Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mai Komawa Zunubi Bayan Tuba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum Wa Rahmatul Laah. Mutum ne zai aikata babban zunubi sai kuma ya yi nadama, ya tuba kamar ba zai sake komawa ba. Daga baya sai kuma ya ƙara komawa ga zunubin, sai kuma ya sake tuba. Haka nan dai ya ke: Bai daina zunubin ba, kuma bai daina tuban ba. Meye hukuncin wannan?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Abin da Allaah Subhaanahu Wa Ta’aala ya ce dai shi ne:

 ۞ قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ

Ka ce: Ya ku bayina, waɗanda suka yi ɓarna ga kawunansu! Kar ku ɗebe tsammani daga samun Rahamar Allaah. Haƙiƙa! Allaah yana gafarar zunubi gaba-ɗaya. Haƙiƙa Shi! Shi ne Mai Yawan Gafara Mai Yawan Jin Ƙai.

(Surah Az-Zumar: 53)

Daga wannan ayar muke fahimtar cewa:

(i) Allaah Maɗaukakin Sarki mai yalwar Rahama da yawan Gafara ga halittunsa ne, yadda yake gafarar dukkan zunubansu gaba-ɗayansu.

(ii) Wannan ya sanya dukkanmu mu zama cikin kyakkyawan fata ga Allaah cewa zai gafarta mana laifuffukanmu, kar mu zama masu ɗebe tsammani daga samun hakan.

(iii) Don haka, wajibin abin da ke kan duk wanda ya yi zunubi daga cikinmu shi ne ya tuba ga Allaah a bisa sharuɗɗan da malamai suka bayyana, kuma ya nemi gafararsa.

(iv) Sannan kuma yawan zunubin da adadin maimaituwansa ba za su zama matsalolin hana samun gafarar Allaah a kansu ba, matuƙar dai an ɗauki matakai da sharuɗɗan tuba da istigfaari.

Don haka, abin da ya wajaba a kan wannan mai maimaita zunubin shi ne ya ɗauki matakan tuban da malamai suka shimfiɗa a duk lokacin da ya aikata wani zunubi. Ya ji tsoron kar Allaah ya karɓi rayuwarsa a cikin halin zunubin ko bayan ya gama zunubin kafin ya tuba.

Muna fatar dai Allaah Ta’aala ya karɓi rayuwarmu da shi ma a bayan mun gama tuba tun kafin mu sake aikata wani zunubin.

Shi dai zunubi, kamar yadda wani malami yake cewa: Ba tilas ba ne. Haƙuri akan yi, a zauna lafiya.

Allaah ya datar da mu.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments