Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 7)

Da farin cikin da yaka sa ɓuya a gareni har ya bayyana ga fuskata da shi na isa gida ina kwaɗa sallama Mama da na ci Karo da ita tsakar gida tana zuba ruwa tukunya ta amsamin tana mai maida kallonta gareni

"Lafiya kuwa, Sumayyah irin wannan fara'a haka?"

Na ɗan turo baki nace

"Kai Mama kin manta yau muka gama exam ta ƙualifying"

Ta ce

"Yo ai harna manta yi haƙuri Sumayyah"

Murmushi na yi a raina ina ayyana mama ke nan ita ba ruwanta ko yaron goye idan bata masa dai-dai ba tana iya basa haƙuri tunanin da nake na katse na ce

"Mama ina Khalil, ko har yau ba’a taso su makarantar ba”

Mama da take ƙoƙarin ɗaukar tukunya ta ce

"Na aikesa ya siyomin fulawa, jeki ki ɗauki Humaira na barota ita kaɗai ɗaki”

"Yawwa Mama yau wainar fulawa za ayi ko?"nayi maganar ina fara tafiya

"A'a sai dai wainar ƙwai ƙarewar ta fulawa, yadda rayuwa ta yi tsada za ki ce wata waina tama fulawa za ayi to yarinya ɗan wake za ayi”

Na zunɓuri baki jin abin da Maman ke faɗa na ce

"Kai Mama daga tambaya”

Tsaki ta yi tare da cewa” Au tambaya ce ke nan, ki jini da yarinya 'yar rainin wayau, ni wuce ki ɗaukarmin 'yata karta tashi taji ba motsi, ki je daƙinku da ita, ki shirya ki ki kawan ita kizo ki yi kwaɓin ɗan waken"

Ba tare da na ce komai ba ina ƙunkunai na shiga ɗakin Maman tamu da ina ji Maman na cewa

"Oho dai yau yin ɗan wake babu fashi”

Saina iya cewa a rayuwata ba ni ƙaunar ɗan wake shi ya sa ko kusa bana ci idan ko na ci sai dai idan ina jin yunwa

Aisha na kinkima kawai na baro ɗakin kayan na cire na koma kitchen da na tarar dawowar Khalil ke nan daga siyo fulawar kwaɓin mama ce ta yi daganan ta anshi Humaira tabar kitchen din ba dan naso ba na jira tukunyar ta tafasa na fara sakin ɗan waken cikin minti talatin na kammala na taƙo plat da abuna na shiga ɗakin Mama ina ci

Mama ta dubi ɗan waken da nake ba za uwar loma

"Ke Sumayyah keda ba kya son ɗan wake ya za ki yi da wannan da kika zubo, khalil ya sa hannu kuci tare”

Na ce

"Mama yunwa na keji shi ya sa, da khalil ɗin zanci abinci ya yi taɓe taɓe da hannun nasa”

Mama ta ce

"Kya yi dai gulmarki kya gama, kuma Khalil ɗin bawan Allah mai ya taɓa”

Nace

"Kai Mama muma ai bayin Allahn ne, kawai dan yaron yaci sunan Abbanku shike nan aita gatantasa, mu Kuma kakanmu ne fa, both side”

Dariya Mama ta yi ta ce

"To ya ranki”

Nima na yi dariya ba tare da na bata amsa ba

Na kalli Khalil da yake ta kallona na ce masa

"Jeka ka wanko hannunka da ragowar klin ɗin da na yi wanke wanke da safe, saura kuma ka karar da klin ɗin"

Kamar jira yake na yi maganar ya fice da gudu na bisa da da kallo Allah sarki Khalil idan ban mantaba yau cikinmu ba wanda ya karya muka tafi makaranta yau dole ne ma muji yunwa, na san yanzunma da alama bashin fulawar aka ciyo sai abunda Abba ya samu yau idan ya dawo za a ba da kudin

Shiru ne ya ratsa tsakanina da Mama da lokacin har Khalil ya wanko hannunsa ya fara cin abincin

Mama ce ta yi ƙoƙarin katse shirun namu ta hanyar cewa

"Sumayyah kina addu'a kuwa a kan ƙualifying ɗinnan taku kin san komai ƙoƙarinka su irin waɗannan jarabawowin sai da addu'a, tun da kuka fara jarabawarnan bana iya rintsawa saina kaiwa Allah buƙatata a kan jarabawarnan da kukeyi, yau ko da kanada yaƙinin za a samu kuɗin biyama jarabawarnan kowa yana da burin yaga yaci, bare kuma ke da babu yaƙinin hakan idan baki ci ba sai dai ki haƙura da karatunnan dan kin san ko gona Abbanku baida ita tasa takansa”

Kai na ɗaga da hawaye suka wankemin fuska tun da mama ta fara maganar nan dan ni ma zullumina ke nan murmushi na yi ina share hawayena na ce

"Mama ina addu'a duk abin da zaifi zama alkhairi a rayuwata ya haɗa ni da samunsa”

Mama ta jinjina kai tare da cewa

"Haka ne Sumayyah kin yi tunani mai kyau, Allah ya ba ku sa'a ke da su Halima da sauran ƙawayenki dama duka musulmai”

Nayi murmushi nace

"Amin Mama”

Mama ke nan rayuwarta tana burgeni tasan ya kamata ita dai inada yaƙinin da Allah zai azurta mamanmu ba makawa za ta kyautatawa 'yan uwanta fiye da tunanin mai tunani sai dai ita haka tata jarabtar take, da inada yaƙinin suma masu kuɗin jarabtarsu ce Allah ya ba su kuɗin da a dalilinsu idan basuyi wasa ba sai su halakar dashi

"Anjima idan an taso su Rumaisa makaranta saiku shirya kuje gidan Mama Atika ku yinar mata, kun daɗe ba ku je ba” maganar da mama ta yi ta katse min tunani na na kalli Maman sororo jin kalmar da take faɗa

"Kike kallona ko ba kiji mai na ce ba ne” faɗin Mama

Na ɗan rausayar dakai na ce

"Naji Mama amma gaskiya bana son zuwa gidan Mama Atika, duk da bata da matsala amma 'ya'yanta ko gaishesu mukayi ba su amsawa kuma na faɗamiki irin abunda suke mana a banzace suke kallonmu gaskiya mama kiya haƙuri nidai ba zani ba”

Mama cikin fushi ta fara magana

"Sumayyah na gaji da kalmomin ɓatanci da kike jifan dangina, danni dangina ba irin dangin ubanku ba ne, da dai danginku kika ce suyi haka ina iya yarda, amma kowa yasan Mama Atika irin alkhairin da take mana duk da ba cikinmu ɗaya ba amma ƙannen Abbanku da suke ciki ɗaya ba wanda zai iya bugar ƙirji ya kawo muku ko da kwancen 'ya'yansu kusa, ina laifin Mama Atika wannan atamfar holland ta jikinki ba kwance Malika ɗiyarta ba ne, da wulakanci suke maku idan kunje ina za su ba ku kaya, dan haka saikinje ba zan zura ido aƙi zumun ci ba idan dangin Abbanku ba su sanku ni nawa suna sanku"

Baki na zunɓura na ce

"Mama ba za ki gane ba ne, amma 'ya'yan mama Atika idan muka je wulaƙanci suke ma. . . "

Mama data kawo hannu za ta bugemin baki na yi saurin rufe bakina da ƙunshe sauran maganata

"Idan kika ƙara yi min magana saina mareki sakarai kawai” faɗin Mama da na san a dalilin ita Bata zuwa gidan Mama Atikar sai dai ta turamu ta faɗi haka amma irin kallon banzar da ake mana da yada mana magana da akeyi idan muka je abin ba 'ƙaramin ƙonamin rai yake ba shi ya sa rabon da muje mun daɗe tun sanda muka je da kwancen kayan Aunty Abida ɗiyar Mama Atikar a jikina muna shiga gidan Aunty Abida da tana ganina cikin ƙawayenta ta fara cewa

"Mai zan gani haka Sumayyah a baki kaya ko wata ba su yi ba duk sun kwarkoɗe omo kike samu su ko, saida na cewa Mama dama karta baki su"

Tana gama faɗar haka ƙawayennata suka kalle ni suka sheƙe da dariya

Haka cikin kunyar tozarcin da suka yi min na wuce cikin na ratsasu ta falon zuwa ɓangaren Mama Atika da suka bini da dariya wata tana cewa da Aunty Abida

"Amma ince yarinyar daga ƙauye take ko?"

Ban dai tsaya saurara amsar da Aunty Abida za ta bayarba na ƙarasa shigewa ciki

Tun bayan faruwar hakan na ji bana sha'awar ƙara zuwa gidan saidai bana so na faɗawa Mama saboda na san ranta zai ɓaci gashi har hakan ya shafi zumun cin Mamar da Mama Atika gashi laifin bawai na Mama Atikar ba ne 'ya'yanta sukamin hakan, kuma tun bayan faruwar haka Mama bata ƙara cewa muje gidanba sai yau

Maganar Mama ta katse min tunanina tana cewa

"Da za ki ce ba za kije gidan Mama Atika ba, ai kya tafi dangin ubanki nanda kwana biyar kije ki yi zaman bauta, da kafin ku girma daidai da gwanjo babu wanda ya taɓa kawo muku, Mama Atika ba abin da bata yi muku harta da sabbin kaya dinko muku take, ai ina tunanin komai 'ya'yanta suka yi muku, ba za ki ce ba za kije gurin Mama Atika ba, saboda cancantar mahaifiyarsu gareku, da Kuma yadda nake da Mama Atika a matsayinta ƙanwar mahaifina”

Kalaman Mama sun yi tasiri gareni, Dan gaskiya Mama Atika batada laifi tanasan 'yan uwanta sosai laifin dama 'ya'yanta ne suma ba su fiye yi gabanta ba, nisawa na yi na ce

"Haka ne Mama kiya haƙuri zamuje, Halima ta ce za ta zo idan ta zo saimu tafi tare”

Murmushi Mama ta yi ta ɗora da cewa

"Yawwa Sumayyah ki ƙara haƙuri da yanayin da rayuwarmu ta zo mana da shi, ko bakomai na san Allah yana sanmu dan rayuwar talauci jarabta ce, Kuma a yanzu ne za mu gane masoyanmu, dan da wani abu garemu za ki ga yadda dangi za su riƙa tururuwar zuwa wajenmu, amma yanzu wa kike gani, sai ɗaiɗaiku musamman dangin Abbanku"

Wani abu na ji ya tsayamin maƙoshina jin Mama ta anbaci dangin Abbanmu dan tunowa da halayyarsu da na yi, Haƙiƙa zan iya cewa akwai banbanci mai girman gaske da muke gani a kowanne ɓangare daga dangin mahaifinmu, hatta Baban katsina duk sallah sai ya ɗinke duka 'ya'yan ƙannensa amma bandamu a ciki, wannan banbancin kaɗai idan na tuno yakan ƙara sawa na ji bana sha'awar zuwa Katsinan nan, domin ina zullumin rayuwar da zan tsinci kaina a can"

"Sumayyah mai kike tunani ne, inata magana”

Muryar Mama da na ji kamar daga sama ya sani dawowa daga duniyar tunanin da na faɗa, na kumayi saurin cewa

"Babu komai Mama”

Mama ta girrgiza Kai

"A'a Sumayyah ban yarda ba, sau biyu fa ina miki magana, hankalinki baya tare dani gaba ɗaya”

Ban san ƙaryar da zan yiwa Mama ba dan tabbas banji maganar da ta yi min ba, sai yanzu

Mama ta dube ni ta ɗora da cewa

"Sumayyah, ba za ki yi haƙuri da rayuwar talaucin da Allah ya ɗoramana ba ko, to wallahi wannan rayuwar ta talauci ita ce hanyar da ake fahimtar haƙurinka, amma kina nufin ke ba za ki yi ba ko, idan tunaninki zai ƙare a haka kina so ki ɗorawa kanki wani ciwo ko, Ni da nake mahaifiyarki na yi haƙuri amma ke baki so ki yi, duk fa halin da za mu shiga ubangijinmu yana sane damu kuma yana tare damu"

Murmushi na yi jin Mama ta yi shiru alamu sun nuna ta kawo ƙarshen zancenta, Mama macace mai sanin ya kamata, babban abunda nake ƙara jin daɗi idan na tuno na samu shi ne uwa ta gari, tunanina na tsaida na maida kallona ga Mama nace

"Mama sam ba tunanin talauci nake ba, saboda na san idan na ce shi zan yi ban yiwa kaina adalci ba, saboda mahalliccinmu da ya fi kowa sanmu ya ƙaddari zuwanmu duniya haka, domin ya jarrabcemu"

Mama ta ɗaga Kai tare da cewa

"Naji to, faɗamin tunanin mai kikeyi?"

Na durƙusar da kaina ƙasa da kwalla ta ciko idona nace

"Mama bana son zuwa Katsinan nan gaba ɗaya, na san ba rayuwar 'yanci zan yi ba, ban san wanna gurbi Baban Katsinan zai aje ni ba, idan naje can"

Mama ta ɗago kaina dake ƙasa tare da cewa

"Kuka kike Sumayyah, Kar ki yi kuka kamar yadda nake yi duk lokacin da na tuno za ki tafi bigeren da ba’a damu da ku ba, saboda yadda Allah ya ƙaddara rayuwarmu za ta ka sance, bigeren da ake kallona a matsayin mai ƙashin tsiya da na hana babanku arziƙi”

Murmushi na yi na ce

"Mama ba kuka na ke ba, yanzune ma maganarki za ta iya sani Kuma”

Ta ce

"Amma ga idonki da hawaye, shike nan Sumayyah Allah yana sane damu karki zub da hawayenki, da ba za suyi anfani ba gurin zubarsu, saboda komai daga Allah ne”

Na ce

"Shike nan Mama bari naje na huta ɗaki”

Mama ta kalle ni a lokacin harna miƙe

"Wannan ɗan waken fulawar fa nufinki Khalil ne zai iya cinyewa?"

Khalil ɗin na kalla da yake ta zuba lomar ɗan wakensa, da ni ko tun da muka fara magana da Mama na ji abinci ya fita raina shiko yana ta ci hankalinsa kwance, tausayi Khalil ya ba ni tunowa da na yi shi ma nan gaba zai girma matsalolin rayuwa su tarar masa kamar mu wanda godiyar Allah kaɗai take wadatarmu a kullum, duk da bana yiwa Khalil fatan ina fatan kafin ya girma komai ya wuce, cikin dauriya dai na cewa Mama

"Na ƙoshi”

Daganan na soma takawa ina barin ɗakin da guntun hawayena, ina shiga ɗakinmu na kwanta saman yagulallar katifarmu ƙirar ta 'yan boarding saidai ta 'yan boarding tafi tamu fasali dan tamu kamar tsumman tabarma take, kuka na rushe da shi ina tunanin rayuwar zumun ci irin na yau danginmu ba su rasa dukiyar da za su tallafi rayuwarmu ba, amma sun bar mu muna rayuwa irin wannan, hannu na kai sama cikin kuka ina cewa

"Ya Allah na san ba ka manta mu ba, ya Allah mun bar komai a hannunka, ba muda kowa sai kai, Allah ka tsare mana zukatanmu ka ƙara mana haƙuri bisa jarabtarmu da kayi, domin ka fi kowa sanmu, Allah ka ƙara mana haƙuri, domin na san wasu irin rayuwarmu suke so amma ba ka ba su ba”

Wannan addu'ar na kanji Mama ta na yi sau tari a duk sanda abubuwa suka ta'azzara gare mu, wanda indai zan shiga ɗakinta na Kan jiyo ta na yi da sai na gama saurarenta nakan shiga kona fasa shiga tun ina yarinya ƙarama na saba jin haka ga Mama, har na haddace su. 

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments