"Zaman har na nawa ne da zaka yi maganar Islamiyya ko kuma zaman ta ke nan, nufinka ba za ta koma garinsu ba, Samir kana sane dai da cewa Abbanku ba san zaman yarinyar nan yake a gidan nan ba, karka ɗorawa kanka nauyi tun kafin ka aje iyalanka, kamin magana tun kwanaki kan Islamiyya kuma ban goyi baya kasata ba shi ne kawai magana”
Muryar Ummi nake jiyo wa daga
falo har zuwa ɗakina
da alamun faɗa da nafi
tsammanin saboda ɗaga
muryar da ta yi nake jiyowa amma ba na jiyo zancensu, ban san mai Yaya Samir ya
faɗa mata ba na ji ta ɗora da cewa
"To taji mana, ai ba zaginta
na yi ba, kawai gaskiya na faɗama
shi Abban naku ba ka fishi kusanci da ita ba amma ya yi biris da lamuranta ko
kulata ba ya yi a kan wanne dalili kai kuma za ka shiga so kake ka ƙarawa
kanka laifi a gurin sa kana gani turka turkar da aka yi kafin ya yarda yarinyar
nan ta zo haba Samir ka riƙa tunani mai kyau"
Kaina ne na ji ya saramin jin
maganganun Ummi da ma Abba baiso zuwana cikin ahalinsa ba ko da yake ba wai
abin musu ba ne dan yanayin da nake gani a gurinsa ya daɗe da fahimtar dani gaskiyar lamari, tunani
nake mai nene makomata a nan gaba a gidannan, zaman nawa kansa mene anfaninsa, tabbas
na fahimci akwai wata ƙaddarar da take sargafe dani da zamana a cikin wannan ahalin, ban
sake jin hayaniyar Ummi ba hakan ya sa ni jin daɗi
ya kuma ba ni da mar ci gaba da tunanina
Da yammacin ranar na fito a
kasalance nake tafiya harabar gidan na nufa dan yau bana sha'awar zaman ko da
falon a tsaye na hangosa ya jingina da bishiyar dake harabar gidan da gani
tunani yake dan shi bai hango ni ba hakan ya ba ni damar kallonsa sosai Yaya
Samir yanayinsa yana burgeni sam bai da kwaranniya daka gansa za ka fahimta
mutumin kirki ne sosai, gurin da yake na ƙaraso ina murmushi tare da sallama
sallamartawa nafi yaƙinin ta maidosa tunaninsa ya yi firgigit ya dawo daga
tunaninsa amsamin sallamar ya yi hakan ya sa ni gaishesa ya amsamin da murmushi
fuskarsa ya kuma yi gyaran murya ya fara magana
"Sumayya ban san ta ina zan
fara baki hakuri ba saboda na san zaman haƙuri kikeyi gidan nan daga zuwanki tabbas
inaso ki koma garinku a yanzu, sai dai kuma duka zaman da ba'afi sati biyu da
kwanaki ba na ce za ki tafi inaga bai kamata ba, dan Allah ki ƙara haƙuri”
Shiru na yi na mintina da sai da
kyar na iya lalubo amsar da zan basa dan gaskiya nafi buƙatar komawa gida da irin
wannan zaman da baida wani anfani sam, zama cikin mutanan da ba su san zumun ci
ba
"Bakomai Yaya Samir ni ma
ban gaji da zama ba”
Ya ce” Sumayyah ke nan na sani ba
wanda zaizo gidannan ya ce bai gaji da zama ba, muddin ba yana da abin hannunsa
ba, gashi batun islamiyyarki ya rushe, dan Allah kimin afuwa ba laifina ba ne”
Shiru na yi na maida kaina ƙasa
ina tuno maganganun ɗazu
da kunnuwana su ka ji na dai daure na ce” Bakomai Yaya Samir tun da ba wai zama
na ke nan ba idan na koma gida zan ci gaba da zuwa”
Ya ce” Haka ne Allah ya kaimu
lafiya, ya ƙara
miki hakuri da juriya”
Na amsa da
"Amin"
Na ci gaba da cewa ina mai duƙar da
kai
"Yaya Samir dan Allah ka
kiramin Halima mu gaisa”
Ya ce
"Halima wace ce haka Kuma” ?
Na ɗago
na kallesa na ce
"Ka manta Halima da Batul ƙawayena
daka tarar dasu gidanmu ranar da za mu taho nan"
Ya ce
"Oh sorry na tuna kina da
number ɗinsu ne ni ba
nida ita”
Nayi saurin ce wa” Eh Yaya Samir
akwai na haddaceta”
Ya ce” ok to"
Da ganan ya miƙomin
wayar yana mai ɗorawa
da ce wa
"Saka number ɗin ki kira”
Wayar na amsa na kira da bugun
farko Halima ta ɗaga
sallamata da taji ya sa na ji 'yar ƙarar da ta saki tare da ta na ce wa
"Nayi tsammanin kece, dama shi
ya sa na ɗaga ba wani ɓata lokaci”
Na yi murmushi na ce
"Shi ne ko amsa sallama
babu"
Naji muryar Haliman tana” ke rabu
dani wanni sallama zan amsa, kullum cikin tsammanin kiranki nake yi baki Kira
ni ba tunanina ko kin manta da ni”
Na girgiza kai kamar tana ganina
"Ya zan yi na manta dake
Halima idan na manta dake ban cancanta da zama ƙawar ƙwarai ba kamarke, Yanzu dai ya kike ya
Batul da Mama”
Haliman ta ce
" ƙawar kwarai ai ke ce
Sumayyah na yi rashinki daga ni har Batul, ni ma ina lafiya haka ma Batul da
Mama dan jiya i yanzu muna tare da Batul, gidanmu ta yini dan har gidanku na
barta za ta biya ta gaida Mama sannan ta wuce gida”
Naji daɗin jin yadda ƙawayen nawa ba su manta dani ba duk da
bana nan sun tuna da mahaifiyata na ce
"Naji daɗi sosai Halima Allah ya bar
zumun ci”
Ta ce "Amin yawwa baki
tanbayeni su Yaya Baffa da Yaya Hakeem ba, da Yaya Yazid kullum suna tambayarki
ke har Faisal ma”
Na ce” yi haƙuri
Halimatu, suna raina fa”
Haliman ta ce
"Ba wani nan, yanzu yaushe Za
ki dawo?"
Na ce” sai sanda Yaya Samir ya sa
rana”
Halima ta ce” Dan Allah karki daɗe, mun yi rashinki sosai
Sumayyah,, kuma ga karatu ma, kin san mun kusa komawa hutu"
Na ce "Haka ne Halima, ai ba
zan daɗe sosai ba duka
ma yau kwana na nawa a nan ɗin"
Haka dai muka ci gaba da fira da
Halima Yaya Samir kuma bai ce na basa wayar ba sai da muka gaji mukayi sallama
na basa wayar sai da ya amshi wayar ya kalle ni
"Da gaske kike Haliman ƙawarki
ce?"
Na ɗaga
kai na kallesa na Kuma maida kaina ƙasa dan bana jurar haɗa ido da mutane sosai ba ma
Yaya Samir kaɗai ba na
ce
"Eh ƙawata ce”
Ya ce” Kai amma abin ya birgeni
kuna ta hira kamar yayarki ko ƙanwarki, ban yi tsammanin akwai ƙawa
kamar wannan ba a yanzu"
Nayi murmushi na ce” Yaya Samir
Halima tana da alkhairi sosai kullum fata na na kwatanta abin da ta yi min
saboda na san ba zan iya biyanta ba”
Ya ce "haka ne insha Allah ni ma zan taya ki kwatanta hakan indai za ki tayani” haka muka ci gaba da fira da hirar duk ta Halima ce sai ko Batul da Yaya Samir ya buƙaci na sanar da shi alkhairin Haliman da Batul a gare ni.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.