Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 6)

Yau muke zana jarabawar Physics da ta ka sance ƙarshen jarrabawar ƙualifying ɗin da muke hakan ya sa ta wani fannin muna farin ciki wani fannin akasin hakan muna zullumi domin a ɗayan biyu muke kodai mu samu komu faɗi dani sai na ce namafi kowa zullumi domin Wanda yake neman abincin yau da gobe ina zai nemo dubu 13 na biyan kudin neco ko wa'ec da indai ba ka ci ba saika biya, gwarama idan kana da English ko math ko da ba ka cinba daga baya gwamnati na biya ma idan na tuno hakan nakan ji damuwa sosai a raina amma duk da hakan nabarwa Allah komai kuma kullum cikin addu'a nake yi bawai ni kaɗaiba har Mama da Abba addu'arsu ke nan kullum gareni.

Fitowarmu daga exam ɗin ke nan na ci Karo da Malam Hamid a bakin class ɗin namu da kayansu na bautar ƙasa da tun bayan wayarmu bansake ganin saba dan banama fatan na gansa yau ɗinma ba hakan nasoba saboda nidai ba gwana bace a fannin so bare harna tattaro kalmomin da za su dace da amsar dazan basa, duk da zuciyata ta gama amincewa da Malam Hamid, saboda baida wata makusa tako wacce fuska, murmushi ya sakarmin tun kafin na matsa kusa da shi da ina haɗe ƙafa na ƙarasa dan kallon da yake jifana da shi gaba ɗaya ya fara ƙoƙarin rikitani, inda yaken na ƙarasa da sallamata amsa mun yi ya yi tare da sakarmin kallo Daya sakani jin kunyarsa hakan ya sa na yi ƙasa da kaina inamai gaishesa amsamin ya yi tare da faɗin

"Kunyata kikeji ke nan maza, ƙawayenki suzo su fassara”

Hakan da ya faɗa ya sa saurin ɗago da kai

"Malam Hamid fassara ta mene”

Ya ɗan lumshe ido ya buɗe ya ci gaba da kallona

"Na alamun muna soyayya, bayan kuma kin hana hakan"kallensa na yi ni ma ni ya kalla ɗaga kansa yayi” baki yarda ba ko?, Habiba ba zan ɓoye miki ba inasonki son da ba zai it's misalta miki kalarsa ba ko nuna miki shi saidai na kwatanta miki rashin amsarki gareni ya karyarmin da zuciya, ko dai inada wani aibu ne?"

Ni zancensa ma dariya ya ba ni yadda ya yi maganar tasa na dai daure na saki murmushi

"A'a Malam na amince, tun lokacin"

Ya kalle ni gami da hararata

"Shi ne kika dinga ba ni wahala ko, toma dame Kika amince”

Na dubesa ina ƙoƙarin basa amsa su Halima suka karaso inda muke tsaye sallama su kayi mana muka amsa musu cikin haɗa baki

"Malam Hamid ina yini, ashe kai ka ɓoyeta muna fitowa exam muka fara nemanta” suka haɗa baki gurin faɗin hakan

Murmushi ya yi ya ce

"Lafiya kalau, a'a ku tambaye ta dai inda ta tsaya ni ma yanzu muka tsaya”

Kallonsa na yi ba tare da na ce komai ba, ni ma ni ya kalla” wannan kallo haka na fara karya ko kike nufi?"

Halima ta dubesa "kai malam Hamid yaushe ta kalle ka kuma” ya ɗan rausayar dakai ya ce” karfa ki cemin baki ga kallon tuhumar da tayi min ba, ko kuma shigar mata za ki "

Halima ta yi murmushi "a'a fa, Kuma ko da ma na shigar mata ai ban yi aibu ba ka san ruhina nace”

Dariya yayi” kamar gaske”

Batul ta dubesa da sai yanzu ta saka baki” gasken gaske kuwa Malam ai ruhinmu ɗaya ne?"

Nidai tun da suka fara maganar da murmushi nake binsu ina jin su a raina sosai Halima da Batul musamman Haliman ma

Muryarsa ta katse tunanina” shike nan to dama yau nake saka ran komawa gida, saina barku da ƙawartaku tun da kun nuna min kunfi sonta akaina”

Kai na ɗago na kallesa bayan ya ƙarasa maganar

Halima ce ta yi saurin yin magana” malam Hamid yau fa?،, ka bari zuwa gobe mana, za ka yi daren hanya” Batul ita ma ta ce "sosai kuwa za ka iya kaiwa sallar isha'i ga ƙasar ba tsaro sosai”

Murmushi yayi” har fa na shirya komai”

Kallonsa na yi cikin marairaicewa nace” Dan Allah kayi haƙurin safiyar kaji?"wani mayataccen kallo ya bini da shi ya kuma sauke idanunsa saman nawa ba zan jure haɗa kwayar ido da shi ba hakan ya sa na yi saurin janye idanuna” akanme zan bari zuwa safiya bayan wadda nake zaune dan ita batasan ina wannan ba” ya yi maganar yana dubansu Batul alamun yana Jin haushina shi ya sa ko amsar tambayata bai ba ni ba, duk da na san Malam Hamid ya damu dani amma nidai na san ba danni yake zaune a Kano ba saboda bautar ƙasarsa yake yi kawai tsarin kalamaine irin na ɗa namiji da yadda matan suka iya suma sun iyasu maganar Halima na ji cikin tunanin da nake

"Waya faɗama bata damu dakai ba, ai saboda damuwarma malam na faɗama garinku za ta taho a satinnan"

Ina kallon yadda fuskarsa ta cika da annuri ya dubi Batul"haka ne Batul?"

Kai Batul ta ɗaga masa tare da cewa” eh haka ne za ta tafi gidan yayan Abbansu"

Halima ta kallesa tace” au da ba ka yarda da maganata ba, shike nan na daina ba ka labari game da Sumayyahn"

Daganan taja Batul ƙi Batul ta juyo ta kalle ni” muna jiranki” na bita da "to" da ba lallai ta ji ba saboda yadda Halima ta ke janta Halima ba dai iya fushi ba Kuma ita fushinta a kan abin da baikai ya kawo ba ma take abinta amma dai daka fahimci halin Haliman shike nan tanada daɗin zama

Suna barin gurin ya juyo da kallonsa gareni” Halima dama fushi gareta haka”

Dariya maganarsa ta ba ni na dai kunshe ta na yi murmushi nace” sosai kuwa, amma fa mara anfani tun da batasan a kan abin da za ta yi fishin ba”

Shima murmushi yayi” haka ne, da gaske Katsinan za ki tafi”

Na daure dan kawar da damuwar data riskeni da ya tunomin zancen tafiyata Katsinan nan da kwana biyar dan karya fahimci inada matsala da dangin nawa nace” Eh gidan yayan Abbanmu zani, acan yake da zama da aiki”

"Alhamdulillah, ashe ba zan yi nisan da nake tunanin zan yi da Sumayyana ba da tuno hakan yakan sani zullumi, wacce unguwar suke a katsinan?"ya karasa faɗin hakan yana kallona

Nace” a layout suke” a raina ina ganin zancen da Malam Hamid yake faɗa game da soyayyata kamar zancensa ne kawai domin dai duka kwanansa nawa da faɗamin yana son nawa, sai dai tunowa da ubangiji yakan iya komai a lokacin da yaso hakan ya sa na cirewa raina soyayyar malam Hamid ɗin ƙarya ce na yarda gaskiya ce

Kamar yasan tunanina na tsinkayi muryarsa Yana cewa

"Alhamdulillah, Sumayya na san za ki yi tunanin soyayyar da nake miki tamkar karyace, amma na daɗe da fara sonki, tun farkon kallona dake”

Murmushi na yi dan gaba ɗaya a tsoroce nake ina tsoron wani malamin ya zo wucewa yaji kalmar so tana fitowa a bakin Malam Hamid ɗin gareni

Kamar yasan tunanin da nake a karo na biyu ya ce” kin amince anjima zanzo gidanku, dan na ga a nan kamar a tsorace kike”

Kai na ɗaga alamun amincewa ba tare da na tsaya yi masa sallama ba nabar gurin, Inna tunanin ya zai yi ya zo gidanmu bayan bai sani ba tunowa da Halima da Batul da na yi suna waya na sallama zancen a raina

A tsakiyar makaranta na ci karo dasu sun tsaya da Malam Mukhtar malamin English ɗinmu, dan su Halima ba dai magana da malamiba da ni ma na bi bayansu, saboda abotarmu tasa kusan komai namu iri ɗaya nee, sai na ce a malamanmu kaɗanne ba su san sunanmu ba amma dai sani a fuska dai sun yi mana duk da ba dai a batun rashin ji ba a dalilin monitor data ka sance Batul yawanci a nan mukayi sanayya, Malam Mukhtar ɗin na gaisar daganan muka fice a makarantar muna firarmu

Halima ta ce "Batul kin san me yau gidansu Sumayyah zanje?"

Batul tace” yanzu, ko anjima, mai za kiyo?"

Halima ta yi 'yar dariya "zanje sanar da Mama soyayyar da Sumayyah take yi da Malam Hamid, Kin ga sai ta fara shiri da wuri”

Dariya Batul ta yi tace” haka ne kuwa Halima kin kawo magana mai girman gaske”

Tsaki na yi tare da cewa” Allah ya shiryi ɗan iskan mutum"

Batul ta yi saurin cewa” ni ko Halima”

Nace” Wanda ya tsargu, ban da iskanci ku da kuke soyayyar na taɓa cewa zanzo gida na sanar dasu Mamanku"

Dariya ƙasa ƙasa Halima ta yi tace” wato dai ni ce 'yar iskar, kema kuma guguwa, kuma ai ni kin san ba wanda bai san Aliyu a gidanmu ba ko yaron goye yasanshi”

Tsaki na yi” ba dole a sanshi ba an na ce saurayi ɗaya kamar mayya”

"Ai a nan darajar take idan Allah ya yi Aliyun ba mijinta ba ne, bayan rabuwarsu sai kiga ta samu mafiyinsa, amma tara samari ai baida daɗi”

Jinjina kai na yi” amma dai ai ba ka ce namiji ɗaya za ka kula kamar autan maza”

Halima ta buga tsaki” please Sumayyah ki ajiye kalamanki bawai dan ba za sumin tasiri ba idan na ji su ba, amma dai kawai ba za sumin tasiri ba dan na daɗe ina jinsu, amma ya kamata a ce zuwa yanzu kin fahimci waye Aliyu"

Jinjina kai na yi a raina ina tunanin maganar Halima.

Note:wasu za su ce ko sun taɓa ganin littafin continuation ne kawai anyi editing ne wani ɓangaren.

**** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604

Na Cancanta 

Post a Comment

0 Comments