Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 12)

Bayan wasu kwanaki ko na ce satuka, da zuwa lokacin sai na ce har na fara sabawa da halin mutanan cikin gidan Yaya Samir kam mutumin kirki ne shi ne abokin fira na idan yana falon idan bayanan zaman idan na ji zan takura sai na shige kitchen wajen Mai yi musu girki Baba Indo da tun farkon zuwa na take min wasa da dariya tana tsokanata da babbar jikarta kamata take take shaidamin, da matsalolin rayuwa ya sa take aikin a gidan amma ba wai zaman na mata da daɗi ba takan faɗa min su mutane ne kusan da ba ka taɓa iya musu ba su tausayin ta, su dai ta musu dai dai sukeso, abune kuma da ba zai yiyu ba, kai kanka ba ka cika goma ba bare kace za ayi ma dai dai ɗari bisa ɗari takan ba ni baki da lallashina idan suka ɓata min rai

Ina zaune falon duk da na takura hanyar ficewa na kesonyi amma kallo kallo ya riƙeni, falon ya yi shiru sai ƙarar Tv da hira ƙasa ƙasa na wasu daga cikin mutanan falon, wanda ni dai da ido nake bin Tv ina Kuma jin daɗin kallon da muke na film ɗin waris

"Yaya Abdulmalik ka san mene?"

Naji Fatima na faɗin hakan

"Yaya Abdulmalik ya bata amsa da

" sai kin faɗa”

Ta ci gaba da cewa

"Ka san me Yaya da zai yi wai makarantarmu sai saka, wannan Sumayyah, ka jifa”

Tsaki ya yi jin maganarta ya Kuma kalli gefena da na nuna masa kamar ban san suna yi ba

"Maine to shafuwarki da hakan Fatima ki raba kanki dai kin san halin Yaya Samir baya san irin gulmar nan, tun da ki ka ga har Abba bai isa da shi ba sai da ya kawota ke to Ina ruwanki”

Yaya Abdulmalik ne yake ta sababi duk da muryar ba da ƙarfi yake ba amma za ka gane sababi yake

Fatima ta ce

"Wallahi kawai dan yana nuna ya fi ƙarfin Abba ne shi ya sa ya kyalesa, yarinyar da suke talakawa ina suka cancanta da zama damu, kaima kanka shaida ne Abba ya ce duk wanda ya zauna da su tsiya cewa zai yi, kuma duk mamarsu ce gashi nan Abba Abdallah ko almajiri dake garari ya fisa kyan gani akanme zama da muguwar mace mai ƙashin tsiya. .

Duk da Ummi na zaune bai hana Fatima yin shiru daga cin zarafina ba, ko Kuma a ce ta kwaɓeta hawaye na ji sun soma biyo kuncina da duminsu ya tabbatarmin da sune, gaskiya na yarda talaka yana ganin garari 'yar uwata da nake tunanin za ta fi kowa sanin ciwona ita ce take faɗin hakan a kaina, ba ma akaina ba a gaban ido nama, lallai tabbas akwai wata ƙaddara a zamana zuciyata tuƙiƙi take amma banaji zan iya hassala komai, ban iya faɗa ba ko cacar baki hasalima rayuwata ni guda nake sai ko su Halima da rayuwarmu ta zo data idan na san ka fini bana shiga rayuwarka gudun irin hakan

Muryar abid na ji kamar daga sama yana cewa

"Haba Yaya Fatima ki bari mana kin ga kuka take, Allah sarki ita bata da laifi dama mu duka za mu zama kamarta”

Fatima ce ta ce

" Allah ya kyauta yaro ƙashin tsiya ta yi gado fa”

Abid ya yi tsaki ya ce

"Kece kika sanshi amma ni dai na san Yaya Sumayyah ta cancanta da zama da kowa kuma ta fiki kirki, ita bata neman rigima”

Fatima ta miƙe ta hayyako ta yi kan Abid za ta bigesa

Shigowar Abba ya dakatar da ita ya daka mata tsawa hakan ya sa ta koma ta zauna tana turo baki sannu da zuwan da ake masa bai amsa ba ya dubi Ummi

"Yanzu kina zaune za su yi mana faɗa ba za ki hanasu ba ko Sa'adatu?"

Ummi ta kallesa ta re da cewa

"Ai ka san halin Fatima baki ya sa mata tana magana ka kosan ba za ta kyalesa ba, laifinsa ne”

Abba ya kalli Abid

"Kai maiyasa kasa mata baki bana hanaku haka ba idan babba yana magana ba'asa baki”

Shiru ya yi Abid ɗin can ya ce

"Abba Yaya Sumayyah Yaya Fatima ke ta nema da rigima Kuma kowa ya yi shiru ya kyaleta, shi ne na yi magana, ni dai na san ba mu da banbanci da Yaya Sumayyah ko Abba”

Abban tsaki ya yi ba tare da ya ce komai ba ya yi gaba kila ko maganata baya so ayi masa ko?, bare yaji ba'asi maiya haɗa abun, jikina ba kwari na bar musu falon ba tare da na kallesu ba da alkawarin ban ƙara zama a falon gaba ɗaya har na bar gidan, ina tafiya na fara jiyo maganar Ummi

"Fatima abin da kikai gaskiya bai dace ba, karki ci gaba da biyewa Abbanku zai kaiku ya baro ku, ni dai na faɗamiki cin zarafi bai da wani alfanu"

Daga nan ban sake jiyo maganarsu ba na kuma fasa shiga daki na yi hanyar kitchen

Baba Indo na samu da sallama baki na na ƙarasa inda take

Kallona ta yi bayan amsa sallamarta tare Kuma da ajiye abin da take ta matso kusa da ni

"Sumayyah na san kina cikin damuwa ko?"

Hawayen da suka ciko idona suka fara zubowa na goge na kalli Baba Indo ba tare da ta ce min nabar zubar da hawaye ba na soma magana domin dai iya shaƙuwa na shaƙu da Baba mukan tattauna al'amura da dama na dangane da gidan harma ta ba ni shawarwari matar bata da surutu da yawan magana dattijuwa ce mai sanin ya kamata hakan ya sa tare muke hira a gidan Kamar muna da alaƙa da ita

"Baba babu mai sona a nan na zo gurin da ban cancanta da zama ba gurin da arziƙi shi ne ƙimarka Yaya Samir kaɗai ke sona a bayan shi sai Kuma ke duk da duk kulawata bata cancanta da ku ba amma wanda ya fi kusa dani bai riƙeni matsayin ɗiya ba Baba bana son ci gaba da zama anan, na fiso naje inda na cancanta da zama na zauna da su cikin so da ƙauna” daganan na rushe da kuka

Baba ta dafani” Sumayyah ba zan hanaki kuka ba danni ma na fara jiyo hayaniyar fatima, ban yi tsammanin Kuma hakanba na ɗauka komai wani abu da kake ji da shi ba za ka yiwa ɗan uwanka ba, Amma abin takaicin kowa yana jinta aka goyamata baya kuma, Amma ki sani baki cancanta da hakan ba kuma Allah zai miki sakayya ke ɗin yarinyar kirki ce mai ƙoƙarin aikata abu mai kyau, na daɗe ina kallo da nazarin 'yam mata kamarki kamarki amma ban sami ɗiya mai hankali nutsatsiya ba a bayan ke, kin ga ko kece kika cancanta da kowa ya soki ma”

Shiru na yi na kalli Baba tare da murmushi Mai ciwo jin ta kawo ƙarshen zancenta na ce.

"Baba ke nan haka mutane da dama suka sha faɗi a gareni amma har yau ban fahimci komai akai ba na kasa fahimtar ta ina Na cancanta, Baba rayuwa ta abar tausayi ce tun da ga yarinya har zuwa girma na sai kin zub da hawaye a lokacin da kikaga Abbana ki ka ga Abban Katsina kowa yaƙi Abbana yaƙi tallafa masa saboda Ummanmu sunce ko sun basa wani abun to a haka zai ƙare ba zai arziƙi ba sai dai idan sun rabu da Ummanmu, hakan ya sa kowa ya barsa cikin ƙunci, bayan soma girmanmu mun ɗauka ƙiyayyar da sukewa Umma a iya ita kaɗai za ta ƙare ashe ta shafemu muma kanmu, mun zama kamar abin ƙyama a cikin danginmu, kowa hantararmu yake, na rasa yaushe komai zai wuce”

Baba ta girgiza kanta ta ce

"Karki sare karki gaggawa komai zai wuce ya zama tarihi kuma za ku zamo abin alfahari fiye da duk wanda zai tunani za ku zama wasu abun insha Allah sai danginku sun fahimci ummanku mai ƙashin arziƙi ce bana tsiya ba, kuma ma ki cire wa kanki tunanin akwai wani Mai ƙashin tsiya kowa dai akwai iya arziƙinsa a rayuwa Kuma kowa zai tadda abunsa, komai daran da ɗewa”

Kai nake jinjinawa ina jin daɗin kalaman da Baba ke anfani dasu gurin lallashina.
 **** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments