Ticker

6/recent/ticker-posts

Babana Yana So Na Aureshi Amma Mamana Ba Ta So

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mallam don Allah inason a amsa min wannan tambaya ni inada saurayi amma babana yana son na auri wannan saurayin ita kuma mamata bataso don Allah Mallam menene mafita hartakai tun ina iya jure zakin cin mutumci da rashin fatan alkhairi agareni har nadaina jurewa don Allah Mallam ina mafita kuma abin yana matukar damuna wlh.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Anan Zaki Kalli Abubuwa guda Biyar. Kamar haka :-

1. Shi wannan Saurayin da Ake tababar Aurensa, kina Sonshi ko kuma baki Sonshi? Idan baki Sonshi, to tin daga nan na sai ki dasa Aya. Idan kuma kina Sonshi, sai ki tafi mataki na biyu.

2. Shin yana da Addini? Sannan kuma yaya dabi'unsa Suke? Idan nan babu Matsala, sai ki tafi Mataki Na Ukku.

3. Zakiyi ISTIKARA Akan Al'amarin shi wannan bawan Allah din. Idan Alkhairi ne, Allah ya zaɓar Miki, idan kuma ba Alkairi bane, Allah ya chanja miki Wanda ya fi zama Alkairi a gareki.

4. Dole zaki Rinjayar da tunanin Mahaifinki akan na Mahaifiyarki. Sabida Tunanin Namiji shi ne cikakken Tunani, ba Mace ba. Amma duk da haka, Zakiyi Nazari Akan, wanne dalili ne ya sa mahaifiyarki ba ta son ki Aure shi, sannan Wanne dalili ne ya sa Mahaifinki yake son ki Aureshi? Anan Ma Zakiyi Nazari sosai.

5. Sai ki Nemi Shawarar Wata ko wani mai tunani da cikakken hankali a nan kusa da ke. In Shã Allahu idan kikabi waɗannan Channel Ɗin, zaki sami taimakon Allah.

Allah ta'ala ya sa mudace.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments