Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Zuwa Wajen Malamin Duba

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum Malam Ina Son Wata Yarinya Ne Sunanta Salima Ni Kuma Musa Se Naga Tana Min Wulaqanci Se Naje Wajan Wani Malami Ya Duba Min Auranmu Akwai Haske Koko Babu? Se ya ce Na Rabu Da Ita Babu Alkairi Auranmu Da Ita. don Allah Malam Ka Duba Min Akwai Haske Azamanmu Da Ita Koko Na Rabu Da Ita?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Lallai ka aikata babban kuskure da har kaje wajen Ɗan duba don ya duba maka al'amarinka. Kuma har ma gashi ka yarda da abin da ya gaya maka. Wannan laifin yana daga cikin Manyan Kaba'irori. Domin kuwa Manzon Allah ya ce : "DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KO ƊAN DUBA KUMA YA GASKATASHI GAME DA ABIN DA YAKE FAƊA,TO HAƘIƘA YA KAFIRCE MA ABIN DA ANNABI MUHAMMADU ya zo DASHI". (SALLAL LAHU ALAIHI WA SALLAM).

Acikin wani hadisin kuma wanda Imamu Muslim ya ruwaito, Manzon Allah cewa ya yi Wanda ya aikata irin wannan laifin ba za a karɓi sallarsa ta kwana arba'in ba.

Zuwa wajen bokaye yana daga cikin rashin yarda da Qaddara. Idan har ka yarda cewa Allah shi ne mai iko akan komai, kuma shi ke juya lamura yadda yaso, to mai zai hana ka dogara gareshi domin samun yayewar damuwa ko biyan bikatu!.

Lallai kaji tsoron Allah ka tuba. Domin harka da bokaye ko 'Yan duba yana daga cikin dalilan da ke janyo ma mutum lalacewar addininsa da kuma cikawa babu imani, da kuma mummunar makoma aranar Alqiyamah. Ka gaggauta tuba zuwa ga Allah Ubangijinka kuma ka dawo bisa tsantsar tasbeehi. Ka kyautata Qudurinka.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments