsa masa sai ya ce: yasamu lada ashirin, sai wani ya zo ya ce :ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKA TUHU, sai Annabi ya amsa masa sai ya zauna, sai Annabi ya ce : yasamu lada talatin, Hadisine sahihi Abu dauda yaruwaitoshi (5195) da turmuzi(2689) Albani ya ingantashi acikin sahihul turmuzi.

Daka A'isha Allah yakara mata yarda tace: manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya ce: wannan Jibrilu ne ya ce inkaranta miki sallama amadadin sa sai tace: sai nace: WA'ALAIHISSALAM WARAHMATULLAH WABARAKA TUHU, Bukhary(3045) da muslim (2447).

Imamul nawawy Rahimahullah ya ce: Ababin yanda ake sallama, Anso wanda zai fara yiwa wani sallama ya ce "ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKA TUHU" ya zo da lamirin sunan dayake nuna mutane dayawa yake yiwa sallamar koda mutum ɗaya zai yiwa sallamar.

Shi kuma mai amsawa ya ce: WA'ALAIKUMUSSALAMU WARAHMATULLAH WABARA KATUHU, ya zo da wawul adaf wacce take nuna mutane dayawane awajan cewa "wa'alaikum" Riyazul saliheen(446).

Amma karin WAL "MAGFIRAH" tazone awasu hadisai na yin sallama dakuma amsawa, sai dai cewa ba su ingantaba, daka hadisan da aka ruwaito akan haka akwai hadisin

Sahal ibn mu'az bin Anas daka babansa daka Annabi sallallahu Alaihi wasallam, da ma'anar hadisin imaran bin husain wanda yagabata, acikin sa akwai mutum na huɗu dayazo wajan manzan Allah ya ce: "ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAHI WABARAKA TUHU WA MAGFIRATUHU" sai Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: yasamu lada arba'in, sai ya ce: haka falala take kasancewa, Abu dauda yaruwaito wannan hadisin (5196). hakika wasu malamai sun raunana wanan hadisin mai karin WAL "MAGAFIRATUHU" daka cikinsu akwai ibnul Araby Almaliky, da ibnul qayyeem, da imamun nawawy, da ibnu hajar asqalany, da Albany, Allah yajikansu.

Ibnul qayyeem rahimahullah ya ce: wannan hadisin bai tabbata ba domin yana da illoli guda uku.

1- ahadisin ya zo daka ruwayar Aba marhuum, Abdurraheem bin maimuun, kuma ba a hujja dashi.

2- acikin hadisin akwai sahal bin mu'az shi ma ba a hujja dashi.

3- Sa'idu ɗan Abah maryam ɗaya daka cikin ruwayoyin sa baya tabbatar da ruwaya, saidai ya ce ina tsammanin na ji nafi'i bin yazeed ya ce:

Zadul ma'ãd fi hadyi khairul ibada (2/417- 418).

Da kuma silsila za'ifa ta Albany (5433).

Dama sauran hadisan dasuka zo akan haka, mafi kamalar sallama shi ne ka ce "ASSALAMU ALAIKUM WARAHMATULLAH WABARAKA TUHU" mafi cikar amsawa shi ne ka ce WA'ALAIKUMUSSALAMU WARAHMATULLAH WABARA KATUHU.

Amma SALAM da ASLM ALKM waɗannan duk ba sallama ba ce, kuma mutum bazai samu ladan sallama ba in ya yisu, haka mai amsawa. komai yawan masu aikata hakan da kuma girman masu yi.

Masu kawo wata shubuha cewa wai SALAM gaisuwar 'yan Aljannace danhaka yahalatta kacewa ɗan'uwanka SALAM, saboda Allah yabada da labari cewa 'yan Alajannah idan sun shiga Aljannah sallamar su ita ce "SALAM"

"تحيتهم فيها سلام"

Sallamar 'yan aljannah ita ce salam.

Sai muce duk da wannan Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya san shi ɗan Aljannah ne, kuma sahabbansa duka 'yan aljannah ne, amma duk da haka ba a samu Annabi yana yiwa sahabbansa irin wannan sallamar ba, kuma ba a ruwaito sahabbai suna yiwa junan su, irin wannan sallamr ba, haka magabata na kwarai, to ko iya wannan ya isa rusa waccan shubuhar, haka kuma rayuwar duniya daban data aljannah, bazai iyu kadakko abun da Allah yabada labarinsa cewa 'yan Aljanna zasuyi insun shigeta ba, kadabbaka anan rayuwar duniya kuma ka ce addinine kake yi, duniya gidan Aikice dafata, aljannah kuma gidan sakamako ce, kuma baka da wani nassi daya tabbatar maka kaidin ɗan Alajannar ne, Anan duniya..

In shã Allahu za mu zo da karin bayani akan ya halatta takaita sallama dawasu kalmomi, ko kuma takaita rubuta salatin Annabi da wasu haruffa, ko rubuta kaɗaitar Allah da wasu haruffa da maganganun malamai akai, Allah ta'ala muke roko Ya karɓi ayyaukan mu, yakuma sanya mana Albarka arayuwar mu ta duniya da lahira.🤲

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments