Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 8)

Ana kiran sallar Azahar na farka daga barcin da ban san ya ɗaukeni ba, da ambaton Allah na buɗe idona gami da ɗora idona tar a fuskar Halima da ta zuba tagumi hannu biyu tana kallona wanda na san ba kallona take ba tun da har bata ji motsina ba, da Kuma maganar da na yi, tsabar tunani ta faɗa da na san Halima akwai zurfin ciki, da kuma nuna damuwarta ga al'amarin kowa musamman al'amarin abin da take so, ta yiyu ni ce sillar taguminta ko dai wani abu daban, motsin da na ƙarayi ya sa Halima a zabure ta kalle ni

"Sumayyah har kin tashi”

Murmushi na yi Halima ba dai tsoro ba abu kaɗan za ka yi ka firgitata, ita ko faɗama tsoro yake bata sai dai fa akwaita da fushi, ban bata amsa ba na dubeta

"Halima yaushe Kika zo ne?"

Kallonnata ta yi ta kuma canza magana

"Kin ga Sumayya ba batun zuwa na ba ki tashi ga abinci na kawo miki duk da na san ba muradinki ba ne shinkafa da miya ne, dan Allah karkice ba za ki ci ba, na san da ƙyar idan kinci abinci kika kwanta, Habiba kina wasa da cikinki ina jiye miki ulcer ta kamaki”

Ta ƙarasa zancen da alamun tsoro

Ban yi mamakin abincin da Halima ta kawanba da idan aka bibiyama shi ne dalilin zuwanta gidanmu da wuri haka gidannamu dan kuwa Halima macace mai kyautatawa duk wanda yake tare da ita, na rasa kulawar dangi amma na samu ta ƙawa, lallai Allah abin godiyane a kowanne hali bawansa ya shiga yakan kawo masa mafita, domin shi ne ya kawo min Halima a lokacin da na rasa kulawar dangina, ba ma ni kaɗai ya kawowa ba hatta 'yan uwana da iyayena duk ya kawo mana ita

Maganar Halima ta katseni

"Sumayyah dan Allah ki tashi kici abincinnan karya wuce, kular bata wani riƙe zafi”

Murmushi na yi na miƙe da cewa

"Bari na wanko hannuna da baki”

Daganan na miƙe na fice daga ɗakin da Mama na ci karo tsakar gida ta kalle ni

"Hala yanzu Kika tashi wato Haliman bata ta shekinba da na ce tana zuwa ta tasheki”

Murmushi na yi na ce

"Mama kema dai kin san Halima ba za ta iya tashina ba, yanzu ma abinci ta zo min dashi, ina tashi ta matsamin na zo naci” .

Mama ta girgiza kai ta kalle ni

"Sumayyah ban san yazan misalta ƙaunar da Halima ke miki ba da har muma ta shafemu, duk da Suma ba want ƙarfi garesu ba amma duk sanda ta samu saita tunkaroki, ta fahimci rayuwar da muke ciki fiye da danginmu, da su suka kasa fahimta, ban san da me za mu iya biyan Halima ba, sai dai kawai Allah ya biyata”

Na ɗaga kai na ce

"Kwarai kuwa Mama dan yanzuma ta yiyu ko abinci bata ci ba ta tawo kawomin, saboda ta lura da wuya na ci abinci na tafi makaranta da safe, na san zai wuya ba haka za ta ce ba”

Mama ta ce

"Sai kije kuci tare, karki shiga haƙƙinta da yawa, Halima akwai lura sosai, rayuwarta Mai burgewa ce”

Na ce

"Haka ne Mama”

Daganan na ƙarasa gefen banbum ruwanmu na ɗauki buta na wanki hannu muka da baki na koma ɗakin da sallamata, Halima ta amsamin na zauna kusa da ita da harta buɗe kular da ƙamshin miyar keta ta tashi kamar ansa kifi ciki, har zan fara ci, na dubi Haliman

"Kisa hannu muci Mana, inada tabbacin baki ci abinci ba kika taho kawomin"

Halima ta dube ni

"To fara ci ki ragemin, dan Allah karki sake magana kici abincinki kawai”

Bansake maganarba kamar yadda, Halima ta buƙata na fara cin daddaɗan girki, da tun da Halima ta buɗe na san zai yi daɗi saboda ƙamshinsa da tun kafin na fara ci na haɗiyi yawu, sai da na ci na ƙoshi na ragewa Halim ta wanko hannu ta fara cin abincin da a lokacin ƙannena 'yan makaranta sun dawo, Ahmad da Rumaisa da Sadiƙ da Khadija da suka shigo a tare, kamar sun haɗa baki, Mama na ji suna tambaya abinci, sai dai ban sake jin mai Maman ta ce musu ba na ji sun yi shiru da ɗai da ɗai suka riƙa shigowa ɗakinmu suna gaida Halima suna kwasar kayansu suna fita da Ahmad a kofar ɗaki ya tsaya suka gaisa ya yi gaba saboda shi ganin sa yake babba kayan sa ma Rumaisa ta ɗaukarmasa dan kayansa duk suna ɗakinmu kwana ne dai a zaure yake yi, da idan ana ruwa sai dai ya je shagon da wani makwabcinmu 'ya'yensa ke kwana ya raɓa ya kwanta, saboda yadda kwanon zauren gidannamu ke shata ta kamar me.

"Yanzu Sumayyah kin kyauta kinwa mutumin alkawari za ku haɗu yau amma ki cemin gidan Mama Atika zan rakaki, da na san da haka wallahi da tuni na yi tafiyata, wannan ai abin haushi ne, kamar wadda bata zuwa islamiyya ki ce za ki saɓa alkawari”

Na rausayar da kaina jin Halima ta Gama sababinta

"Dan Allah Halima karki ce komai a kaina kimin uzuri Mamace ta ce lallai sai naje Kena kin san ba san zuwa nake ba”

"Duk da haka gaskiya banji daɗi ba, da tun zuwana kin faɗamin inada tabbacin da tuni mun dawo, yanzu gashi uku harta gota, yaushe har muka je muka dawo"

Na ce

"Oh Halima ke nan, ke ɗinfa ba dai mita ba”

Hijabinta ta ɗauka ta miƙe tana cewa

"Idan kin gama zancenki saiki biyoni”

Tsaki naja mata na miƙe ni ma ina cewa

"Kiji rainin wayau irin naki waye mai zancen idan ba ke ba, kin isheni da mitarki”

Tana ƙoƙarin barin ɗakin ta ce

"Mita ta a kan gaskiya take”

Nayi murmushi jin zancen Halima wato ita dai a kan Malam Hamid za ta iya faɗa dani kaina, bayanta na bi ina saka hijabina da yaketa kyallin guga a kofar ɗaki na ci Karo da Halima muka ƙarasa ɗakin Mama ta ba mu kuɗin napep da jaddada mana mu gaida Mama Atika ta Kuma bimu da addu'a muna amsawa da Amin har muka bar cikin gidan da addu'ar fita gida a bakina

Bamu wani ɓata lokaci bakin titi ba muka samu napep na faɗamasa unguwar da za mu mukayi sa'a zaije Nnasarawar, daalima tun da muka fito gida har muka shiga napep ɗin bata furtamin komai ba tanajin haushina

Na dubeta nace

"Amini na yi laifi ne, tun da muka baro gida baki sakemin magana ba”

Tsaki tayi

"Dan Allah Sumayyah ki kyaleni da Aminin munafurcinki, gaba ɗaya yau haushi kin riga kin gama bani, bawan Allahn nan Hamid yana sonki amma ke ɗin kina nuna baki sonsa, kina nuna masa ko in kula, saboda ke fa yaƙi tafiya jiya”

Wani tsaki ni ma na yi

"To ni banison shi ke nan kike nufi ko ya ya”

Ta kalle ni

"Allah masani, ina zan sani, wannan sai zuciyarki. . "

Bata ƙarasa faɗar zancenta ba wayarta ta yi ƙara tasa hannu aljihun doguwar rigarta ta ɗauka tana kallon wayar kafin ta maida kallon ta gare ni tana miƙomin wayar

"ungo malam Hamid ne”

Na kalleta ni ma nii ta kalla

"Ki amsa mana kada ta katse, ki san mai za ki faɗa masa” ta ƙarasa zancen tana miƙomin wayar, haka na amsa da tunani da yawa a raina sallamar da ya yi na amsa ina ji sanda ya yi ajiyar zuciya kafin ya ci gaba

"Sumayyah ce ko?"

Na amsa da

"Eh ni ce ina yini”

"Lafiya Lau, da fatan kin shirya zuwa na yau ko dan harna fito gida” Jin maganarsa da ya faɗa ya sa ni yin shiru sai da ya sake magana

"Baki jina ne”

Na ɗan daure na ce

"A'a na ji amma kaya haƙuri, ina komawa gida Mama ta aikemu ni da Halima, kaya haƙuri”

Shiru ya yi a wayar ba tare da ya ba ni amsa ba sai bayan wasu sakanni

"Shike nan Sumayya na fahimta ba laifin ki ba ne, amma naso ganinki a yau, wani unguwa aka aikeku?"

Na ɗanyi jim kafin na ce

"Nasarawa GRA”

"Oh God unguwar da nake zaune bara na dawo yanzu, amma yi min kwatancen layin da gidan da zaku"

Shiru na yi ina zullumi, ni ɗin daba wata bace a gidan ina ni ina kwatancen gidan Mama Atika, ni ɗin ni kaɗai ba tarbar arziƙi nake samu ba daga gurin 'ya'yan gidan bare naje da saurayi, maganarsa da tamin amsa kuwwa a kunne ta dawo dani tunani

"Ko baki ji ne?"

Na daure na ce

"A'a na jika, kawai dai ba zan iya kwatancen gidan ba ne”

Ba tare da na ji mai zai faɗa ba wayar ta yi ƙara na sauketa a kunne na ina dubawa na ga ta ɗauke da yiyuwar cajin ya ƙare ke nan, na miƙawa Halima wayar

"Ta ɗauke rigwagwar wayarki”

Tsaki ta yi ta amsa

"Za ki barni da jin haushinki da nike ko Za ki ƙaramin da cewa wayata rigwagwa”

Na ɗan kunshe dariya ta na ce

"Tuba nake Amini”

Halima ta dube ni

"Sumayyah maganar gaskiya banso kika ki faɗawa Mama gaskiya ba za ki yi baƙo yau ba za ki gidan Mama Atika ba, dan gaskiya ni ban da bana so kiji babu daɗi a ranki ban san mai zai kaini karo na da yawa zuwa danginki ba, saboda kinfi kowa sanin halinsu, banga mene anfanin kayi zumun ci da wanda bai san muhimmancin zumun ci ba”

Na runtse ido ina tunanin wasu abubuwa da sukemin ciwo idan na tunosu na Kuma buɗe ido na kalli Halima

"Halima ba laifin su ba ne, su ka ɗai harda laifinmu fa muma talakawar munada kwaɗayi

Na tsinkayi muryar dieban adaidata sahun da muke ciki ya na cewa

"Yarinya kin yi tunani mai kyau halinmu ya ja mana, sai dai kuma duk abin da ka bawa ɗan uwanka ba ka faɗiba matsayinsa gareka ya fi komai daka mallaka, shi ɗan uwa kamar ƙashin baya ne, kana iya dawo da komai daka rasa amma ban da ɗan uwanka, dan ka kyautatama sa ko kullum zaginka yake ba ka faɗi, amma yarinya zumun cin ne kawai masu kuɗin ba su buƙatar yi damu, wanda duk wuya duk rintsi mu kuma karmu yankesa domin munsan muhimmancin sada shi mun kuma san hukunci yanke shi”

Na jinjina maganar mutumin da duk ta ratsa mu wanda daganin sa dattijo ne dan duk ya haifi kamarmu za mu iya kiransa Baba, Halima ta jinjina kai ta fara magana

"Amma Baba masu kuɗin ba su buƙatar zumun cin damu ne”

Baban ya ce

" 'Ya ta ke nan ni zan faɗamiki ba su san zumun ci damu ƙanina uwa ɗaya uba ɗaya mai kuɗine sosai Abuja yake da zama yana kasuwanci amma da ɗiyata ta faɗamasa zataje hutun waya ya kirani ya ce” Shi dai yanzu ba wani jin daɗi yake ba maleji yake amma wasu gani suke kamar wani Abu yake da shi amma duk an zuba ido Shi zai yi komai a dangi, hakanma bai isa ba har sai yara sun riƙa zuwa hutu kowa ɗaukarsa wani jin daɗi suke” "na ba ku labari sai da na ci ma sa mutunci saboda na san dani yake kira ya yi ta yi min rashin mutunci a fakaice dake shi wawane bai iya ba, kuma na ba ku labari ni da shi saina ƙirga abunda ya taɓa haɗa ni da shi, amma daga 'ya ta za ta hutu ya kira yana faɗamin maganar banza kamar yayannan nawa, kuma duk da hakan saida yarinyartawa ta tafi hutun dan ni bana so yarana su fahimci komai kuma ko da sun fahimta bana so ya zama su fahimta a guri na, bare ma zumun ci ba mune muka ce a yi ba Allah da manzansa suka ce ayi, kuma idan na yanketa na san makomata, shi fa zumun ci abu ne mai girma duk da yadda zumun cin ya lalace bana so a haɗu dani gurin lalatashi, idan na tuno yadda zumun ci ya lalace a wannan zamanin har mamaki nake ku duba da fa, da babu ko da abun Hawa yadda ake zumun ci ba tare da an yi tunanin wane zai kawomin nauyi ba, shi kuma mai zuwa ba yana tunanin mai za a basa ba idan zai taho, to amma yanzu fa da hanyar sada zumun cin ta yi sauƙi yanzune ba'asan sada shi”

Kai muke jinjinawa maganar mutumin tana ratsa ilahirin jikina duk da ban san Halima ya take ji ba amma nafi tunanin hakanne ita ma, haka ya ci gaba da Yi mana Nasiha mai shiga jiki yanayi yana jawo mana ayoyi da hadisai, wannan ya ƙara tabbatarmin mutumin mai ilimi ne musamman na addini kuma yana anfani da iliminsa wanda ƙasarmu irinsu take buƙata a yanzu, ba waɗanda boko ta ratsasu ba ilimin addini ba, haka na ci gaba da tunani akwaisu irinsu a ƙasarnan ashe amma ƙasar bata buƙatarsu shi ya sa ba wanda yasan dasu, duk da tarin ilimin Abbanmu amma na fahimci wanna yafisa saboda shi Abbanmu ya fi zurfafa ilimin boko inda yake da Masters na addininma yana da shi sosai amma dai wannan ya fisa amma saina dubi yadda rayuwarsu take tafiya kamar waɗanda ba su yi ilimi ba babu wani ci gaba sai dai godiyar Allah tun daganan na ƙara fahimci rayuwar bawa arziƙinsa da talaucinsa duk a hannun Allah suke, shi ne yake bawa wanda yaso ya kuma hana wanda yaso ba wai dan baya ƙaunarsa ba sai dan ya jarrabasa, A haka muka ƙarasa Nasarawa GRA da har kofar gidan Mama Atika ya kaimu, wanda ko da mu ka fito motar muka basa kuɗin napep bai ansa ba yadai ce

"Ku dai ku sada zumun ci karku gaji, ladanka kake buƙata gurin Allah, dan ɗan Adam indai danshi zaka yi abu to a ko da yaushe kana iya dainawa, dan shi mantuwa garesa”

Zancen Baban ya ƙara ratsani kuma na yi alƙawarin zan sada zumun ci ba tare da gajiyawa ba da yardar ubangiji, godiya muka masa muka ƙarasa kofar gate ɗin gidan Mama Atika muka buɗe kofar shigar muka same ta buɗe hakan ya sa muka danna kai cikin gidan da harabar motocinsu ke ciki a ƙalla guda uku, da ginin ya ka sance self contained ne mai kyau. 

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments