Ticker

6/recent/ticker-posts

Na Cancanta (Kashi na 10)

Kuka ba zai zama maganin komai ba, ina roƙonki kar ki yi kuka, hakan idan ki kayi zan ji daɗi saɓanin hakan kuma zan ji babu daɗi saboda Sumayyah tunanina gida za ki je kowa naki ne a gidanmu, idan wani akasi ya faru ba yadda muka so ba kina dani, zan yi miki abunda ko wanne Yaya yake yiwa kanwarsa Sumayyah dan Allah kar ki yi kuka saboda hakan zai ɓatamin rai zan ji ya sagarmin da gwiwa” Maganar Yaya Samir ita ta ratsamin zuciya na ɗago na kallesa bayan yakai ƙarshen maganarsa

"Yaya Samir ba kuka nake ba” nayi Maganar ina maida kaina ƙasa

"Kina jin babu daɗi ko, rabuwa da iyaye Sumayyah saidai bisa dole kema ki ɗauki hakan tamkar dole, kuma ina fatan ki ɗauki nawa iyayen kamar naki, bana so ki yi maraici ta dalili na, ni ma zan yi addu'ar Allah ya sa ba za a samu matsala tare da nawa iyayenba, Sumayyah inasan zumun ci, kuma inason yinshi da ƙarfina da kuɗi na, kimin addu'a Allah ya sa kar nida iyayena muci amanar zumun cinmu"

Murmushi kawai na yi Jin Maganar da Yaya Samir yake yi, da maganarsa tasa hankalina ya kwanta sosai harna daina jin zullumi sosai haka dai na daure na ce

"Amma Yaya Samir zan kai yaushe kafin na dawo gida”

Murmushi ya yi da na gani kan fuskarsa ya ce

"Sai mun yi aure tukunna za ki zo ki ga gida” ya ƙarasa zancen yana hararata

Duk da na san wasa yake yi sai da gabana ya yanke ya faɗi jin batun aure danni a ƙaddarata bana fatan Allah ya ƙaddaramin auren zumun ci musamman yadda zumun cin ya ta ɓarɓare, Maganar Yaya Samir ta katse min tunanina

"Ya kikayi shiru Ƙanwata wasa nake miki, ba za ki daɗe ba za ki dawo, amma saikin saba da mu 'yan uwanki, dan tun farkon zuwana na fahimci kamar tsoronmu kike ji, wanda baikamata ɗan uwa ya ji tsoron ɗan uwansaba, shi ya sa na yi alƙawarin zan ɗaukoki ki zauna tare damu, ken samu har sai za ki yi aure ki dawo, idan ma a katsinan ne da nafi kowa jin daɗi” nidai shiru na yi dan gaba ɗaya bana fahimtar inda zancen Yaya Samir ya dosa barci ma na ji ina ji hakan ya sa na yi shiru na fara gyangyadi, tsayawar motar ya sani buɗe idona parking Yaya Samir ya yi gefen titi dai dai Rufaida fura and yoghurt na rijiyar za ki fita ya yi a motar ba tare da ya ce min komai ba, dan nafi tunanin yaji haushina ne, ya yi magana ban basa amsa ba, bai jima da fita ba ya dawo ya miƙomin ledar Rufaida yana cewa” ga wannan dan tafiya Katsina ba dai nisa ba na san za kiji yunwa kafin mukai”

Godiya na yi masa, shi ma na shi da ya siyo ya sa bayan mota muka ci gaba da tafiya da muke tafiyar ina tunanin makomata a nan gaba kaɗan, kaina na mayar ƙasa ina tuno komai na rayuwata yau ni ce wai zanje inda ba muda wata daraja a idanunsu, gidan mutumin da saboda Mamanmu ya hana Abbanmu aiki a haka har zan yi tunanin akwai wata soyayyar da zan tarar a gidan wan mahaifina, zan jure komai na yi alƙawari ba wai dan kowa ba sai dai Yaya Samir da a baya na ɗauka ni ɗin babu wani Wanda zai so rayuwa da mu, a cikin dangin Abba, amma sai ga Yaya Samir yana so na rayu har abada a tare da su, da a ce dangin Abba kamar Yaya Samir suke da na san babu abin da xamu rasa a rayuwarmu, duk da ba wanda yake azurtawa sai Allah amma dai na san da abubuwa da dama sun ragu

Sai wajen ƙarfe huɗu da mintina muka ƙarasa Katsina dan Yaya Samir ba wai gudu yake a mota ba, kuma gashi Katsinan ma akwai tafiya babu laifi Katsinan ta burgeni sosai duk da ba wai takai inda na baro ba amma dai tana da abun birgewa ita ma

A Kofar gate ɗin wani gida upstairs Yaya Samir ya fara horn ɗin motarsa wanda ko ba’a faɗamin ba gidan Abban Katsina ne, cikin mintina ƙalilan aka hangame gate din gidan, ya kunna hancin motarsa cikin gidan mai gadi yana ɗaga masa hannu da ce masa "sannu da zuwa” Gurin aje motoci ya ƙarasa ya parking ɗin motar ya fito, ni ma ba nida zaɓi da ya wuce na fito gabana yana tsananta faɗuwa da addu'ar da na fara ta rage haka har na tsaya na bi gidan da kallo tabbas gidan ya yi kyau sosai, dan za suyi kyau ɗaya da gidan Aunty Asma'u daga fara kallonsa da na yi, a raina na ci gaba da ayyana muna da masu kuɗi haka duk a 'yan uwan Abbanmu amma rayuwarmu take haka babu Wanda zai kalle ni ya ce akwai dangina masu kuɗi musamman idan ka ga gidan da na fito Maganar Yaya Samir ta ktsemin tunanina

"Kizo mu karasa ciki, Malam Musa zai shigo da kayanki cikin gida” ya ƙarasa zancen yana fara tafiya ni ma ba nida zaɓin da ya wuce bin bayansa da na yi Kofar falon muka ƙarasa knocking mukayi ta buɗe muka shiga da sallama babu kowa a falon sai ƙarar fanka da Ac kawai a falon tsayawa na yi kawai kaina a ƙasa dan bana so a lura da ƙauyancina shi ya sa na maida kaina ƙasa

"Ki zauna mana bari na kira Ummi na sani tana ciki” Maganar da Yaya Samir ya yi ya sani ɗago kaina da kafin na zauna Yaya Samir har ya fara tafiya hakan ya sani zama a kujera mai ɗaya ina ware idanuna a kan komai dake cikin falon komai ya yi dai dai da tsarin falon komai na falon brown ne harda labulaye, Maganar da na fara ji ya sani maida kallona ga inda nake jin maganar Yaya Samir ne sai Mamarsu da kallo ɗaya na yi mata na ganeta inda nake suka ƙaraso

"Maraba da Kanawa, ansha hanya”

Naji Maganar mamarsu Yaya Samir kamar daga sama da ban tsammaci hakan daga gare taba, murmushi na yi da a lokacin take ƙoƙarin zama kujerar dake kusa da tawa da shi ma Yaya Samir ya zauna kusa da mamarsu

"Ummi in yini” nayi maganar da alamun rashin sabo

"Lafiya ƙalau Sumayyah, ya kuka baro su mamarku"

Na ce” Alhamdulillah"

Daganan Ummin ta fara ƙoƙarin kunna Tv tana cewa

"Bari a kawo miki abinci ko ciki za ki shiga, ki huta, ki yi sallah"

Kafin na yi magana Yaya Samir ya rigani

"A'a Ummi gwara ta shiga ciki ta gaji sosai koni buƙatar hutun nake”

Ummin ta ce

"Shike nan taje ɗakin, Fatima ka nuna mata tun da saika wuce bangaranku"ni dai kallon Ummin kawai nake dan har yau na kasa fahimtar farin ciki take da zuwa na ko akasin hakan, Yaya Samir ne ya miƙe tare da cewa” taso na raka ki”

Ban musa ba na miƙe na bi bayansa jikina duk a sanyaye da tunani da yawa a raina kodai za su barwa Yaya Samir da yakawoni gidan ɗawainiyatane, da wannan tunanin nawa muka fara taka step har muka ƙarasa hayewa Yaya Samir kallona ya yi bayan mun gama ƙarasa hawan

"Sumayyah kiya hakuri da yadda kika ga Ummi ta yi Miki, ita ɗin haka take, sam bata fiye son mutane ba komai zance ne”

Murmushi na yi

"Yaya Samir to mene na faɗamin hakan"

Murmushin shi ma ya yi ya ce

"Sumayyah inaso Allah ya kawo sauyawarsu su so duk wanda zai raɓemu ko da ba muda alaƙar jini, dan su ɗin, bari dai kawai za ki tabbartawa kanki, yanzu ki shiga ki huta ki yi sallah ga ɗakin Fatiman nan" ya ƙarasa zancen yana nuna min dakin da hannu da ganan ya yi gaba ba tare da ya jira mai zance ba ba nida zaɓi da wuce shigewa ɗakin, komai na gidan masu kuɗi ya yi ɗakin kansa kamar na tawa amarya yake Kuma ɗakin budurwane kamar ni, dakin ya burgeni sosai, komai na dakin ya dace da muhallinsa, sallah na yi kawai ka sancewarta ƙasaru ma, daganan na kwanta saman carpet ba yunwa nake ji ba, dan nasha yogurt ɗin da Yaya Samir ya siyamin a mota, ban jima ba barci ya ɗaukeni da tunanin makomata, a irin wannan gidan da Yaya Samir ya fara sanar dani, wanda dama na sani ba su san talakawa, amma har yau naka sa fahimtar dalilin ɗaya ƙwaƙƙwara da ya Sanya Yaya Samir kawoni cikin rayuwar da bata dace dani ba” .

 **** **** 

Masu Neman Wannan Littafi na Iya Tuntuɓar:
Marubuciya: Halimatussa'adiyya Ibrahim Khalil
Lambar Waya: 08124915604
Na Cancanta

Post a Comment

0 Comments