Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Annabi Muhammad ﷺ Ne Farkon Halitta?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam ina da wata tambaya wacce ta daure mun kai, idan ka san amsa don Allah ka ba ni tare da gamsassun hujjoji. Tambayata shi ne, shin Allah Annabi Muhammad ne Allah ya fara halitta? Shin wai Allah ya ajiye shi ne sai lokacin da ya gadama sannan ya zo duniya?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikum assalam, Akwai hadishin da ya zo wanda yake nuna cewa Annabi shi ne farkon wanda aka fara halitta, saidai hadishin bai inganta ba, wasu malaman hadisin, kamar Ibnu-kathir a tarihinsa da Albani a silsilatussahiha hadisi mai lamba 458, sun ce hadisin karya ne.

Faɗin cewa Annabi shi ne farkon wanda aka halitta ya saɓawa alqur'ani, ta ɓangarori da dama ga wasu daga ciki:

1. Allah ya tabbatar da cewa Annabi Muhammad mutum ne kamar yadda hakan ya zo a ayoyi daban-daban, sannan kuma Allah ya tabbatar da cewa gaba ɗaya mutane daga Annabi Adam aka same su, kin ga idan ka ce Annabi Muhammad shi ne farkon halitta hakan ya saɓawa ayoyin alqur'ani.

2. Tarihi ya zo da bayanin nasabar Annabi Muhammad tun daga mahafinsa har zuwa Annabi Ibrahim, kin ga wannan yana nuna an halicce shi ne daga maniyyin mahaifinsa, kamar yadda aka halicci ragowar mutane daga hakan.

Zance mafi inganci shi ne: Farkon abin da Allah ya fara halitta shi ne Al'arshi, kamar yadda ya zo a cikin Sahihi Muslim a hadisi mai lamba 2653, cewa: "Allah ya kaddara abubuwa kafin ya halicci sama da kasa da shekaru dubu hamsin a lokacin Al'arshinsa yana kan ruwa"

Kin ga wannan yana nuna cewa Al'arshi ne farkon abin da aka fara halitta ba Annabi Muhammad

Allah Yana cewa:

وَهُوَ الَّذِي خَلَقَ السَّمَاوَاتِ وَالْأَرْضَ فِي سِتَّةِ أَيَّامٍ وَكَانَ عَرْشُهُ عَلَى الْمَاءِ لِيَبْلُوَكُمْ أَيُّكُمْ أَحْسَنُ عَمَلًا ۗ ...

Kuma shi ne wanda Ya halicci sammai da ƙasa a cikin kwanaki shida, kuma Al´arshinSa ya kasance akan ruwa, domin Ya jarraba ku, wanne ne daga cikinku mafi kyãwon aiki... (Suratul Hud : 7)

Wasu kuma su ka ce Ruwa shi ne farko, kamar yadda aka tambayi Manzon Allah , yadda duniya ta fara, sai ya ce:

« كان الله ولم يكن شىء غيره وكان عرشه على الماء وكتب في الذكر كل شىء ثم خلق السماوات والأرض »

«Allah ya wanzu kuma babu wani abu a tare da shi. Ya halicci Al'arshi [Ya sanya shi] a saman ruwa. Sa'an nan kuma (Ya umurci Alƙalami ya rubuta) a cikin Alƙur'ani, dukan abin da zai auku. Sai Allah ya halicci sammai da ƙasa.»*

 [Bukhariy ya rawaito shi]_l

Annabi tsira da aminci su tabbata a gare shi, ya amsa wannan tambayar da fara bayyana cewa samuwar Allah ba ta da mafari, watau shi ne madawwami. Babu wanda aka jingina shi da dawwama face Shi. Watau babu abin da ya wanzu sai Allah, kuma Allah ne ya halicci komai, watau ya fitar da dukkan halitta daga babu, subhanallahu wata ala.

Allah, bai halicci dukan halittu a lokaci guda ɗaya ba. Kuma da Ya so wannan da ta auku. Amma sai ya yi hakan a cikin kwanaki shida, Ya halitta sammai da ƙasa. Kuma acikin Duniya Allah ya halicci koguna da duwatsu da kwaruruka. Wanda hikimar wannan ita ce koya mana kada mu yi gaggawar acikin al'amuran mu.

Annabi ya ce:

إِنَّ اللهَ تَعَالَى خَلَقَ كُلَّ شَيْءٍ مِنَ الْمَاءِ

«Allah ya halicci komai daga ruwa.» [Ibn Hibban ne ya rawaito shi]

Wannan kuma yana nufin Allah ya halicci ruwa kafin ya halicci haske, da duhu, da ƙasa, da sama, da Al'arshi, da Allo mai tsaro. Allah ya sanya ruwa ya zama tushen sauran halittu. Ya halitta Al'arshi daga ruwa. Sa'an nan kuma Ya halicci Alƙalami kudra, sa'an nan kuma littafin da ke ɗauke da ayyukan bayi. Bayan waɗannan halittu, sai Allah ya halicci sauran halittu: irin su kasa, sammai, dabbobi, duwatsu, bishiyoyi, koguna. Adam, tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi, ya kasance daga nau’in halittun Allah na karshe, karshe, wato mutane.

Akwai sauran bayanai da hujjoji na malamai da yawa, Kuma Allah ne mafi Sani.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments