Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Kasa Daina Zunubi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

 As-Salaam Alaikum. Mutum ne yake fama da matsalar aikata wani abin da ya saɓa wa shari’a. Yakan samu damuwa sosai bayan ya aikata laifin, yakan tuba, ya yi sallar dare, ya ɗauki alƙawarin cewa ba zai sake ba har abada. Akwai ma lokacin da ya yi alwashin idan ya sake zai yi azumi guda sittin! Amma kuma bayan tsawon lokaci sai ya sake komawa! To, wai menene hukuncin wannan? Me ya kamata ya yi a kan wannan matsalar?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Babu shakka saɓon Allah abune da ke haifarwa da bawa matsaloli masu yawa, amma kuma Allah mai yalwar falalane matukar mutum ya yi nadama yagane kuskuren sa ya tuba to lallai Allah mai yawan gafarta zunubaine, Allah maɗaukakin sarki ya ce:

وَتُوبُوا إِلَى اللَّهِ جَمِيعًا أَيُّهَ الْمُؤْمِنُونَ لَعَلَّكُمْ تُفْلِحُونَ

Kutuba zuwa ga Allah gaba dayanku yaku muminai Zaku samu tsira da rabauta. (Suratul Nuur : 31)

Yasake cewa:

قُلْ يَٰعِبَادِىَ ٱلَّذِينَ أَسْرَفُواْ عَلَىٰٓ أَنفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُواْ مِن رَّحْمَةِ ٱللَّهِ ۚ إِنَّ ٱللَّهَ يَغْفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلْغَفُورُ ٱلرَّحِيمُ

Kace dasu yaku bayin Allah wadanda kukayi Laifukawa kawunan ku kada kuɗebe zaton tunanin Allah bazai iya yafe muku ba, lallai Allah yana gafarta zunubai gaba ɗaya kuma shi Allah mai yawan gafara ne dajinkai ga bayinsa. (Suratul Zumar 53)

Kalmar tuba tana da girma da dalililai masu zurfi, bakamar yanda wasu dayawa suke ɗauka ba, kawai kafurta da harshe kuma kaci gaba da aikata laifuka, ka lura ka kula dafadar Allah maɗaukakin sarki:

وَأَنِ ٱسْتَغْفِرُواْ رَبَّكُمْ ثُمَّ تُوبُوٓاْ إِلَيْهِ

Kunemi gafarar ubangijinku sannan kutuba zuwa gareshi (Suratul Hud : 3)

Haka ɗin dai zai yi ta bin matakan da malamai suka shimfiɗa a duk lokacin da yi zunubin kuma yake son samun ingantacciyar tuba, karɓaɓɓiya a wurin Ubangijinmu Tabaaraka Wa Ta’aala.

Matakan da za ki ɗauka domin neman gafarar Allaah da samun tubansa da yafewarsa a kan kowane irin zunubi su ne kamar haka:

Ki daina yin aikin saɓon a daidai lokacin da hankalinki ya dawo jikinki, kika fahimci kin saɓa wa Allaah Ubangijinki.

Ki yi ƙoƙari tuban naki ya zama saboda Allaah Maɗaukakin Sarki ne kaɗai, ba domin wani dalili daga cikin dalilai na dabam ba.

Ki ji a cikin zuciyarki da jikinki cewa, wannan abin da kika aikata mummunan aiki ne, wanda kuma zai iya haifar miki da mummunan sakamako a Duniya da Barzahu da Lahira, idan Allaah Ta’aala bai tausaya miki ya yafe miki ba!

Ki yi nadama da baƙin ciki a kan abin da ya auku na wannan mummunan sakacin da kika yi har wata gaɓa daga cikin gaɓoɓinki ta karkace ta faɗa cikin saɓon.

Ki faɗa wa Allaah Ubangijinki Masanin ciki da wajen al’amuranki cewa: ‘Ya Allaah! Na tuba kuma na komo gare ka. Don haka ka yafe mini saɓon nan da na tafka.’

Ki ɗaura niyyar cewa ba za ki sake komawa ga yin irin wannan sakacin ba, balle har a samu wata gaɓarki ta sake aikata laifi mai kama da wannan a iya tsawon rayuwarki.

Ki yi amfani da wani kyakkyawan aikin imani da kika taɓa aikatawa ko wani mummunan aikin sharri da kika nisance shi saboda Allaah kaɗai, ki yi tawassuli da hakan ga Allaah a wannan lokacin.

Watau, ki roƙi Allaah Taaala da wannan aikin.

Ki yi ƙoƙarin gyara abubuwan da kike iya gyarawa na ayyukan da sakacinki ya sa suka lalace, ko waɗanda kika ɓarnata ta dalilin wannan saɓon, idan suna iya gyaruwa.

Ki rabu da wuri, ko duk wanda ya zuga ki ko ya yaudare ki ko kuma ya taimaka miki har kika tafka wannan zunubin.

Ki yi ƙoƙarin kusanta ko haɗuwa da sababbin ƙawaye da sauran mutanen kirki, waɗanda za su iya taimaka miki su zuga ki ga ci gaba da aikata alhairan da za su iya zama gyara ko masu kankarewa ga abin da ya gabata na ɓarna.

Idan kuma laifin ya haɗa da haƙƙin waɗansu bayin Allaah ne, to a nan sai kin mayar musu da haƙƙoƙin nasu, ko kuma kin nemo amincewarsu da yafewarsu.

Lalata duk kayan da ake amfani da su wurin aikata laifin, kamar misali kwalaben giya ko ƙwayoyin daskarar da ƙwaƙwalwa ga masu shaye-shaye, ko kuma hotunan tsiraici ga masu kallon fima-fimai da sauran makamantansu.

Waɗannan su ne matakan da za ki riƙa ɗauka a duk lokacin da waɗannan maƙiyan suka sa kika zame kuma kika afka cikin aikata dukkan wani zunubi ko saɓo. Allaah Ta’aala nake roƙo ya tsare mu, ya taimake mu gaba ɗaya, kuma ya sa mu fi ƙarfin shaiɗanunmu da zukatanmu. Allaah ya shiryar da mu.

 WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments