𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
shin akwai
addu'ar da mutum zai yi yashawo kan budurwa tasoshi saboda Allah suyi aure?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
الحمد لله
Babu wata
addu'a kebantacciya cikin abun da muka sani wacce mutum zai lazimci yinta idan
yana neman aure, wacce ta tabbata daka Annabi Sallallahu Alaihi wasallam,
Saidai wajibine karoki Allah ya azurtaka da mace tagari.
Hakika Annabi
Sallallahu Alaihi wasallam yakoyar damu Addu'ar "Istikara" Ma'anarta shi
ne kanemi Allah ya zaɓa
maka abun da yake shi ne alkhairi agareka, cikin al'amura gaba ɗaya duniya da lahira,
wannan addu'a ita ce wacce jabir bin Abdullahi Allah yakara masu yarda
yaruwaito ya ce: Annabi sallallahu Alaihi wasallam yaka sance yana koyar damu
"istikara" acikin dukkan al'amura gaba ɗaya,
kamar yanda yake koya mana sura daka alqur'ani, ya ce: Idan ɗayanku yai niyyaci wani
al'amari, ya yi sallah raka'a biyu, ba ta farillah ba, saiya ce:
اللّٰهُمَّ إِنِّيْ أَسْتَخِيْرُكَ بِعِلْمِكَ، وَأَسْتَقْدِرُكَ بِقُدْرَتِكَ، وَأَسْأَلُكَ مِنْ فَضْلِكَ العَظِيْمِ فَإِنَّكَ تَقْدِرُ وَلاَ أَقْدِرُ، وَتَعْلَمُ وَلاَ أَعْلَمُ، وَأَنْتَ عَلاَّمُ الغُيُوْبِ اللّٰهُمَّ إِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الأمْرَ (وَيُسَمِّيْ حَاجَتَهُ) خَيْرٌ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِي، فَاقْدُرْهُ لِيْ وَيَسِّرْهُ لِيْ ثُمَّ بَارِكْ لِيْ فِيْهِ وَإِنْ كُنْتَ تَعْلَمُ أَنَّ هَذَا الْأَمْرَ شَرٌّ لِيْ فِيْ دِيْنِيْ وَمَعَاشِيْ وَعَاقِبَةِ أَمْرِيْ فَاصْرِفْهُ عَنِّيْ وَاصْرِفْنِيْ عَنْهُ وَاقْدُرْ لِيَ الْخَيْرَ حَيْثُ كَانَ، ثُمَّ أَرْضِنِيْ بِهِ
FASSARA:
Ya Allah ina
neman zaɓinka domin
ilminka, kuma ina neman ka ba ni iko domin ikon ka, kuma ina rokonka daga
falalarka mai girma, domin kai ne mai iko, ni kuwa ba ni da iko, kuma Kaine
masani, ni kuwa ban Sani ba, kuma Kaine masanin abubuwan fake, Ya Allah! Idan
kasan cewa wannan al'amari (sai ya ambaci bukatar tasa) alheri ne gareni a
cikin addinina, da rayuwa ta, da kuma karshen al'amarina, - a wata ruwayar da
magaggaucin al'amarina da majinkircinsa - ka qaddara mini shi, kuma ka saukake
mini shi, sannan ka albarkaceni a cikin sa, kuma idan kasan wannan al'amari
sharrine a gare ni a cikin addinina, da rayuwata da qarshen al'amarina - a wata
ruwaya; da magaugaucin al'amarina da majinkircinsa - Ka kawar da shi daga gare
ni, kuma ka kawar dani daga gare shi, kuma ka kaddara mini alherin a duk inda
yake, kuma ka sanya ni in yar da shi.
Bukhari (
1109).
Dangane da
miji Annabi sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( idan wanda kuka yarda da
addininsa da halayensa ya zo neman auren 'yarku ku aurar masa, idan ba hakaba
fitina za ta auku aban qasa da fasadi mabayyani,) Turmuzi ( 1084) da ibnu majah
( 1967).
dangane da
Mace: Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya ce: ( Ana auren mace saboda abubuwa
huɗu:
1. kyawunta
2. Nasabarta.
3. Dukiyarta
4. Addininta.
kanemi
ma'abociyar addinin za ta hutar da hannuwanka ) Bukhari (4802) da Muslim (
1466).
Alhafiz ibnu
hajar rahimahullah ya ce: Ma'anar mace taka sance mai addini, addini yaka sance
shi ne abun da mutum yake dubawa akan komai, musamman akan abun da za ka daɗe kana zama dashi, Sai
Annabi Sallallahu Alaihi wasallam ya Umarceshi da ma'abociyar addini, wanda shi
ne kololuwar abun nema, fat-hul bari ( 9/135).
Wannan shi ne abun
da za ka mai da hankali a kansa wajan dacewa dasamun mace tagari maisonka don
Allah kuyi aure.
WALLAHU A'ALAM
Questions And
Answers According To Qur'an And Sunnah. Join Us...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂��𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.