TAMBAYA (38)❓
Salãmun
alaikum warahmatullah, Uncle barkada yamma, Dan Allah uncle meye hukuncin
alwalar Wanda arashin sani konace bada wata manufaba wani ban gare na jikinshi
yataba wani ban gare na jikin mace. Misali idan Dr ya zo yiwa yaro allura Sai
manar yaron tariqe yaron to Sai ko hannunta kowani ban gare na jikinta yataba
jikin Dr, ko hannunsa kafin yadauke daga inda yama yaron allura itakuma takawo hanu
donta massaging din wajen,
Komisalin
yataba jikin yarinya qarama ya ji yanayin temperature jikin ta, Amma ranshi
lafiya qalau Babu wata manufa Kota misqala zarratin
AMSA:
Haramun ne
mutum namiji ya taba wadda ba muharramarsa ba
An rawaito
daga Ma'qil ibn Yassar RA ya ce: Annabi SAW ya ce: "A samu qusar qarfe a
bugawa mutum a kansa shi ne ya fi masa sauqi akan ya taba macen da ba ta halatta
a gareshi ba"
Dabarani ne ya
rawaitoshi a cikin al-Kabeer, 486. Shaykh Albani ya ingantashi a cikin Saheeh
al-Jaami' 5045
An karbo daga
Urwah, Nana Aisha RA ta ce masa: Lokacinda matan Muhajirun sukai hijira zuwa
Madina sun kasance suna Mubaya'a ne ba da musaffah ba (Gaisuwar hannu da
hannu), tace: Annabi SAW bai taba shafa hannun wata mace da hannunsa ba. Saidai
yana bayanine akan ga abin da Mubaya'a take nufi idan mace ta amince sai ya ce:
Je ki an amshi Mubaya'ar ki"
Sahih Muslim
(1866)
Haka kuma an
karbo hadisi daga Umaymah RA yar Raqeeqah RA tace: Annabi SAW ya ce: "Bana
gaisawa (musafaha) da mata"
al-Nasaa'i
(4181) da ibn Majaah (2874). Shaikh Albani ya ingantashi a cikin Saheeh
al-Jaami' (2513)
Hadisin da
al-Tabaraani ya rawaito a cikin al-Kabeer da kuma al-Awsat da aka rawaito cewar
Annabi SAW yana gaisawa da mata da karkashin hannun riga, wannan hadisi da'ef
ne (Al-Haytham ya ce bai ingantaba saboda a cikin isnadin hadisin da akwai
'Ataab ibn Harb shikuma a ilimin hadisi da'eef ne)
Majma'
al-Zawaa'id, 6/39
Shaykh Ibn
Baaz (Rahimahullah) ya ce: fadin Annabi SAW: "Bana gaisawa (musafaha) da
mata" kadai hujjace da ke kawarda duk wani hadisi wanda zai kawo shubha
(Hashiyat
Majmoo'at Rasaa'il fi'l-Hijaab wa'l-Sufoor, p. 69)
Al-Zayla'i ya
ce: Gameda riwayar da aka ce Sayyadina Abu Bakr RA yana gaisawa da tsofaffin
mata, wannan ghareeb hadis ne"
(Nasab
al-Raayah, 4/240)
Ibn Hajar ya
ce: "Ban ga wannan hadisin ba"
(al-Diraayah
fi Takhreej Ahaadeeth al-Hidaayah, 2/225)
Gaba daya
mazhabobin Hanafiyya, Malikiyya da Hanbaliyya duk sun tafi akan hukuncin taba
mace ko yin musafaha da ita haramunne
Mazhabain
Shafi'iyya kuma Imam an-Nawawi ya ce: "Haramunne taba mace ta kowacce
siga". Shi kuma Wali al-Deen al-'Iraaqi ya kara da cewar saidai idan ya
zamana idan har Annabi SAW wanda yake gudun fadawa zargi zai yi taka tsantsan
to sauran mutane su ya fi cancanta su nesanta da hakan
Manyan malamai
sun karawa juna sani akan cewar haramun ne taba jikin wadda ba muharrama ba ko
da kuwa fuskartace. Amman sun samu banbancin ra'ayi ta ban garen kallon mace
idan babu sha'awa kuma hakan bazai haifar da wata fitina. Idan ya zamana akwai
ad-darurat (larura) misali: rashin lafiya, cire haqori. Idan babu macen da za
ta iya wannan aikin to ba matsala idan mutum ya taba wadda ba muharramarsa ba
(misali: ya ji jikinta akwai zafi ko wani abu makamancin haka)
Tarh
al-Tathreeb, 7/45,46
Don haka a
takaicedai indai har babu wani abu da ya fita daga jikinsa silar sha'awa to
alwalarsa tananan in sha Allahu saboda a bisa babin larurane ya taba wadda ba
muharramar ta sa ba
Hadisin
"Innamal a'amali binniyati" shi ne zai aiki anan
Idan ya yi ne
a bisa ad-darurat (larura) to ba matsala amman idan da niyyar jin sha'awa ya yi
to haramun ne
Amsawa:
Usman Danliti
Mato (Usmannoor_As-salafy)
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.