Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Mazinaci Da Baya Sallah

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Meye hukuncin mazinaci wanda baya sallah sabida zina da yake yi wai Allah baya son sallarsa, tun da ya yi zina kuma yana Sallah juma'a?

𝐀𝐌𝐒𝐀

To farko dai ka sani sallah ita ce babban ƙinshin da ke riƙe da Addini domin ita ce abu mafi girma, kuma ita ce take riƙe da Addinin bayan kalmar shahada. Kuma rashin yin sallar na daga cikin manyan hanyoyin da ke sawa mutum ya afka a cikin manyan laifukan ire-iren su: shan giya, sata, da ita zinar. Dalilin faɗin Allah maɗaukakin sarki:

 ۖ إِنَّ الصَّلَاةَ تَنْهَىٰ عَنِ الْفَحْشَاءِ وَالْمُنْكَرِ ۗ وَلَذِكْرُ اللَّهِ أَكْبَرُ ۗ وَاللَّهُ يَعْلَمُ مَا تَصْنَعُونَ

Lalle salla tanã hanãwa daga alfãsha da abin ƙyãma, kuma lalle ambaton Allah ya fi girma, kuma Allah Yanã sane da abin da kuke aikatãwa. (Suratul Ankabut : 45)

Abu ba biyu ita zina bata fitar da mutum daga musunci, ballantana har ta hana a ƙarɓi sallarsa. Sai dai aikata zina babban laifi ne, kuma Alfasha ce kamar yadda Allah ya ambata a cikin littafinSa mai tsarki:

وَلَا تَقۡرَبُوا۟ ٱلزِّنَىٰۤۖ إِنَّهُۥ كَانَ فَـٰحِشَةࣰ وَسَاۤءَ سَبِیلࣰا ٢٣۝

Kuma kar ku kusanci zina. Haƙiƙa! Ita alfasha ce, kuma mummunar hanya ce. (Suratul Israai: 32)

Abu na uku duk wanda ya faɗa acikin irin wannan ya sani barin yin sallar ka iya fitar da shi daga musunci, kuma yin sallar juma'a kaɗai ba tare da yana yin sauran salloli ba, ba zai iya hana shi haɗu da azabar Allah ba, matuƙar bai tuba ba ya har ya mutu. Saboda da Allah maɗaukakin sarki ya iyawa waɗanda suke yin wasa da sallah alƙawarin azaba a cikin suratul Ma'un:

فَوَيْلٌ لِلْمُصَلِّينَ ٤۝ الَّذِينَ هُمْ عَنْ صَلَاتِهِمْ سَاهُونَ ٥۝

To, azaba yã tabbata ga masallata. Waɗanda suke masu shagala daga sallarsu. (Sūratul má'un : 4-5)

Kuma Aranar ƙiyama idan an tambayi ƴan wuta me ya shigar da su a cikin wutaza su ce ne rashin yin sallar. Kamar yadda Allah maɗaukakin sarki ya faɗa a cikin littafinSa mai tsarki:

مَا سَلَكَكُمْ فِي سَقَرَ ٢٤۝ قَالُوا لَمْ نَكُ مِنَ الْمُصَلِّينَ ٣٤۝

(Su ce musu) "Me ya shigar da ku a cikin wutar Saƙar?" Suka ce: "mun kasance ba ma yin sallah" (Suratul mudasirb:42-43)

Haka kuma ya tabbata a cikin hadisi, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallam ya ce: " Tsakanin mutum da shirka da kafirci shi ne barin Allah

Allah maɗaukakin sarki ya ce:

قُلْ يَا عِبَادِيَ الَّذِينَ أَسْرَفُوا عَلَىٰ أَنْفُسِهِمْ لَا تَقْنَطُوا مِنْ رَحْمَةِ اللَّهِ ۚ إِنَّ اللَّهَ يَغْفِرُ الذُّنُوبَ جَمِيعًا ۚ إِنَّهُ هُوَ الْغَفُورُ الرَّحِيمُ ٣٥۝

Ka ce: (Allah Ya ce): "Yã bãyĩNa waɗanda suka yi ɓarna a kan rãyukansu! Kada ku yanke ƙauna daga rahamar Allah. Lalle Allah na gãfarta zunubai gabã ɗaya. Lalle Shĩ, Shĩ ne Mai gãfara, Mai jin ƙai. " (Suratul zumar: 53)

Ibnu kasir rahimahullah ya ce: Wannan aya tana kirane ga dukkan masu saɓo harda kafirai su tuba su koma zuwa ga Allah, tana kuma ba da labarin Allah yana gafarta zunubai baki ɗaya ga duk wanda ya tuba yadawo daga aikata laifukan, komai irin yawansu da girmansu ko da sunkai yawan kumfar kogi, matukar anyi tuba na gaskiya Allah yana gafarta su.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments