Ticker

6/recent/ticker-posts

Ina Tashi Sama A Mafarki Idan Miyagun Mutane Suka Biyoni

 TAMBAYA (30)

Assalam malam antashi lafiya,Allah ya karawa rayuwa albarka. Ina tambaya,mal Ina yawan mafarkin miyagun mutane nabina, sai dasun biyoni sai intashi sama,toh malam da inatashi da bacci tsoro nakeji,yanzukuma tsoro da bacin rai sukahade DANALLAH miye nufin hakan? Jazakallahu khairan!

AMSA

Idan kikai mafarki kina tseren-tsere da wani, sai kikai nasarar tsere masa (ma'ana bai kamaki ba) to hakan yana nufin zaki yi nasara akan maqiyinki kuma zaki fi shi daukaka. Mafarkin tashi a sama daga inda ka sani zuwa waje me nisa inda baka sani ba yana nufin mutuwarka.

Idan mace ta yi mafarki tana tashi a saman gidansu wani saurayi wanda ta sani hakan yana nufin za ta aureshi. Mafarkin tashi daga kasa zuwa sararin sama ba tareda fuka-fukaiba na nufin burin mutum zai cika. Idan mutum ya yi mafarkin yana kwance akan gwado kuma shi da gadon sun tashi sama hakan na nufin rashin lafiyarsa ko kuma wata rashin lafiya da za ta samu kafafunsa. Idan mutum ya yi mafarkin tashi sama daga waje mara kyau zuwa waje mai kyau kamar gona ko masallachi hakan na nufin samun riba mai kyau a sana'arsa

SHARHI

Kowa a duniyarnan yanada maqiyi, kuma indai yanda kika fada ne cewar kin ga miyagun mutane suna binki, sai kiga kin tashi sama, to hakan na nufin kina tsira daga sharrinsu silar yawan azkar

Don haka ki ci gaba da azkar na safiya da na maraice

Annabi SAW ya ce duk wanda zai karanta "A'uzu bi kalimatillahit tamma min kulli shaidanin wahamma wamin kulli aynin lamma" sau 3 da safe sau 3 da yammaci, to ba abin da zai iya cutar da shi a wannan ranar har sai abin da Allah SWT ya rubuta masa. Kuma an rawaito cewar Annabi SAW yana yiwa jikokinsa (Hassan da Hussaini) irin wannan addu'ar kamar ynda ya zo a cikin hadisin Sahihul Bukhari mai lambata 3371

Dukkan halittu (khaliqai) basuda tasiri akan sauran halittu saidai su zamo sabab (sila) amman al-Khaliqu shi kadai ne yake saka tasiri ko da sila ko kuma da QudirarSa

Ki dage da neman kariya daga sharrin mahassada da miyagun mutane

Kada ki manta da addu'o'in da Annabi SAW ya koyar ya yinda mutum zai kwanta bacci kamar irinsu Mu'awwidathayn (Falaqi da Nasi a kara da Ikhlas sau uku uku a shafe jiki ya yin kwanciya bacci) kamar yanda hadisin Sahihul Bukhari mai lambata 5748 ya tabbatar da hakan

Domin kuwa miyagun mutane suna amfani da wannan lokaci su turowa mutum abin da kan iya cutardashi idan bai yi azkar ba

Annabi SAW ya ce: "Babu abin da ke sauya qaddara sai addu'a"

Allah ya karemu ya rabamu da sharrin kawunanmu, miyagun mutane da kuma sharrin shaidan

Wallahu ta'ala a'alam

Amsawa:

Usman Danliti Mato (Usmannoor_As-salafy)

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments