Ko da So..... (Kashi na 9)

    In kin Karanta ki yi sharing please

    Yadda ta gaji jiya sabida yawon da suka sha, ya sa take ji tamkar kar ta tashi, sai dai kasancewar ta yi missing ɗin class ɗin BIO1202 da yawa ya sa ta daurewa ta tashi tsaf ta shirya cikin doguwar rigar ta Ja da aka mata adon ruwan gold ta yi mata kyau sosai kofin tea ɗin da ke hannunta ta ajiye lokacin da taga bakwai saura minti goma tasan in ba zuwa ta yi ta tashi yaya Usman ba tas za ta makara, Malam Musa ya je garin su wannan ya sa take mannewa yayan dan ya sauke ta kafin ya wuce faculty ɗin su inda yake lecturing.

    Ƙamar yadda ta yi tsammani bacci yake a hankali ta taɓa shi, "yaya ka tashi za mu makara fa, tunjiya na faɗa ma kai zanbi fa,”

    Ɗan muskutawa ya yi cikin muryar bacci ya ce " haba Hafsa ko maka za mu ai kya bari garin ya waye ai" ya faɗa tare da jan bargon sa.

    Takaici ne ya kama Hafsa " wane wayewar gari kuma, yanzu fa 7"

    A ɗan furgice ya ta shi " what! 7 shi ne baki tashen ba yau nayi tamar rufewa yara da yawa ƙofa, baki kyautamun ba" ya faɗa lokacin da ya turo kofar ɓan ɗakin sa, murmushi ta yi shidai yaya kwai mugunta bacin ma ba anfani yake da attendance in ba ya sa mutane duk su tsorata.

    Dining area ta koma ta haɗo masa breakfast ta kai masa har ya fito sama sama ya ci suka fito, kamar yadda suka za ta Momy bacci take wannan ya sa suka fice ba tare da yi mata sallama ba, dan in suka sake suka tashe ta sai tafi sati tana nuna kanta ciwo yake dan sun tashe ta.

     Tafe suke Usman na mitar yau yana shiga aji zai banko ƙofa ko minti biyar ɗin da yake ƙarawa bazai ƙara ba Hafsa na faman dariya ai yaya yau sedai ka yi haƙuri kafin 8:10 ɗin sun cika aji tsaki ya yi ya kunna Radio shirin ‘yanci da rayuwa ake wanda Aisha Bello Mahmud take gabatarwa har ya sa hannu zai canja Hafsa ta ce Please karka canja, inason program ɗin yadda suke hira da wanda ya taɓa zama a kurku akwai darussa, sam makarar da na yi ya sa bance ka kunna ba, ina son program ɗin bai ce komai ba ya ci gaba da tuƙin sa.

    Har ya wuce Hafsa ta ce "lah yaya dan Allah koma baya"

     "mai ne kuma,?", ya faɗa a ɗan fusace, murmushi ta yi "Ba shir da na baka labarin yana koya mana electricity da Mechanics na gani na san makaranta zashi" bai ce komai ba ya koma baya.

    Hafsa ce ta leƙa "Yah Ba shir dama a Hotoro kake?"

    Jin an kira sunan sa ya sa shi juyowa daga ƙoƙarin tarar adai daita sahun da yake "lah Hafsa"

    Murmushi ta yi "sch zaka?"

    "Eh" kawai ya ce

    "Tom" shigo mu tafi.

    Usman ne ya ce ki koma baya sai ya zauna gaba ba ta ce komai ba ta fito ya shiga ta koma baya.

    Ba shir ne ya dube Usman "ina kwana?"

    "Lafiya ƙalau kawai Usman ya ce"

    Inda Hafsa da Ba shir suka ci gaba da hira sama sama kusan dai duk na kan Physics ɗinne.

    Adai dai gadar old site aka sauke Ba shir ya sauka yana ta zuba godiya, juyowa Usman ya yi "Hajiya dawo gaba"

    "Kai yaya dan Allah yanzu lokacin da zan ɓata wurin dawowa gaban ya yi munje kabuga, na faɗa ma mutumin nan rufe aji yake malamin class B ne baya rufewa" bai ce komai ba kawai yaja motar sa fuuu, murmushi kawai ta yi tasan haushi ya ji dan ya tsani ta zauna a gaban nan ya ce shi ba driver ba bane.

    A harabar faculty of Agriculture ya sauke ta cikin sauri ta leƙa gaban motar, "thank you Yaya" ba ta jira cewar sa ba ta yi gaba cikin sauri, shi ma bai jira amsar ta ba ya juya yabar faculty ɗin zuwa FEES ba nisa tsallakawa kawai ya yi ya shiga.

    Da sauri gudu gudu ta taƙarasa yau ce last lecture ɗin mutumin dan ya ce da an dawo mid semester break shi test zai shike nan sai dai su haɗu a exam.

    Turus taja ta tsaya ganin wasu daga cikin ‘yan ajin su a tsai tsaye agogon da ke maƙale kyakkyawan ɗantsen hannunta ta kalla takwas da minti goma sam ba ta yi tsammanin ya zo ba dan takwas da kwata yake zuwa yau ya shammace su da yawa, kusan kamar minti goma duk ta gaji da tsaiwa, matsawa ta yi bakin taga cikin sa'a ta hangi Bilkisu kusa da taga cikin ƙasa da murya ta ce " Bilkisu kimin attendance" muryar malamin da ta ji ya ce "Bilkisu karki mata attendance" wannan ne ya sa ta barin gurin tana dafe ƙirji ya yin da ‘yan ajin suka sa dariya.

    Ƙasa Hafsa ta tafi cikin kujerun zaman ɗalibai ta samu guri ta zauna tana duba wayar lokaci lokaci tana kallon ɗaliban da ke kai kawo a wurin.

    Sai wurin goma saura sannan Malamin ya fita, class rep ne ya ce " sir attendance sheet ɗin" juyowa ya yi indai har akwai irin su Bilkisu a class ɗin nan ba ni amsar sheet ɗin nan masu yiwa ƙawayen su attendance, Hajiya Bilki sai ki faɗa mata ban ƙarɓa ba" kowa ya sa dariya sabida yadda ya faɗa kamar ya san Bilkisun.

    Har ta fara ƙoƙarin kiran Hafsan lokacin da ta sauko sai kuma ta yi nasarar ɗora idanun ta kan Hafsan murmushi ta yi ta ƙarasa gun nata " Haba Hafsa test ne fa damu anjima shi ne zaki zauna karanta novel anya kinma kanki adalci kuwa?"

    Zaro ido Hafsa ta yi "test kuma, yau she aka sanya,?"

    " Lallaima wai kina nufin da gaske baki san da test" ɗin Bio1201 ba?" Bilkisu ta faɗa lokacin da ta zauna gefen Hafsa.

    Walllahi ban sani ba laifin ki ne da baki faɗamin ba," ta faɗa tana ƙoƙarin zaro littafin da ta ke jotting ciki ta hau dubawa inda ita kuma Bilkisu ta ɗauko handout ɗin ta dan ba ta yadda da karatun abin da ta rubuta ba dauring lectures tafi son cover to cover.

    *****

    "Umma ina kwana?" Muktar ya faɗa lokacin da fito daga ɗakin sa yana tazar kai, "lafiya ƙalau kar dai ka cemun harka fito" Umma da take jefa ƙosai cikin kaskon mai ta tambaya.

    Agogon hannun sa ya kalla " eh Umma na fito sauri nake banson in fara makara tun ba aje ko ina ba" ya faɗa yana ƙoƙarin dai dai ta hular da ke kansa. Ajiyar zuciya Umman ta yi "eh to haka ne amma gaskiya ka bari in kwashe kosan nan ko a hanya ne ka ci, jibi yadda ka faɗa daga fara aikin nan na san kuma duk ƙin karin da kake ne"

    Juwairiyya da ta fito daga ɗan ƙaramin kitchen ɗin su ɗauke da botiki, "yaya ina kwana?" Lafiya ƙalau ya ce.

    "Nama gama kokon ko a jarka ne shi ma sai a zuba masa, yawwa zuba masa Inna ta faɗa lokacin da ta tsame kosam " in kin zuba masa ki zo ki ɗaura masa kosan"

    "Sallamu Alaikum, wai a bada ƙosai na Ɗari uku kokon ɗari" yaron da ya shigo ya faɗa, juwairiyya ta amsa ta hau zuba masa in da muktar ya ce shi ya fita, a zaure suka ci karo da Hajara ta shigo ɗauke da botikin markaɗe na miyar abincin rana da suke siyarwa ne.

    Ɗan kaucewa ta yi yaya ina kwana " lafiya kalau, da kin ɗora mata miyar ki tafi Makaranta kina ji na Juwairiyya ta kula da shi tun da ita yanma take"

    "Tom yaya adawo lafiya" ta faɗa tare da yin ciki.

    Allah ya sa ya ce ya wuce titi, takwas dai dai ta masa a bakin gate ɗin makaranta cikin hanzari ya wuce ajin da yake da shi.

    Har ya kusa office ɗin malamai maza ya ji muryar yarinyar na cewa "Uncle" juyowa ya yi ganin Kadija Mansur ya sa shi yin murmushi " a'a Kadija lafiya dai ko kar principal ya zo ya ganki waie during lesson" ya faɗa cikin harshen Turanci.

    Shafa fuskar ta ta yi tare da miƙo masa takarda dama Abban mu ne ya ce in baka number ɗin sa zakuyi magana kan yana son ka dinga mana extra lesson na physic karɓar takardar ya yi "ok tom" zan kira shi ya faɗa tare da yin gaba ita kuma ta koma aji.

    Har ya zauna ya fito da zummar samun principal da maganar sai dai office din a kulle hangar sa cikin office din school proprietor ya sa shi leƙawa da sallama ya gai dasu kafin ya ce da principal ɗin gurinsa ya zo.

    Karka damu shigo bayani. Yadda sukai da Khadia ya musu Alhaji Isma'il ya yi murmushi "Malam Muktar ke nan dan wannan ai ba sai ka tambaya ba, lokacin ka ne in kaga za ka musu, sai dai yanzu ma maganar da muke da principal ke nan ta lesson ɗin ‘yan SS3 ce"

    Takardar da ke hannun sa ya miƙawa Muktar, Muktar ya amsa yana murmushi dubawa ya yi kafin ya mayar masa, "shike nan in mukai wayar zan faɗa masa sai dai ko weekend ko Friday," murmushi Alhaji Isma'il ya yi ya yin da Muktar ya taso ya baro office ɗin.

    Rubutawa

    Aeshakhabir

    Fadimafayau

    Soyayya
    Credit: LuckyTD

    No comments:

    Post a Comment

    ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.

    HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.