Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Mai Yin Istimna'i Zai Tashi Ranar Lahira Hannunsa Ya Ɗauki Ciki?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu allaikum mallam yaya ingancin fadin da akeyi kancewa duk maiyin istimna'i Zai tashi ranar lahira hannunsa Ya dauki ciki?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Hadisin dayayi wannan maganar mai raunine (DA'IFINE) amma dangane da ISTIMNA'I hukuncinsa a musulunci haramun ne, dalilin fadin Allah Madaukakin Sarki acikin Alqur'ani suratul ma'arij 29-31:

وَالَّذِينَ هُمْ لِفُرُوجِهِمْ حَافِظُونَ ٩٢۝

Da waɗanda suke, ga farjojinsu, mãsu tsarewa ne.

إِلَّا عَلَىٰ أَزْوَاجِهِمْ أَوْ مَا مَلَكَتْ أَيْمَانُهُمْ فَإِنَّهُمْ غَيْرُ مَلُومِينَ ٠٣۝

Sai fa a kan matan aurensu da abin da hannayensu na dãma suka mallaka (baiwa). To lalle ne sũkam ba waɗanda ake zargi ba ne.

فَمَنِ ابْتَغَىٰ وَرَاءَ ذَٰلِكَ فَأُولَٰئِكَ هُمُ الْعَادُونَ ١٣۝

To, duk wanda ya nemi abin da yake a bayan wannan, to, waɗancan sũ ne mãsu ƙetare iyãka.

Masana kiwon lafiyan ɗan Adam sunce mai yin istimna'i yana da matsaloli da dama musanman ga Lafiyata. Kaɗan daga ciki kawo Yawan mantuwa, rage hazaqar kwalwa, kankancewar zakari da maraina, saurin kawowa ko rashin karfin mazakuta. Sauran matsalolin dazai iya haddasawa , sun haɗa da: ramar jiki ko 'karancin sha'awa, karancin maniyyi ko tsinkewar maniyyi da raguwar ingancinsa (wanda na iya haddasa rashin haifuwa) , raunin jiki, raunin garkuwar jiki, jin ciwon kai akai-akai, ciwon baya, fitar maniyyi daga zakari hakanan ba tare da mutum ya yi niyya ba - ba tare da ya yi istimna'i ba ko ya yi jima'i, haka nan kawai. Wasu illololin da za su iya faruwa saboda istimna'i: bushewar fatar kan zakari ko illa ga fatar saboda gugar fatar, karkacewar zakari ko sauya masa sigarsa ta asali, bugawar zuciya da sauri, zubar gashi, kurajen fuska da dai sauransu..

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments