Ticker

6/recent/ticker-posts

Mijinmu Baya Iya Saduwa Damu, Kuma Ya Ƙi Ya Sake Mu, Shin Za Mu Iya Gudu Mu Barshi?

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

As-Salaam Alaikum warahmatullahi Wabarkatuhu. Mijinmu, ba ya iya saduwa da mu, kuma ya ƙi yarda ya sake mu. To, ko za mu iya gudu mu bar shi, idan mun gama idda mu yi aure? Ko kuwa yaya za mu yi?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa Alaikumus Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.

Akwai wasu matsaloli da sukan bayyana ga ma’aurata a bayan ɗaura aure, wasu daga miji wasu kuma daga matar. Daga cikin waɗanda sukan bayyana daga miji akwai: Rashin ƙarfin gaba, ta yadda ba zai iya saduwa da matar ba.

An samu atharai tabbatattu da Al-Imaam Al-Albaaniy ya sahhaha a cikin Irwaa’ul Ghaleel: 6/324 daga Sahabbai irin su: Umar da Uthmaan da Ibn Mas’uud da Mugheerah Bn Shu’ubah (Radiyal Laahu Anhum) cewa:

الْعِنِّينُ يُؤَجَّلُ سَنَةً

Mai matsalar rashin ƙarfin gaba ana yi masa jinkiri na tsawon shekara guda.

Malamai suka ce:

1. Idan har ya iya saduwa a tsawon wannan lokacin ko da sau guda ne, to ba za a ɗauke shi mai matsalar da har matar za ta neman a warware auren ba. Amma idan ya kasa hakan a tsawon wannan lokacin to, a nan ne take da haƙƙin neman a warware.

2. A wannan zamanin ya halatta a yi amfani da maganganun ƙwararrun malamai masana ilimin likitanci domin a gano ko larurar mijin irin wacce take da magani ce don haka matar ba ta da ikon neman a raba su, ko kuwa wacce ba ta da magani ce don haka matar tana da ikon neman a warware auren.

Don haka, abin da ya wajaba ga waɗannan mata shi ne: Su fara ɗaukar matakan tabbatar da irin nau’in matsalar mijinsu tukun, har su san ko irin wacce take da magani ce, ko kuwa dai irin wacce ba ta da magani ce.

Idan ya tabbata cewa: Matsalarsa irin wacce ba ta da magani ce, to sai su ɗauki matakin neman a warware aurensu da shi a gaban alƙalin kotun musulunci mai adalci.

Idan kuma a inda su ke babu alƙalin musulunci, to sai su ɗauki matakan sanar da manyansu waɗanda suka ɗaura musu auren ko da ta waya ce, domin su san abin da ke wakana. Don haka su iyayen sai su ɗauki wannan matakin a gaban shari’a.

Amma ba daidai ba ne su kama hanya su gudu kawai, ba tare da mijinsu ya sake su. Domin ba zai yiwu su fara idda ba har sai bayan mutuwar aurensu. Kuma aure ba ya mutuwa har sai an kashe shi: ko dai daga miji ko kuma daga mata a gaban alƙali.

WALLAHU A'ALAM

Sheikh Muhammad Abdullaah Assalafiy

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments