𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
Assalamu
alaikum. Malam wanda ya bige mutum yamutu amma wanda aka bige arne ne. Shin
akwai azumi 60 akan shi?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa'alaikumus Salam
warahmatullahi Wabarkatuh
Idan wanda ka
Kashe kafiri ne Wanda shari'ah ta ba shi kariya, to anan za ka yi kaffara kuma
za ka biya diyyah ga iyalansa ko yan'uwansa. Dalili kuwa shi ne faɗin Allah maɗaukakin sarki:
...ﻭَﺇِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﻣِﻦْ ﻗَﻮْﻡٍ ﺑَﻴْﻨَﻜُﻢْ ﻭَﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻣِﻴﺜَﺎﻕٌ ﻓَﺪِﻳَﺔٌ ﻣُﺴَﻠَّﻤَﺔٌ ﺇِﻟَﻰ ﺃَﻫْﻠِﻪِ ﻭَﺗَﺤْﺮِﻳﺮُ ﺭَﻗَﺒَﺔٍ ﻣُﺆْﻣِﻨَﺔٍ ﻓَﻤَﻦْ ﻟَﻢْ ﻳَﺠِﺪْ ﻓَﺼِﻴَﺎﻡُ ﺷَﻬْﺮَﻳْﻦِ ﻣُﺘَﺘَﺎﺑِﻌَﻴْﻦِ ﺗَﻮْﺑَﺔً ﻣِﻦَ ﺍﻟﻠَّﻪِ ﻭَﻛَﺎﻥَ ﺍﻟﻠَّﻪُ ﻋَﻠِﻴﻤﺎً ﺣَﻜِﻴﻤﺎً.
...Kuma idan
ya kasance ɗaya wasu
mutãne ne (wadanda) a tsakaninku da tsakaninsu akwai alkawari, sai (Ku bada)
diyyah abar miqawa ga mutanensa, da yantawar baiwa mumina, to Wanda bai sami
(baiwar ba) sai (yayi) azumin watanni biyu jere, domin tuba daga Allah. Kuma
Allah ya kasance Masani, Mai hikima. (Sūratun Nisaa'i, Ayah 92).
Mafiya yawan
malamai sun tafi akan ra'ayin cewa yin kaffarah ya zama dole ga Wanda ya Kashe
kafiri wanda shari'ah ta bawa kariya.
Kafirai
wadanda shari'ah ta bawa kariya sun kasu kashi uku (3):
1. AL-DHIMMI: Shi
ne wanda aka yi alkawarin ba shi kariya Wanda yake Zaune a kasar musulmai ko
garin musulmai.
2.
Al-MU’AAHAD: shi ne Wanda aka yi yarjejeniyar zaman lafiya da mutanensa.
3. AL-MUSTA’MAN:
wannan shi ne wanda ya shigo kasa ko garin musulmai kuma an tabbatar da tsaron
lafiyarsa, kamar wadanda suke shigowa yin kasuwanci ko ziyarar yan'uwansu. Da
sauransu.
Duk Wanda ya
Kashe kafiri Wanda shari'ah ta bawa kariya, dole zai yi abu biyu (2):
1. DIYYAH: Zai
biya diyyah ga iyalan wanda aka kashe. Zai bayar ne idan su iyalan mamacin ba
Muhaaribeen bane (wato masu yaki da musulmai). Idan iyalansa Muhaaribeen ne, to
ba su cancanta a ba su diyyah ba, saboda jininsu da dukiyarsu ba haram bane.
(Tafseer
al-Sa’di, shafi na 277).
2. KAFFARAH:
Wannan shi ne ra'ayin mafiya yawan malamai.
Ibn Qudaamah
ya ce acikin Al-Mughni, 12/224)
Wajibi ne yin
kaffara ga kisan kafiri wanda shari'ah take kariya, sawa'un ko yaya ya kasance
dhimmi ko musta’man. Wannan shi ne ra'ayin mafiya yawan malamai.
Hassan da
Maalik sunce baza ayi kaffara ba. Saboda Allah ya ce:
ﻭَﻣَﻦْ ﻗَﺘَﻞَ ﻣُﺆْﻣِﻨًﺎ ﺧَﻄَﺄً ﻓَﺘَﺤْﺮِﻳﺮُ ﺭَﻗَﺒَﺔٍ ﻣُﺆْﻣِﻨَﺔ....
Wanda ya kashe
mumini a bisa kuskure, sai ya 'yanta baiwa Mumina.... (suratun Nisaa'i ayah 92)
Anan su
fahimtarsu shi ne baza'ayi kaffara ba idan Wanda aka kashe ba Mumini (Ko
Musulmi) bane. Wannan shi ne fahimtar Al-Hasan da Maalik.
Amma kar mu
manta Allah ya ce:
...ﻭَﺇِﻥْ ﻛَﺎﻥَ ﻣِﻦْ ﻗَﻮْﻡٍ ﺑَﻴْﻨَﻜُﻢْ ﻭَﺑَﻴْﻨَﻬُﻢْ ﻣِﻴﺜَﺎﻕٌ ﻓَﺪِﻳَﺔٌ ﻣُﺴَﻠَّﻤَﺔٌ ﺇﻟَﻰ ﺃَﻫْﻠِﻪِ ﻭَﺗَﺤْﺮِﻳﺮُ ﺭَﻗَﺒَﺔٍ ﻣُﺆْﻣِﻨَﺔ.
...Kuma idan
ya kasance ɗaya wasu
mutãne ne (wadanda) a tsakaninku da tsakaninsu akwai alkawari, sai (Ku bada)
diyyah abar miqawa ga mutanensa, da yantawar baiwa mumina...
Anan Dhimmi ya
shigo cikin jerin wadanda aka ambata a wannan ayar. Kuma wannan shi ne abin da
za a iya fahimta daga wannan ayar.
Kuma saboda
shi mutum ne Wanda aka Kashe bisa kuskure, wajibi ne ayi kaffara, kamar yadda
ake yin kaffara idan an kashe musulmi.
Wannan shi ne
ra'ayin da wasu malaman Tafsiri suka zaba, kamar Al-Tabari (9/43), Al-Qurtubi
(5/325), Ibn Katheer (2/376).
WALLAHU A'ALAM
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.