Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Saurayi Ɗan Luwaɗi

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

 Assalamu Alaikum Wa Rahmatullah. Malam Barka Da Asuba. malam wata 'yar'uwammuce take tambayata tana da saurayi suna soyayya har an sa musu ranar aurensu amma yarinyar sai ta gano saurayin aikinsa neman maza yan'uwansa wato luwaɗi shi ne take tambaya

 menene hukuncinsa? Shin ya halatta ta rufa masa asiri suyi Aure?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa'alaikumus Salam warahmatullahi Wabarkatuh

Luwaɗi shi ne Namiji Ya Sadu da Namiji ɗan'uwansa. Luwaɗi da Madigo yanzu awannan zamanin sun zama kamar ruwan dare atsakanin Matasa maza da mata. Sun biye ma sha'awa irin ta Shaiɗanci wacce ta mamaye zukatansu. Hakika duk cikin nau'o'in zina da danginta, Luwaɗi shi ne mafi Muni, kuma mafi Qazanta. Kamar yadda Allah yake gaya mana acikin Alqur'ani:

وَلُوطًا إِذْ قَالَ لِقَوْمِهِ أَتَأْتُونَ الْفَاحِشَةَ مَا سَبَقَكُمْ بِهَا مِنْ أَحَدٍ مِنَ الْعَالَمِينَ ٠٨۝

Da Lũɗu, a lõkacin da ya ce wa mutãnensa: "meyasa kuke yin irin wannan alfashar? babu wani wanda ya rigaku aikatawa daga cikin talikai (halittu baki ɗaya)" Suratul A'araf : 80)

إِنَّكُمْ لَتَأْتُونَ الرِّجَالَ شَهْوَةً مِنْ دُونِ النِّسَاءِ ۚ بَلْ أَنْتُمْ قَوْمٌ مُسْرِفُونَ ١٨۝

"Lalle ne ku, haƙĩƙa kuna zuwa ma mazaje ta fannin sha'awarku maimakon mataye; ôa, kũ mutãne ne maɓarnata." (Suratul A'araf : 81)

Kuma saboda munin laifinsu shi ya sa Allah yayi musu azabar da bai taɓa yima kowa kafinsu ba. Allah ya aiko da Mala'iku suka ciccibe garin zuwa sama, suka watsa narkon azaba sannan suka Kifar dasu. Kamar yadda Allah yake cewa:

وَأَمْطَرْنَا عَلَيْهِمْ مَطَرًا ۖ فَسَاءَ مَطَرُ الْمُنْذَرِينَ ٨٥۝

Kuma mukayi ruwan (duwatsun azaba) akansu, lallai ruwan duwatsun azabar nan ta waɗanda akayi musu gargaɗi yayi muni kwarai. (suratun Namli ayah ta 58).

Saboda tsananin bala'in da yake cikin wannan aika-aikar, Manzon Allah ya ce: "MAFI GIRMAN ABIN DA NAKE TSORACE MA AL'UMMAH-TA, SHI NE IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT (luwaɗi)". (Tirmizy ya ruwaitoshi acikin Sunanu, hadisi na 1,457. Ibnu Maajah hadisi na 2,563).

Awani Hadisin kuma, Manzon Allah yana cewa : "TSINANNE NE DUK WANDA YAYI JIMA'I DA DABBA, KUMA TSINANNE NE DUK WANDA YA AIKATA IRIN AIKIN MUTANEN ANNABI LUUT (Luwaɗi)". (Imam Ahmad ne ya ruwaitoshi acikin Musnad, Hadisi na 1878).

Manzon Allah () Yana Cewa: An Karɓo Daga Ibn Abbas (ra) Ya ce: Annabi () Yana Cewa: “Duk Wanda Kuka Sameshi Yana Aikata Irin Aikin Mutanen Luut (Luwaɗi), To Ku Kashe Me Aikatawan da Wanda Ake Aikatawan Dashi”. {Tirmizi: 1456}

Saboda haka Ta sanya a yi masa nasiha ko ita ta yi masa, in har ya tuba, tuba ingantacce za su iya yin aure, saboda wanda ya tuba daga zunubi kamar wanda bai taɓa aikatawa ba ne. Ya tuba zuwa ga Allah, ya sani cewa rahamar Allah tana da yalwa, kuma ALLAH yana son bayinsa masu tuba.

 قُلۡ یَـٰعِبَادِیَ ٱلَّذِینَ أَسۡرَفُوا۟ عَلَىٰۤ أَنفُسِهِمۡ لَا تَقۡنَطُوا۟ مِن رَّحۡمَةِ ٱللَّهِۚ إِنَّ ٱللَّهَ یَغۡفِرُ ٱلذُّنُوبَ جَمِیعًاۚ إِنَّهُۥ هُوَ ٱلۡغَفُورُ ٱلرَّحِیمُ ٣٥۝

Ka ce: Ya ku bayina, waɗanda suka yi ɓarna ga kawunansu! Kar ku ɗebe tsammani daga samun Rahamar Allaah. Haƙiƙa! Allaah yana gafarar zunubi gaba-ɗaya. Haƙiƙa Shi! Shi ne Mai Yawan Gafara Mai Yawan Jin Ƙai.

(Surah Az-Zumar: 53)

In bai tuba ba ana iya fasa auran saboda mai wannan aikin fasiki ne. Annabi yana cewa: (Idan wanda kuka yarda da addininsa da dabi'unsa ya zo muku to ku aura masa) kamar yadda Tirmizi ya rawaito.

Mai neman maza dabi'unsa ba yardaddu ba ne, wannan ya sa za a iya hana shi aure. Sannan bai kamata a rufa masa asiri ba, musamman idan aka masa nasiha a asirce ya ki tuba saboda maɓarnaci ne.

In har za su yi aure ya kamata ayi gwajin jini saboda yiwuwar ya kwashi wata lalurar ta hanyar masha'ar da ya aikata a baya .

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam 

Post a Comment

0 Comments