Ticker

6/recent/ticker-posts

Shin Akwai Banbancin Darajar Sallar Mai Aure Da Wanda Ba Shi Da Aure?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Menene ingancin hadisin da ke cewa sallar mai aure ta wuni ɗaya tafi ta wanda bai da aure har tsawon shekara dubu arba'in. Shin akwai banbancin darajar sallar mai aure da wanda ba shi da aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wannan hadisin karyane babu shi kwata kwata acikin littafan hadisi, kuma falalar da ke cikinsa ta saɓawa hankali da tunani, lallai musulmai su tashi sunemi ilmin addinin musulunci haikan, ire-iren waɗannan hadisai da makamantansu basune za su nuna daraja da falala da aure yake da itaba, ba kuma sune za su zaburar da matasa zuyi aure ba.

Shi ɗan bidi'a kullum yana jin saiya haɗa dabkarya da tatsuniya da kuma wasu ababe wanda hankali bazai ɗauka ba, shi aganinsa da wannan kawai zai nuna daraja da falala ta wani abu dayake san kwaɗaitar da musulmai a kansa, wanda wannan kuskurene maigirma, kuma maiyinsa da yaɗa shi yana cikin haɗari mai girma ranar alkiyama.

Babu shakka addinin musulunci ya zo da kwaɗaitarwa da kuma nuna falala ta aure wanda sukazo a harshen manzan Allah salallahu Alaihi wasallm, dakuma ayoyi na alkur'ani mai girma daga ciki akwai hadisi shahararre wanda Manzan Allah ya ce: ( Ku auri Mafi soyuwa agareku cikin mata kuma masu haihuwa, domin dayawanku zan yi alfahari ranar alkiyama)

hakama Allah maɗaukakin sarki ya ce cikin alkur'ani (yana daka cikin ayoyin Allah daya halicceku maza da mata dankuyi auratayya dajuna ya sanya kauna da soyayyah datausayi atsakaninku)

Wadannan nassoshi kaɗai sun isa suna falala ta aure domin abun da dazaka ciyar ma iyalinka murmushi kallo zance duk za ka samu lada akai haka ma kabiya bukatarka da matar taka ko tabiya bukatarta dakai shi ma duk cikin lada yake, danhaka wannan kaɗai ya isa yanuna falala ta aure basai an haɗa da tatsuniya da kuma karya ga manzan Allah sallahu Alaihi wasallam ba.

Aure yana tattare da falaloli da rajajoji masu tarin yawa wadanda Alqur'ani da Hadisai Ingantattu suka bayyana. A iya binkicenmu zuwa yanzu bamu samu wani nassi da yake nuni da fifita darajar Sallar Mai Aure da gwauro ba. Sallar Gwauro da magidanci ba ta da wani ban-bancin daraja ko lada tsakaninsu. Wanda ya fi iya sallah da kwatanta yinta yanda manzan Allah sallallahu Alaihi wasallam ya zo da ita, da yinta cikin jam'i a lokacinta shi ne abun dubawa wajan samun falala da darajar sallar mai gida da tuzuru. Duk wanda ya fi kiyayeta da cika sunnoninta da farillanta da mustahabbanta shi ne sallarsa zatafi daraja da falala... Aure ko rashinsa ba shi ne ma'aunin gane darajar sallah ko rashin taba. Saboda haka Babu wani ban-banci daraja tsakanin Sallar Mai Aure da Gwauro. Wasu zantuka da kakeji ana cewa sallar Mai Aure tafi wanda ba shi da Aure dara sau saba'in ko kaza da kaza, duk qare rayine da ba su da tushe acikin addinin musulunci.

Yawanci Gafalallune suke yaɗasu, yawancinsu daka shafukan 'yan shi'a zindiqai suke dakkowa su watsawa musulmi, saboda su dama qarya acikin addininsu kamar kalmar shahadace acikin Addinin Musulunci.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments