Ƙofar babban falon gidan Mama Atika muka buɗe da sallama dauke da bakinmu, babu kowa falon sai ƙarar Tv da tashar Africa TV ce ake kallo zama mukayi nida Halima a kujera mai 2seater muka fara kallon film episode na Iyalina da shi ake haskawa tashar Africa TV ɗin muka tarar, ba mu jima da zama ba Mama Atika ta shigo falon da sallama gami da fara'arta muka amsa mata ta zauna kujera mai kallon tamu
Gaisheta muka yi ta amsa murya
sake ta kalle ni
"Lale marhabin da manyan baƙi, Yanzu
Ina kitchen na ji kamar anyi sallama shi ne na leƙo ashema kune, amma kuka tsaya daganan
kamar gidan baƙonki ne Sumayyah"
Mama Atika ta ƙarasa
zancen fuskarta sake
Na kalli Mama Atikar na ce
"Yanzu nake shirin shigowa
sai gaki”
"Mama Atikar ta ce
"Ya mutanan gidan, kwanaki
Khalifa ya yi anguwar taku har na ce ya biya yaji lafiya kwana biyu, Auntyn
tasu bata turoku, to sai ya kirani waya ya ce dare ya yi ba zai samu biyawa ba,
ni ɗinma naso zuwa to
hidimar yau da kullum idan ba ka ya ki cewa saita hanaka zumun cin na”
Na jinjina kai na ce
"Haka ne Mama, muma
makaranta ta ɓoye mu
ba mu zuwa”
Ta ce
"Haka ne yanzu a jikinki
nawa ne”
Na ɗan
yi murmushi
"Wannan shekarar mukayi ƙualifying"
Mama Atika ta ce
"Allah ya taimaka ya ba da
sa'a”
Na amsa da
"Amin"
"wannan fa banganeta ba”
Tayi maganar tana nuna Halima
Na ce
"Ƙawata ce, sunanta Halima,
ai mun taɓa zuwa nan
da ita”
Mama Atika ta ce
"Aiko bangane taba, sai
yanzu. . . . "
Ba mu ƙarasa zancen ba, Aunty
Abida ta ƙaraso
cikin falon ta nufi gurin Mama tana magana a shagwaɓe, ko gaisuwar da muke mata bata saurara ba ta
fara magana
"Mami yunwa nake jii”
Tsaki Mama Atika ta yi ta kalleta
"Zoki daukeni ki cinye, tun
da baki san hanyar kitchen ba sakarai kawai, Kuma baki ga su Sumayyah ba ne, har
gaisheki suka yi”
"Yi hakuri Mami ban ji ba ne”
ta ƙarasa
zancen tana kallonmu
Mama Atika ta ce
"Kyaji ai”
"Sannunku"Aunty Abida
ta ce Mana
Muka amsa cikin haɗa baki "yawwa, Aunty
Abida ina yini”
Ta amsa da
"Lafiya lau"
Daga nan ta yi gaba a girme Aunty
Abida ba wani girmemin ta yi da yawa ba kawai matsayinm ƙanwar uwa gare ni nake
girmama ta, amma ban da haka mai zai ja min gaidata, kawai matsayin ta gareni
ya ja haka.
Maganar Mama Atika ta katse min
tunanina
"Ina Rumaisa ne, ba ku zo da
ita ba”
Na ce
"Eh amma Mama ta ce za su so
da ita da Ahmad da Khadija, ni ma saboda zan tafi Katsina na zo yau"
Mama Atika ta kalle ni
"Katsina Kuma gurin
wa?"
Na ce” gidan Abba Hashim (Baban
Katsina”
Mama Atika ta kalle ni ba tare da
ta ce komai ba ta ce
"Allah ya kaimu lafiya”
Na amsa da "Amin" na
san Mama Atika ta yi niyyar magana sai dai ganin Halima nafi tunanin ya sata
yin shiru domin tunaninta bai bata Halima tasan abubuwa da dama a rayuwata ba
Sai la'asar bayan mun yi sallah
muka baro gidan Mama Atika bayan mun ci abinci mun ƙoshi da duk da na ce mata
mun ci abinci sai da ta tilasta muka ƙara ci, Kaya masu yawa ta ba mu da kuɗi dan Mama Atika akwai san
kyautatawa 'yan uwanta yaranta ne dai ba su da kirki, zan iya cewa kaf dangin
Mamanmu babu mai san Mama kamar Mama Atika kodan ka sancewar kusan tare suka
taso kuma gidansu ɗaya
sai dai matsala guda Mama Atika bata zuwa gidanmu sosai bakomai na halin da
muke ciki ta sani ba, ita kuma Mama bata fiye kai ƙorafin yanayin rayuwarta
ba takan ce” Ubangiji ya kamata mu kaiwa kukanmu, shi ne yake son mai roƙarsa
amma ɗan adam bayansa
roƙo,
ta kance shi ma korafi kamar roƙo ne, ita bata fatan tayi” hakan ya sa bakomai
'yan uwan Mama suka sani game da rayuwar da take ciki ba sai inhar sunzo su
gani da idonsu su yi ta faɗa
bata faɗamusu, duk da
suma ɗin ba wani ƙarfi
garesu ba, Mama Atika ce dai dukta fi su hutawa, ita kuma ba wani zuwa dangi
take ba, wasu sunce mijin tane bai fiye bari ba
Yau ta kama Asabar ranar da Yaya
Samir zaizo tun asubar fari na gama shirina wanda inayi ina tunanin makomata
idan naje gidan Baban Katsina ya rayuwata za ta ka sance.
Mama ce ta kalle ni da na fara
hawaye jin Yaya Samir ya faɗawa
Abba ya tawo yana hanya, hakan ya sa Abba ya fita waje, da tun zamansa gidan
yau faɗa da Nasiha
yakemin kamar wadda za a yi wa aure ko na tafi ke nan ba zan dawo gidanmu ba
"Sumayyaha kukan mai kikeyi
kamar wata yarinya ya kamata ki samawa kanki lafiya, ko ni da aka tura boarding
tun daga JS1 ban taɓa
kuka haka ba, bare ke ɗin
da girmanki kuma cikin 'yan uwanki za ki tafi”
Maganar da Mama ta yi ta katse
min tunanin da nake da na san dauriya kawai ta yi amma dai kowa yasan ba
rayuwar 'yanci zan yi ba gwara a ce ma rayuwar boarding ɗin, kamar ba zan magana ba na dai daure nace
"Mama ina tsoron mai zaije
ya dawo bayan zuwana kina ganin dangi Abba babu mai sonmu"
Ta dafani
"Haba Sumayyah ki tuna Allah
a ko da yaushe yana tare dake kuma shi ne yake ƙaddara komai duk yadda akaso cutar dake
ki tuna Allah baya zalinci kuma zai miki sakayya a gurin Mai ƙoƙarin
zalintarki fatana dai dake duk wuya kada ki taɓa
tunanin zalintar wanda ya zalinceki ki sakawa mai zalunci da alkhairi a ko da yaushe,
sai kiga alkhairi da albarka ya lulluɓe
ki, zan riƙa
miki addu'a insha Allah babu abin da zai faru dake koma ya faru ki ƙaddara
a ranki ƙaddarar
ki ce”
Na share hawaye na, na ɗagama Mama kai tare da ce
wa
"Mama kinason ki kwantarmin
da hankali bayan ke naki ba kwance yake ba, kawai kina daurewa ne”
Mama ta riƙe hannuna
"Karki ce haka, Habiba
hankalina a kwance yake saboda inada Allah, kuma ma komai za su miki karki
manta kansu za su yiwa, kuma ba za su canza ki ba 'yar uwar su ce ke dole, idan
Kuma sun hana wasu su faɗa
ba bazssu hana wasu faɗi
ba, Kuma komai sukayi na munana miki karki manta haka Allah ya ƙaddaro
miki”
Kai na ɗagawa Mama, bankai ga cewa komai ba na ji
sallamar su Halima da Batul amsa musu mukayi da murmushi cike da fuskata Mama
suka gaisar daganan suka maida kallonsu gareni na hararesu
"Malama hararar mai kike mana”
faɗin Batul tana ita
ma hararata
Na ce” kunfi kowa sani, yanzu a
ce sai yanzu da ina gaf da tafiya za ku zomin sallama”
Tsaki Batul ta yi
"Dama kika samu muka
zo"
Na ce” ai na san ko baki zo ba Halima
za ta zo"
"Kin manta Kalima ce za ta zo
ba Halima ba, ai ni yanzu da Halima munfi tip da taya, tun da gashi za ki gudu
ki bar Halima” faɗin
Batul da ta bini da muguwar harara
Mama ta fara magana
"Kai Batul da Sumayyah
sababbu kun fara fa ke nan, ni ku tashi ku barmin ɗaki”
Halima da sai yanzu tasa baki ta
ce
"Wallahi Mama korasu"
Batul ta ce
"Ai harda ke”
Haka muka koma ɗakinmu muka zube saman
tabarma muka ci gaba da fira da yi min nasiha ko waccensu da idea ɗin da za ta kawomin kuma
kowacce shawararta abar dubawa ce bayan sun game min nasihar na kallesu
"Gaskiya na gode sosai, na
kuma ƙara
godewa Allah da ya haɗa
ni da ƙawaye
kamarku, ko ba’a faɗa
ba na san na san zan yi rashin masoya”
Murmushi Halima tayi
Batul ta goge hawayenta
"Sumayyah ban taɓa haɗuwa da ƙawar da nake jinta raina ba sama da ke, sai
kuma Halima, kin CANCANTA da mu yi miki komai ba ma nasiha ba”
Halima ta dafani
"Sumayyah kin cancanta da
komai garemu ke ƙawa ce”
Na goge hawayena da ni ma suka
tararmin
"NA CANCANTA!NA
CANCANTA!haka kowa ke faɗa
amman har yau na kasa fahimtar hakan"
Halima ta ce
"Dama ke ba za ki fahimta ba,
amma ke ƙawace,
ta kwarai, baki taɓa
yin wani abu na rashin dai-dai gabanmu ba saima idan mukayi mu ki nuna mana bai
kamata ba, mu shaidane a bayanki akwai uwa ta gari Mama ta miki tarbiyyar daba
wanda ba zai so ki da ita ba, muddin yasan kansa”
Nayi murmushi na ce
"Kuma bayanki akwai iyaye na
gari kamar Mama na na gode Allah da na ka sance na samu ƙawaye na gari waɗanda su kayi dacen uwaye na
gari”
Dariya mu kayi da dariyar tamu ta
yi dai-dai da sallamar Abba da kuma baƙon murya wadda na san ta ya Samir ce, da
mintina ba su fi biyu ba na ji Abba ya fito tsakar gidan yana cewa
"Ina Sumayyan ne?"
Na jiyo muryar Mama tana cewa
"Tana ɗakinsu Batul da Halima ne
suka so"
Sallamar Abban na ji ɗakinmu muka amsa masa su
Batul suka gaishesa ya amsa da fara'arta ya ƙara da cewa
"Wato an zo rakiya, Allah ya
sa ƙawartaku
karta mantaku idan taje Katsina?"
Na ce cikin muryar tausayi
"Kai Abba karkamin addu'ar
haka”
Yayi dariya ya ce
"Ba addu'a bace, kunsan mene”
Duk muka girgiza kai
Ya ce” haka Mama da Mama Atika
suka yi da suka je boarding suka dawo hutu"
Na ce” Mama” da ƙarfina
Abba ya ce
"Yi hakuri, tashi kuje ku
gaisa da Samir, karki haɗamin
tanbotse da Mamanku, ke ɗiyar
Mama”
Gaba ɗaya muka yj dariya muka miƙe
inasan Abbanmu saboda yadda yake mu'amala damu tamkar abokansa, danma baida
lokaci sosai a gida, amma hakan baisa mun raina sa ba, haka muka miƙe ba
wai dan naso gaisuwar ba da sallama muka shiga ɗakin
Mama da shi kaɗai muka
samu ɗakin yana zaune
saman Carpet ɗin
sallah ya ki shigiɗa
da jikin bango da gorar faro kusa da shi yana danna waya babu laifi Yaya Samir
yana da kyawunsa iya nasa Kuma ya iya kwalliya gaisuwar da na ji su Halima sun
fara masa ya dawo dani tunanin da na tafi ba tare da gama ba na yi saurin bin
gaisuwar da sukeyi muka ƙarasa tare cikin murmushi ya amsa mana
Yana kallan su Halima dani kaina
ya ce
"Habiba ban gane su ba”
Na ce
"Kawaye nane, tare muke Day
dasu"
Na nuna Halima na ce masa
"wannan Halima” na nuna Batul na ce” wannan Batul"
Yayi murmushi ya kalle ni
"Idan kika barni, ku fa 'yan
uku ne, ashe ƙawaye ne, Allah ya raya ku musha biki”
Nayi murmushi kawai a raina na
amsa da Amin
Kallonmu da Yaya Samir keyi ya
sani saurin miƙewa na ce
"Yaya bari muje”
Ya kalle ni ina tafiya fa zamuyi
yanzunnan"
Na ce” to ɗakinmu zamuje”
Muna shiga ɗakinmu na yi saurin cewa
"Kai Yaya Samir ba dai kallo
ba, kunga yadda yake kallonmu"
Batul ta kalle ni sheƙe ƙe
"Kin ji yarinya da rainin
wayau, ki ce dai Yana kallanki shi ya sa ma muka miƙe za mu ba ku guri ke
Kuma kika biyo mu"
Halima ta ce
"Faɗa mata dai, ashe shi ya sa taƙi Yaya
Hakim da Malam Hamid ashe zumun ci za a haɗa”
Batul tasa dariya ta ce
"Sosai kuwa, mu dai Allah ya
sa kar ana wanna tafiyar muji labarin ɗaurin
aure babu gayyata”
Tsaki na yi na ce
"Ku fa daɗina da ku yarinta”
Batul tasa dariya ta ce
Au ban da ke, ko da ke ba sabanba
anyi saurayi Mai mota”
Duk muka yi dariya, rayuwarmu da ƙawayena
tana burgeni idan muna hira ba za ka ba mu ƙananun shekaru ba
Haka cikin mintina da ba su fi goma da zuwan Yaya Samir ba muka fito tafiya gaba ɗaya gidanmu dasu Rumaisa suka ƙi zuwa Tahfiz saboda tafiyata da ƙawayena suka rakomu har wajen motar Yaya Samir muna kukan rabuwa da ba musan ranar sake haɗuwa ba danma ina da number ɗinsu a kaina sai dai babu batun yin wayar tun da ba ni da waya Mama Rumaisa, Ahmad, Khalil hawaye suke zubarwa da ni ma haka ne gurina ana saka kayana a boot Yaya Samir ya shiga motar ni ma na shiga gidan gaba ya ja motar da addu'o'in iyayena da 'yan uwana dasu Batul muka bar kofar gidanmu da ni dai tun da nake ban taɓa zuwa guri na kwana ba, fuskata na rufe cikin hijabi ina hawaye ganin muna ƙoƙari ficewa unguwarmu.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.