Ticker

6/recent/ticker-posts

Makauniyar Shari'a [Kashi na 6]

Ya Allah ina godiya da bisa dukan ni'imominka a gareni. Yanda na fara Lafiya ka ba ni ikon gamawa Lafiya. Alkhairan da ke cikinsa ka ba ni ladansa, sharrin da ke ciki ka yafe min.

Allah ka dauka Alkalamin marubuta a duk in da suke

Gaisuwa ta musamman gareku na hannu dama ta.

  • Besty (Sarat Alkasum)
  • Maman Amatullah
  • Ummu shkura
  • Fadila Sani Bakori
  • Maman Sharifa
  • Mamashu
  • ABBA Yakubu
  • Dan Salma
  • Da Autan Jarumai.

Waɗanda ban samu damar kiran sunansu ba, duk ina mika sakon gaisuwata a gare ku.

Yayyena abun Alfaharina

  • Hadiza
  • Hussaina
  • Hassana
  • Maryam

Gaisuwa ta mussaman gareki

Anty Zulai, mutan Kano, surukar Auta na.

Jarumai Writers Association, marubuta masu aiki da Jarumta wajen Fadakar da Al'umma

MAKAUNIYAR SHARI'A

MAKAUNIYAR SHARI'A

IKILIMA ADAM (Kyauta daga Allah)

09069080725 ko +22953726162 (Whatsapp kaɗai ban da kira)

Marubuciyar da ta nishaɗantar da ku a littattafanta kamar haka:

  1. Kai ka ja wa kanka
  2. Kanwata
  3. RAI DAYA (Jan Za ki)
  4. RUDANI (mai tafiya daukan rai)

Da sauran su.

Yanzu ga ni ɗauke da sabon littafina mai suna MAKAUNIYAR SHARI'A

Littafin nan, na kuɗi ne. Da zaran free page ya kare za ki daina ganin sa. Hanzarta ki biya naki kada a yi babu ke.

Kibiya dari biyar kacal domin samun shiga group na musamman.

Domin Karin bayani a tuntuɓe ni ta wannan lambar 09069080725 ko + 22953726162.

Siyen nagari mai da kuɗi gida.

SHAFI NA ASHIRIN DA DAYA

Cikin gigita da fitar hayyaci ta fara ihuuu tana zabga salati, hannayenta na rawa kamar ana kadata da ganga, wani irin kyaikya yin azaba ta fara ji dukan sassan jikinta, cikin azaba take kallon Mamy da ta tashi zaune tana salati, Fauziyya bakinta na rawa ta ce.

" Mamy wayyo azaba zan mutu, Mamy ki agazan ". Waiwaya ta yi wajen Firdaus da su kayi caa akanta suna zabga salati ganin yanda jikinta nan da nan ya fara canza halitta, hatta fuskarta wasu kuraje kamar marurai suka cikasu har wani jini jini suke yi. Safiyya ban da" Innalilahi" ba abunda take maimaitawa, kana cikin rawar murya da kadawar harshe ta ce.

" Wallahi Tallahi idan na amince da cutar Fauziyya shegiya nake, haba wannan abun da take sai ka ce sammu aka mata, wallahi idan na yarda ba Mamy ta haifan sai na ci kutumar bura uban duk wanda yake son gigita min yar uwata ". Ta karashe zancen agigice hannunta na kan Fauziyya da ke ihunn neman agaji. Firdaus gabakidaya kanta ya kulle ta rasa wannan wani irin iftila'i ne suke fuskanta daga wannan sai wannan, fuskar babu digon rahma ta kai hannunnta kan Fauziyya da ke kururuwa, ganin Mamy na hawaye bibbiyu daga zaune, ba karamin shiga tashin hankali suka kara yi, a kidime Firdaus ta dau waya domin kiran Jibrin.

Bangaren Jibrin yana zaune a office dinsa shida abokan sai hirar Shari'a da akayi a kotu suke, cikin yakini yake jaddada in sha Allah sai ya taimaki Mamy, dan zaluncin ya yi yawa, karar wayarsa ce tasa shi ɗan murmusa ganin kiran Firdaus ya san Fauziyya ce ke son magana dashi hakan ya sa ya amsa kiran fuskarsa ɗauke da annuri, soma zazzare idanu ya yi jin kururuwar Fauziyya ta cikin waya yana jin muryan Yasmin cikin kuka tana fadin " anti Fauzy kiyi hakuri, wlh ba mu san maganin da za mu baki ba ki samu sassauci ba ".

 Zumbur Jibrin ya mike tsaye yana zagba salati, kasa tsayawa ya yi ya saurari maganar da Firdaus take masa, abokansa ne suka yi caa akansa sai tambaya suke "lafiya kuwa"? be ba su amsa ba illah cigaba da zagba salati, zufa na keto masa a fuska, bakinsa na rawa dakyar ya iya furta " Fauzy na jama'a ku taimakeni dan Allah karta mutu, wlh zan mutu inna rasa Fauzy". Ya karashe zancen a dimauce.

Abokansa duk sun gigice su kansu ba su san me yake faruwa ba, amma sun tabbatar ba ƙaramin Matsala ba ne, gani suka kayi ya saka wayoyinsa a aljihun wandonsa, ji yake kamar sam baya sauri hakan ya sa be tsaya ko sauraren abokansa ba, ya ja mashin dinsa aguje yabar office din ko tsayawa rufewa beyi ba. Abokansa kam suna ta sakawa da kwance daga hakan suka fara fatan Allah yakawo sauki.

Cen Bangaren Basma duk abin da yake faruwa suna kallo ita da Bokan nata, ba karamin dadi ne ya lullubeta ba, cikin shauki ta ce " Boka wannan Yarinyar anya cutar nan bazeyi ajalinta ba?".

 Murmushi keta Boka ya yi tare da fadin " ko dai kina son a kasheta ne? ". ya karashe zancen cikin son jin amsa.

 Guntun murmushi ta yi tana taunan cingam da ta sanya a baki, tare da fadin.

 "Ni in har zata mutu zan fi kowa farin ciki, na tsani yarinyar nan wlh, saboda tana kama da munafukar uwar mijina, ni in har zeyu a fara kasheta wlh". ta karashe zancen cikin tsanani bukatuwa.

 Boka dan jim ya yi alamun tunani kafin ya kara kai dubansa akanta, ɗauke idanunsa akanta ya yi yana mai ci-gaba da kallon kwaryan da ke gabansa, kana ya kara kallonta a karo na biyu, cikinsassaita nutsuwa ya ce.

 " Ba zeyu mu kasheta ba, saboda Uban Mijinta gangarumin malami ne, yana gani kamar hanji, in har ze san kasheta akayi to tabbas ze dawo da aikinmu akaina ko akanki ko a kan yayanki ". ya karshe zancen cikin tabbaci.

 Ya kara da fadin " Zaman kotu da za'a koma baze masu kyau ba, hatta alkalin mun fara aiki akansa, ita kanta Hadiza Ibrahim za mu sanya mata cutar mantuwa, kwata kwata zata manta da wannan case din, ko binciken ba zata samu damar yi ba, bare har ta tuna zuwa kotun ". Ya idasa zancen yana bushewa da dariya mai tsoratarwa.

Basma kwalalo idanu ta yi a waje tana mai rike bakinta, murya na rawa ta ce " A'a in har sai abun ya dawo kanmu a kyaleta da ranta a iya hakan ma ai gwamma mutuwarta, kokan Surukin nata ya gane meke damunta ai tasha jiki, gaskiya Barister Hadiza zata gane kurenta shegiya mai farar kafa, malam zan tafi kar yaga na dade ban dawo ba ". tana kai ayar zancen nata ta mike cikin dan saurinta.

 

Jibrin na isa ƙoƙarin shiga daga cikin Gidan yake ya ci karo da Alhaji Isah Sharifai yana ƙoƙarin shiga motarsa a harabar Gidan, kallon kallo sukewa juna, kana Jibrin ya yi karfin halin fadin " Ina wuni " be damu da jiran amsa daga bakinsa ba, in da sabo har ya saba.

Alhaji Isah kauda kai gefe ya yi kamar be ji gaisuwar ba, hanzarta shiga motarsa ya yi, ƙoƙarin tada motar yake ya ji sautin ihuu Fauziyya ya karade kunnennsa wanda ya sa cak ya tsaya be tada motar ba, a kidime ya furta "Fauziyyata". kana ya saka dukan hannayensa kan sitiyarin motar yana sauraren kururuwan da ke cika dodon kunnensa, nan da nan ya shiga tariyo shekarun baya duk sanda beda lafiya Fauziyya ce take dawainiya da shi bata iya barci inhar yana cikin tsananin rashin lafiya, ita ce mai zuwa yin wankau dan ta samo kudin da za'a sai masa magani ko zuwa asibiti, nan da nan ya fara tariyo lokacin haihuwarta da yanda ya haifeta babu kuɗi ko ragon suna be yanka mata saida ta shekara bakwai, da wayonta ta ci naman sunan haihuwarta. " innalilahi wa'inna ilairajun' ya shiga maimaitawa jin cikin kururuwar da fauzy ke yi tana fadin.

" Ya Allah !! Ka taimakeni ya Allah !! Ya Allah ka shiga lamarina ya Allah !! ".

 Muryan Jibrin ya ji yana Faɗin " Fauzy nine Jibrin dinki ki tsaya ki mun bayani mana, gayamin ina ke miki ciwo ya Fauziyyata ".

 Yanda yake jiyo muryan Jibrin cikin fitar hayyaci ya sa shi bude motarsa ya fito zumbur, hanzarta rufe motarsa ya yi ya kama hanyar da ze sada shi da sashin su Mamy, dai-dai lokaci Motar Basma ya kunno kai Gidan, me Gadi na wangale mata babban get babu bata lokaci ta shigo harabar gidan, cikin tashin hankali take kallon Isah ya bi sashin Mamy, ko tsayawa daidaita parking din motarta ba ta yi ba ta bi sahunsa a guje sai kiran sunansa take tana fadin.

" Isah!! " amma ina sam be san tana yi ba, hankalinta a tashe ta fara gudu gudu sauri sauri har ta kusa cimma masa, cikin rawar murya ta ce.

" Is. . a. . . h ". ta karashe cikin daga murya, sautin muryanta har cikin dakin Mamy, daga Mamy har yayanta da surukinta kowannensu mamaki ne ya cika su jin muryan Basma a sashin su.

 

Isah kuwa, cak ya tsaya yana kallonta tana karasowa hannunsa na kan handle Kofar, tana karasowa bakin ta na rawa ta ce. . . . . . . . . .

Ayi hkr dakyar nayi editin banjin dadi ina barar addu'a.

Taku har kullum (kyauta daga Allah)

[10/23, 5:37 PM] Kyauta Daga Allah: Utilise ce lien pour intégrer mon groupe WhatsApp : https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 NA

 IKILIMA ADAM

 (Kyauta daga Allah)

 09069080725

 Jarumai writ association

 SHAFI NA ASHIRIN DA BIYU

 Saura page uku in gama free page, wa'yanda ba su payment ba ku hanzarta kada a yi babu ku.

Tana karasowa bakinta na rawa ta ce.

 " Kayi batar hanya ne?".

 Hada rai ya yi cikin hanzari ya ce " kamarya  ba suke nan? ".

 Wani irin tsorone ya shige Basma lokaci daya, cikin aro jarumta ta ce.

 " kar ka je dakin nan yanzu haka wani sabon makirci ne ake shirya maka" ta karashe zancen tana kallon reaction dinsa.

 Kallonta yake kamar me nazartan wasu abubuwan, kana ya sauke nauyayyan ajiyar zuciya mai zafi, karamin macijin tun daga nesa yake tahowa cikinsauri sauri gudu gudu, kamar walkiya ya shige cikin babban yatsarsa na kafarsa na dama, wanda nan take Alhaji Isah ya dafe kansa, yanda macijin ke bin sansan jikinsa haka yake jin yanayinsa na sauyawa, saida macijin ya zo kwanyar kansa ya kara yabi ta hancinsa, kana ya samu mazauni a kan harshensa, cikin tafasar zuciya Isah Sharifai ke kallon Basma da duk ta tsorace da lamarinsa.

Jin ya kamo hannunta ya sa ta kallonsa kamar wata tabbabiya sake da baki.

 " Alhaji daman nazo in hanaka fadawa ga ha. . . . . ".

 " Shiiihhh " Alhaji Isah ya mata tare da hana ta karasa abin da take shirin fadi, kama hannayenta ya yi cikin ban hakuri ya ce" Basma bansan ma nazo ba, kiyi hakuri my baby " ya karashe zancen cikin kashe murya.

Basma kuwa sauke ajiyar zuciya mai sanyi take yi akai akai domin ta tabbarar macijin ya shigo jikinsa.

 Cen Cikin dakin kuwa duk hirar da Basma da Isah suka yi duk a kan kunnensu, Allah yakyauta suka furta tare da dawowa kusa da Fauziyya da barci barawo ya yi awon gaba da ita.

Jibrin fifita yakewa Fauzy cike da kulawa, sai fadi yake.

 " Wannan lalurar Fauzy bata asibiti ba ce, zan kawo Abbana yanzu ya dubata ze iya gane me yake damunta " ya yi furuci cike da kulawa.

Mamy girgiza kai kawai take ita kaɗai ta san halin da take ciki.

 

Cikin karfin hali ta ce.

" Jibrin Alhaji yasaka maka da Alkhairi, samun irinka babban saa ce arayuwa " karashe zancen ta yi cikinsanyin murya.

 Da" Ameen " suka amsa dukansu dakin.

 

Bayan kwana biyu

Tun bayan sallah asubahi Ridwan be koma ya kwanta ba, safa da marwa yake ta yi cikin dakinsa, sakawa da kwancewa yake ya rasa ta inda ze kamo bakin zaren abin da ke damunsa, samun damar makalewa jikin bangon dakinsa ya yi yana tuno abin da ya faru shekarun baya, dode kunnuwansa ya yi sakamakon jin kamar harbin bindiga yake ji anayi agabansa, duk da shi ɗan sanda ne amma wancen harbi da yake jin sautinsa na rikirkita tunaninsa yana nuni da alokacin shi ba dan sanda ba ne yana nuni kamar bakon abu ne a wajensa a wannan time din, jujjuya kansa yake yana ganin kamar abin da ya faru shekarun baya sune yake faruwa yanzu haka reality agabansa.

Cikin fitar hayyaci da tsoro yake fadin " Abba an kasheka ko? Abba ka bude idanunka, Abba ni ne Ridwan dinka, ga Faisal dinka cen yana barci ". Azauce yake sassaka kalamansa, wanda ya ja hankulan gabakidaya all din yan Gidan har ma da ma'aikatansa da masu aikin gidan.

Mamy da sautin maganganun sa ya fito da ita dakinta, tana fitowa ta ci karo da Anisa da Amina, sun fito daga dakunan su, Faisal da dukan alamu daga barci ya tashi dan idanunsa na dishi dishi, cikin hanzari suka haura sama domin zuwa ganewa idanunsu.

Me aikin Gidan wacce suke kira da Dumbaru yar matashiya ce kalarta kalan Dumbaru na industry yarinya ce wacce bazata haura shekaru Ashirin da biyar ba. Salati take yi da dogon bakin nata tare da fadin.

 " oh Shugaba Ridwan lafiya yake surutai, shi dai kullun duk yanda nake ado dan in burgeshi sam baya kallona, anya yana da idanu kuwa, yanzu ma fa nasaka doguwar riga wanda ta matseni., karshenta yana fitowa ya watsa min harara tunda shi be san abun arziki ba, bari dai in bi bayansu dan in ji me ke faruwa da Honey na ". ta karashe zancen cikin dan sauri saurinta tana tafiya tana kwarkwasa.

Cen Cikin Dakin Mamy sosai ta rikice dan jin yanda yake kalamai daga bakinsa, Mamy na ƙoƙarin dafa shi ahanzarce ya bude idanunsa da suka kada jajir, hannu ya mata alamun kar ta kuskura ta taba shi. Cak ta tsaya tana kallon Anisa da Amina da ke suke taba shi be ce komi ba, Faisal ma hannunsa ya rike shi ma be ce komi ba, sai ita ce ze hana ta taba shi, take tambayar kanta yanzu fa Ridwan yana nufin bata isa ta rabe shi ba? rasa me bata amsa maganar zucin da take ya sa ta kallonsa yanda ya bude idanunsa yana kallon kannensa da suke masa magana cike da kulawa, ba karamin dadi ya ji ba, hakan ya sa ya kama Anisa da Amina ya rungume su atare, shi ma Faisal janyosu ya yi yana kara matse su ajikinnsa, fesar da numfashi ya yi sannan ya sake su, kallon Mamy yake yanda tashin hankali ya bayyana karara afuskarta, har ya taho ze rungumeta yana tuna wani abu da baya baya ya koma yana mai ƙoƙarin shiga ban daki domin ji yake komi ze iya faruwa.

Dumbaru abakin Kofa ta tsaya tana kallonsu, cikin kasa da murya ta ce.

 " Mijina Ridwan be son ana takura masa dan haka kowa ya fita yabar mana dakin". Cikin mamaki ta ga Mamy ta wuceta tana sheshekar kuka, ahanzarce Faisal da Anisa da Amina suka take mata baya, koda suka zo kusan Dumbaru sun zata ta zo gyaran dakin Ridwaan ne, bayan sun san in yana ciki be yarda a masa gyara ba, ba su bi ta kanta ba suka wuce ta dukansu, suna barin wurin kwabe baki Dumbaru tayi, sai leka dakin take tana tunanin kar ta shiga ya korota kamar yanda ya saba, ahankali ta fara taku tana tura kofar dakin, Ridwan da yake zaune yana amsa waya da dukan alamu da Mansur yake waya, fuska babu annuri, lumshe idanunsa ya yi kamar me barci yana sauraren Mansur, ahankali ya fara bude idanunsa tare da sauke su a kan Dumbaru, kwalalo idanu waje ya yi yana mai kallon kansa da ko riga babu ajikinsa, sosai Dumbaru take kallon gargasan jikinsa yanda gashin jikinsa ya kwanta gwanin ban sha'awa, ganin jikinsa take kallo ya sa shi hada rai tare da katse wayar. .

Tsawar da ya daka mata, gigitar da ita ya yi har saura kadan ta yi tuntuɓe ba.

 " Me kike nema adakina bayan kinsan ban fita ba?". ya yi tambaya yana kallonta da idanunsa masu kwarjini.

 " Wallahi yallabai Ina sonka ". ta fada saman labbanta.

 " Me kike fade ne? Kin yi shiru ni fa ban son iskanci ya za kiyi ta Magana kasa kasa ba'a ji ".

 " Yi hakuri Yallabai daman, ina bukatar kuɗi ne, Mamata cen gida ba lafiya na kai sati ban sanin fitarka da shigowarka shiyasa dana ga su Mamy sun zo shi ne nazo ko Allah zesa asamu. "

 Shiru ya yi yana kallon kasa alamun tunani kafin ya iya furta

 " Ok ki je wurin Mai Gadi zan bar masa kudi, ze baki, Allah ya sauwaka ya bata lafiya, dan Allah kar ki sake shigomin daki bana so " ya ƙarashe zancen cikin tsanani ɓacin rai.

 Ita kuwa ba karamin jin dadi ta yi ba ganin yau ta yi fira da Ridwan har tsawon wasu mintuna.

Hanzarta barin dakin tayi, shikuwa yana ganin fitar ta, tashi ya yi yaje da kansa ya rufe kofar, tare da yin hanyar ban daki domin yin wanka da bukatun sa.

 

Karfin Iko sosai yake Safa da marwa a cikin babban Falonsa, gefensa Malam ne, hagunsa kuwa Hasina ce, cikin tsananin damuwa karfin Iko ke fadin.

 " Amatullah tana hannun Dsp Ridwaan mai Nasara, taya zan kwato ta, wallahi bazan iya barinta ba, nasan halinsa ze iya yimun tarko da ita, Ridwaan babban Jami'i ne mai ƙwaƙwalwa kamar Computer yanada wayau fiye da tunani, ko tafiya yake baya barin sawayensa a fili, baya tafiya sai da waiwaye, ai tunda Ridwaan ya yi nasarar kama wani dan ta'adda da ake nema sama da shekaru ashirin, ina tabbatacin kamani, ba ze masa wahala ba, sai de inda matsalar take yarinyar da ke hannunsa badan ita ba, wallahi yanda na zama duhu agaresa ahaka zeci gaba da tafiya " ya karashe zancen cikin tsananin tashin hankali.

Malam cike da damuwa ya ce " Haruna na fika shiga damuwa Yarinyar nan nasanta wallahi !! Bansan samu damar yin Magana da ita, kaddara ta sake rabawa" ya ƙarashe zancen rai a dagule.

Karfin Iko ahanzarce ya ce " karfa ka ce kana son Amatullah fa?.

 

 Malam ne ya yi hanzarin fadin " ni in so Amatullah kake nufi?".

" kwarai kuwa, haka nake nufi ". Cewar Karfin Iko.

 "Haba !! Amatullah ai kamar ya ce a wurina kaɗaina wannan zancen a samu mafita kawai ta yanda za mu sato ta daga hannun Ridwaan Mai nasara ". Ya ƙarashe zance yana kallon Hasina da ke jînjina gaskiyarsa.

Hasina cikin karfin hali take fadin.

 " Akwai hanyoyi da dama da za mu gwada domin kwato Yarinyar nan hannun Ridwaan, barinta hannusa zeyi yanda zeyi ganin ya san siririnmu dan shegen wayau da naci gare sa. ".

Karfin Iko fesar da numfashi ya yi yana mai kallon Hasina cikin huci tare da fadin.

 " Ai babu wani sirrinmu da Amatullah ta sani " ya yi magana cikin babban murya.

 

 Hasina cikin dukar da kai ta ce.

 Wallahi Haruna na sanar mata da sirrin Gidan nan hatta gidan nan sai da na karanto mata sunan Unguwar, dan Allah ka yafe mun bansan hakan ze faru ba " ta karashe zancen cikin neman afuwa da nadama.

Karfin Iko kallonta yake cike da tsoro da takaicinta, kasa magana ya yi ya dunkule hannayensa yana dukar iska.

 Malam ne ya numfasa yana mai samun kansa da zama kan lallausan kujerar falon, kallon Ƙarfin Iko yake cikin tausasa lafazi yake fadin.

 " Haruna ka daina damuwa da zancen Amatullah karta tona asirin Gidan nan, nasan bata da wayon yin haka, abin da ya fi cancanta shi ne ka amso ta daga hannunsa dan gudun kar ya cutar mana da ita kasan shi yana da fadin rai " Malam ya karashe zancen yana jin babu abin da yake bukata da gani sama da Amatullah. Zama suka yi dukansu suna nazarin yanda za'a shiryawa Ridwan tarko domin kwato Amatullah daga hannunsa.

 

 

Ridwaan zaune a office dinsa rubutu yake kan wani file gabakidaya ma'aikata sun zagaye shi, knoking da akayi daga waje ne yasa, sakatariarsa shigowa cikin shigarta na dogon riga abaya mai adon stone, kasantuwa abayar ja ne ba karamin kyau ya yi da dan madaidacin jikinta ba, siririyar muryanta ta doka sallama kana cike da Respect ta ke sanar masa da sakon Commission da kuma tana neman yiwa mansoor iso a garesa, duk maganganun da take kallonta yake rike da habarsa, kana ya dan yi gajeran tsaki, tare da fadin " Rakiya duk wata ma'aikaciyar yan sanda irinki sun san waye Mansoor a wurina, daga yau kar ki sake gangancin hana shi shigowa da fatan kin gane?".

Cikin hanzari ta gyada masa kai kamar kadangaruwa.

Ya kara da fadin.

 Shi kuma Commissiner zan kira wayarsa, kin hanzarta barin Mansur ya shigo, kina fita ki rufe min kofa " ya karashe zancen yana mai mai da hankalinsa kan aikinsa.

Gabakidaya ma'aikata soma fita suka ringa yi dan sun san in har Mansoor ya zo office baya son ganin kowa kusa da su.

Suna fita, Mansoor ya shigo Office din cikin shigarsa boyel maroon colar ba karamin kyau ya yi da hular kansa da takalmi ba, fuskarsa ɗauke da murmushi ya zauna suna face din juna, musabaha suka yi cike da girmamawa kana Mansur ya yi saurin fadin.

". Ridwan haka ake Rayuwa kasa ankai yarinya gida kai baka ce komi ba, yarinya bata da aiki sai kuka ".

Kif kif da idanu Ridwan ke kallon Mansur, cikin mamaki yake maimaita" kuka kuma?".

" kwarai kuwa, kukan take sai kiran sunan Papy take, kuma kai bakamin bayanin komi ba akanta bare har na baka shawara akanta". Cewar Mansur cikin damuwa.

" Ridwaan mikewa tsaye ya yi yana mai tafiya kamar ingarman doki, taku yake irin nasu na yan sanda kana ya nufi wurin window office din idanunsa na kallon farfajiyar ma'aikatan. Cikin kasan zuciyarsa da tsananin damuwa a bayyane a saman fuskar, cike da raunin sa ya ce.

" Mansur ka gafarceni na Daura Aure ".

Zumbur Mansoor ya mike daga zaune yana kallon keyarsa, cikin tsananin tashin hankali domin ya zo ne ya sanar masa da yanda Mansura take sonsa. Cikin surprise din zancen har bakinsa na rawa ya ce.

". Ridwaan dan Allah kasan ba mu saba irin wannan wasan ba, Please dan Allah kar ka fara a yau ". Ya karashe zancen cikin kaduwa.

 Ahanzarce Ridwaan ya waigo yana murmushi mai ciwo bakinsa cike da yakini ya ce.

" Dagaske nake nayi aure, zan iya wasa a kan komi ban da irin wannan ".

 " wacece matar ka my Rid".

Ridwaan cikin gaskiya da gaskiya ya ce. .

Na duri diyar. . . . . . . . .

Taku har kullum Kyauta daga Allah

[10/23, 8:14 PM] Kyauta Daga Allah: https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

Makauniyar Shari'a

 Sai a lahira

 NA

 IKILIMA ADAM

 (Kyauta daga Allah)

 09069080725

Saura page biyu in gama free page, ki hanzarta biyan naki domin a yi tafiyar da ke

Ku nuna mun soyayya ta hanyar following dina a arewa book, a kan suna kyautadagaAllah10

Ga link din https://arewabooks. com/book?id=6536baf758cd413f0dcb1996

Zaku samu complete din makauniyar sharia da aauran littafaina

 Jarumai writ associations

 SHAFI NA ASHIRIN DA UKU

 

 " Na auri diyar. . . " sai kuma ya yi shiru be karasa ba, yana taune lip dinsa.

" Kayi shiru ina magana haba Ridwaan ka gayamin abin da yake faruwa, ni shakikinka ban sani ba " cewar Mansur cikin tsananin mamaki da jiran amsa.

Ridwaan kallonsa yake kamar wanda sam beda damuwa tattare da shi, cikin dabiarsa da na yau da kullum tare da tattara nutsuwarsa a kan Mansur, cikin rashin sanin makama ya fara fadin.

" Wallahi Mansur auren nan na wucin gadi ne aiki na ne ya biyo ta hakan domin kama tarkona, Commissioner shi ne yabani ba ni Umarnin yin haka, kai ma kasan in har zanyi abu dan kare kasata komin wahalarsa ina yi, ba kowace yarinya ba ce na aura sai wannan Amatullah da ke tare da ku a gida" ya karashe zancen yana mai jin zafin hadin Commissioner da kulla alakar aure.

Mansur sankaka sake da baki yake juya wai Amatullah ya aura in har ze iya tunawa yarinyar ta masa kama da wacce suka taba gani a kauye, sannan kuma ta ina ta bullo ta iso Abuja. dafa shi da Ridwan ya yi hakan ya sa shi dawowa hayyacinsa a firgice.

" Zauna muyi magana don na ga kamar abin be maka dadi ba, kamar yanda nima be min dadi ba " cewar Ridwan cikin rauninsa.

 Mansur fesar da numfashi ya yi yana kallon Ridwan ya kawo kujera biyu ya hade su wuri daya. Jiki babu kwari ya zauna kujerar da ke kusa da wanda Ridwan din ya zauna. Kallon Ridwan yake yanda yake kallon sama kamar me tunani, kana ya yi saurin sauke kansa kasa yana kallon sa kana ya furta.

" Mansur a jiya aka daura kuma yarinyar tana da masaniya dan Commissioner da kansa ya mata magana ta amince duk da nasan be kai ciki ba, na ga tsananin tsoro tattare da ita, auren yarinyar nan da kuma fitar da sanarwar aurenta ze sanya Karfin Iko yin yunkurin yin komi domin nayi bincike na tsananta bincike karfin Iko yana tsananin son yarinyar nan akanta ne ze shigo hannu, shi kansa ba tare da ya ankare ba" cewar Ridwan cikin damuwa.

" To me me ya sa ba zaku yi karya ace ka aure ta ba, tunda kunada damar yin hakan " cewar Mansur cikin soma yarda da maganganun Ridwan din, ya san karya ba dabi'arsa ba ce.

 " Eh bazan iya yin karya ba Mansur sashina zata zauna, kuma kai kasan ajiye ta babu aure ze kawo zargi a kan yan gidan mu, bare kuma daga majiya me karfi suka san ba gaskiya ba ne, za'a min kallon mutumin banza bayan nasan bazan iya aikata komi da wannan yarinyar ba". ya karashe zancen yana mai rike hannun Mansur.

Numfashi Mansur ya fesar shima damke hannun Ridwan ya yi sosai cikin nasa, kana ya murmusa cikin fara'a da sakin fuska ya ce.

" Wallahi na gamsu dari bisa dari kuma wannan hanya ce ka ɗauka domin kawo nesa kusa " cewar Mansur yana kallon Ridwan.

Ridwan murmushi ba dabi'arsa ba ce amma yau kam saida ya yi na gefen baki, kana suka dauko hirar Mansura a kan yanda take son Ridwaan din.

Ridwaan cikin damuwa ya ce

" Abokina kai kasan in har zan iya aure da tuntuni nayi, Mansura bazata gane ba, bazan iya aurenta ba, ni fa kwata kwata bansan me Ma'aurata suke ji in sunyi aure ba da za su shafawa kansu lafiya da sun zauna kalau, aure sunnah Manzon Allah Sallallahu alaihi Wasallama ne, amma da sai ince a zamanin Annabi akayi me dadi da ni'ima, ni auren wucin gadi nayi kai kasan bazanyi aure ba, ita ma wannan zaka ga yanda zan sallameta cikinsauki " cewar Ridwan cikin yakini.

Murmushi Mansur ya yi yana juya kalaman abokinsa, kana ya yi karfin halin fadin.

" Humm bazance komi ba amma su Mata ba'a musu hakan ita ma wannan din bar ganinta kwaila wallahi tafi Mansura baiwa da komi" ya karashe zancen cikin yakini.

Tsaki Rudwan ya dinga jerowa akai akai yana kara jin haushi furucin Mansur, cikin yatsine fuska da takaici ya ce. .

 " Ni fa ka daina hadani da wannan yarinyar saboda ko lissafin Mata ban sanyata ba, ai gwamma Mansuran in har dagsk Auren zanyi ita ce ta fi cancanta, kawai ma abar zancen nan, Mansura kuma Please kar mu sake Maganarta a barta bana so " ya karashe zancen cikin tsanani jin haushi.

Mausur kuwa murmushi yake dan ya san Ridwan komi a duniya in ya nema ze masa in har ya halarta amma ban da ba shi shawara a kan aure, fesar da numfashi ya yi hakan ya sa suka fara wani hiran da ya shafi aikin Npower da Mansur ke jagoranta in har babu Ridwan a kusa.

 

Abokin Umar a Gidan me Gidan Umar ya sauka me suna Alhaji Abdullahi, sun yi sintiti har sun gaji ba su samu damar ganin Umar ba, Alhaji Abdullahi da kansa ya nemi ahada da Dsp Ridwan Muhammad Mai nasara domin an ce case din a hannunsa yake, sun samu damar zuwa koda suka zo yan sanda da ke kai kawo sunce in har me gidan nasu yana tare da shakikinsa Mansur baya amsar kowa in har ba Umergency matsala ba ne ya taso.

Sun dade Zaune Usman sai sakawa da kwancewa yake hannunsa rike da carbi tunawa ya yi yau yau befi saura kwana goma a kotu ba, hakan ya sa shi girgiza kai yana tunanin yanda zata kaya a zaman da za'ayi na gaba.

Har sun fidda rai da fitowar Ridwan din, sai gani suka yi ya bude kofar office dinsa, Alhaji Abdullahi cikin zazzare idanu yake kallon Ridwan din, ya ganshi fari tass karfafan Namiji a tsaye, duk wani abu da ake kiran namiji mai haiba duk ya tattara uwa uba kyakkyawan ne fari sangiri, gefe daya kuma sosai yake kallon yanda suka yi mugun kamannin da Muhammad Mai Nasara duk da ya san Ridwan din ze mance shi ɗan tun yana yaronsa suke zuwa gidan, dayan kuma zuciyarsa tunowa da Mamy ya yi nan da nan ya ji ransa ya sosu akanta, karasowar Ridwan gabansu ya sa shi dawowa hayyacinsa firgit.

Murya na rawa Dr Abdullahi ya ce.

" Ridwan mai Nasara dan Jagindi da ke jahar Kaduna, Ko ba haka ba?" ya yi tambaya yana tsare Ridwan da idanun.

Be bashi amsa ba duk da ya ji abun da yake fade, illah son ya wuce kusa dasu ya yi, shi da Mansur, ahanzarce Usman da Alhaji Abdullahi suka take masa baya, ganin yana musabaha da jama'ar wajen, hakan ya nuna kamar ya tashi daga aiki  ba suke nan. Ahanzarce suka sha gabansu shi da Usman. . .

Ridwan kallon kallo suke wa juna shi da Alhaji Abdullahi, kana ya fesar da numfashi, hannun Alhaji ya mika masa suka yi musahaba, kana suka gaggaisa har da Mansur din.

Alhaji Abdullahi cikinsakin fuska ya ce " Haba Ridwan ni abokin mahaifinka ne tun kana yaro na sanka kuma dani da Mahaifinka akaje neman auren Saratu a Jagindi watau Mahaifiyar ka.

Ridwan sosai yake nazartan kalaman sa jin ya ambaci mahaifinsa cike da girmamawa ya kara basa hannu suka yi musabaha, bakinsa na rawa ya ce.

" Abba ka yi hakuri, akwai dayawa masu zuwa damuna ba tare da wani dalili ya kawosu ba, nasan yanda nake sannanne ba abu me wuya ba ne dan ansan garin mahaifiyata ba, shin Alhaji lokacin da Mahaifina ya rasu kana ina? ina ga banga fuskokinka cikin wa'yanda suka zo zaman makoki ba, abar wannan zancen yanzu akwai taimakon da zan maka ne?" ya yi magana cikin ladabi.

Alhaji Abdullahi girgiza kai ya yi domin yanda Ridwan ya jero masa tambayoyi ya tabbatar ba yaron yanada zurfin ilimi da hangen nesa.

" Ridwan daman nazo ne a kan yaron nan da aka kama watau Umar Isah Sharifai, sam anki ba mu damar ganinsa hakan ya sa nasa ahadani dakai dan zatin Ubangiji ka mana hanyar ganinsa, sannan muna so mu zauna dan jin irin laifin da ake zarginsa da shi, sannan kayi magana a kan Mahaifinka ina ina ya rasu banzo gaisuwa ba, bana kasar ma bakidaya, amsar wannan tambayar yana bakin Magaifiyarka ko kuma in ce in lokaci ya samu zan fada maka komi a kan Mahaifinka nasan bakasan wasu dayawa daga ciki ba "

Numfashi Ridwan ya sauke yana kallonsa hade da nazartansa yanayinsa da kalamansa, cikin hanzari ya ce.

" Umar Faruk ku bari zuwa gobe karfe goma zaku gansa da kunzo ku nemi sakatariya ku ce mata ni ne nace afito da Umar, dan Allah zan iya tafiya dan akwai inda zan je sauran maganganun za mu karasa in mun sake haduwa " ya karashe zancen yana juya kalaman da Alhaji Abdullahi ya fada masa da ya je ya tambayi Mamy, barin wani tunanin ya yi suka barsu nan tsaye shi da Mansur.

 

Mansura zaune a farfajiyar Gidan ita da Amatullah da ke goge hawaye dan tunda ta ji wai andaura mata aure da dan Sanda ta san ajalinta ne ya zo dan ta yi imani kuskure kadan zata aikata ya harbe mata kai, Mansura da ke mata kallon yar yarinya matashiya cikinsakin fuska ta ce. .

" Wai ke Amatullah ba za ki saki jikinki ba, nan fa kamar Gidanku ne, bakiga inata koyamiki abubuwa ba, kuma fa yaya Mansur har Makaranta ya ce ze sanyaki, ki nutsu daman ban da yar uwa mace tunda na sameki ai dadi naji kafin lokacin aurena da yaya Ridwan ya yi shi ne kawai ze rabamu" ta karashe zancen cikin shauki sai da dimple dinta ya lotsa.

Zazzare Idanu Amatullah ta yi jin wai Murna take in har akayi aurenta da wannan malakun maut din, dayar zuciyarta take fadin. . .

"  ba suke nan ni da Mansura ze hada ya fallewa kai  ba suke nan? " rasa me bata amsa ya sa ta mayarwa Mansura da murmushi.

Sosai idanunta ke kallon yanda tsuntsaye ke shawagi a sama kana yanda tsakar gidan yake a tsare babu wasu motoci sai kwaya daya kacal wanda da dukan alamu motar Mama ce.

Mansura sai zuba take ita kam Amatullah da idanu take bin ta da shi tana yar murmushi.

 

Salim yana kwance ya dan fara samun sauki, likita ne ya shigo dakin, cikin shigarsa na likitoci hannunsa ɗauke da file, cikin fara'arsa ya ce.

" Mama congrat an samu wanda ya dau nauyin fitar da Salim kasar waje dan haka mun tattara takardu ranar Monday zaku tafi, dan haka zan bada kuɗi a muku password Umergency, sannan in ya samu lafiya ya dauki nauyin karatunsa acen kasar waje ze iya karasawa tunda ya yi nisa" cewar likita cikin jin dadi.

Mama cikin hanzari ta durkushe kasa, kuka take sosai iya ranta dan sun fidda tsammani, murya na rawa ta ce.

" Dan Allah wani dan Aljanna ne ya taimaka mana? Ina son in masa godiya, Allah ya rabasa da kunci da baƙin ciki Allah ya daurasa a kan makiyansa" ta karashe zancen cikin muryan kuka.

Docto kallonta yake yi, cikinsanyin murya yace.

" Me yi dan Allah ne baya son a sani baya fadar sunansa, baya son godiya ke dai ki gode wa Allah, dan ni kaina cikin takardan ansa Fisabidillah babu suna akai sai yawan kuɗaɗen da kuma bayanan wanda ake son ataimakawa " ya karashe zancen cikin jin dadi.

Mama da ke kallon Salim yana murmushi, tashi ta yi zaune cikin farin ciki ta rike hannun Salim tana fadin.

"Kaga dan Aljanna ya taimaka mana Allah ya biya masa da bukatunsa duniya da lahira " dukansu da Ameen suka amsa har salim din, shi da a saman labbansa ya amsa amma kana ganinsa kasan yana cikin farin ciki.

Da jim ya yi gefe daya na zuciyarsa yana tunanin in har ya samu dawowa ta ina ze fara neman Amatullah domin ya cika mata burinta na gina mata gida ya kuma aure ta domin cire ta cikin wahalar rayuwa, ya dade yana tunani har Likita ya bar dakin be sani ba. .

 

Bayan sati daya

Kwanaki na shudewa inda ya rage be fi saura kwana uku a koma zaman kotu ba.

Barister Hadiza Ibrahim bincike take yi babu kama hannun yaro, sosai Hajiya Basma ta tsorata jin wai Hadiza Ibrahim har cikin gidan nasu ta zo yin bincike,  ba suke nan Boka yana nufin aiki be kama Hadiza Ibrahim ba  ba suke nan take tambayar kanta, rasa me bata amsa ne ya sa cikin hanzari ta shirya ta tafi wajen bokanta. Tana zuwa ta iskesa da baki, bakin na tafiya ta zauna cikin damuwa ta zayyane masa damuwarta shi kuwa yana bugawa kasa cikin rawar murya ya ce.

"Kyale Hadiza Ibrahim na lura mace ce wacce bata wasa da adu'oi, ai in ita be kamata ba Alkali dole ne ze kamashi tunda shi ne me yanke hukunci. Kuma kar ki damu dan Fauziyya ta warke na gayamiki surikinta maye ne, abin da za'ayi kawai a yi yanda kika ce wajen sanyawa mijin nata sha'awar karin aure a nan ne zata gane ƙurenta " cewar boka cikin yakini.

Basma ta ji dadin haka inda ta ajiye masa makudan kudade kana ta bar wajen gudun kada Alhaji Isah ya dawo be ganta ba.

Tana komawa gida iske Nasara diyarta da Basira da Badariyya ta yi har ma da Laila suna tikar rawa, tsakiyar falo ko ina sashin tashin hayaniyarsu ake ji.

 Tana kallonsu tana dariya tare da wuce su bata ce musu komi ba, su ma ko sannu da zuwa ba su mata ba suka ci gaba da tikan rawa cikin kananun kayansu riga da wando da ke jikinsu.

Nasara sai fadin take.

" Allah ya kaimu Kotu a kora mana ya'yan awaki daga gidan nan" ta yi furucin tana tikar rawa.

Laila ce ta dan bata rai cikin yar murya ta ce.

" Su da Gidan Ubansu za'a koresu, ai tunda muma muna zaune ciki, su ma babu inda za su je " ta karashe zancen tana cigaba da rawar ta.

Sosai kalaman ya ratsa kunnuwan sauran yan Uwan nata, ahanzarce suka kashe kidar da ke tashi tare da matsowa kusa da Laila suna juya kalamanta cikin tsanani ɓacin rai.

Nasara ta ce " ke amma Laila bakida hankali ko? ni kike gayawa ba za su bar gidan ba? ". ta karshe zancen cikin fada.

" kwarai kuwa ba za su bar gidan ba ai suma ya'yan Daddy ne, kuma bakiga yanda Yasmine take kama da Kakan mu Muhammadu ba, kuma Anty Fauziyya tana kama da Daddy " ta karashe zancen cikin turo baki.

Caraf kalamanta cikin kunnen Alhaji Isah da Hajiya Basma da ke saukowa daga kan matakalan step saboda jin tashin hayaniyar fada.

Zazzare Idanu Basma ke yi jin yanda Laila ta yi furuci babu tsoro, bata ankare ba sai ji ta yi Nasara ta ɗauke Laila da zafafan maruka guda biyu. Tana ƙoƙarin kara mata wani marin ne ta ji kakkausar Muryan Alhaji Isah yana fadin.

" Dakata " kar ki kara marinta, in har ta yi laifi gyara mata za'ayi kuma abin da ta fada ina ga fahimtarta ce sai kuma barta a hakan tunda kunsan yarinya ce, dudu bata fi shekaru 15 ba, kunsan bana son ɓacin ranta " ya karashe zancen tare da kama hannun Laila ya yi sashinsa da ita tana kuka, ko magana beyi wa Basma ba dan yaga ranta a ba ce yake.

Nasara cikin takaici take fadin.

" Laila zata sani ne har ta fito " ta karashe zancen tana hura hanci, sun dade suna hira da Basma tana ba su hakuri kana suka dan manta da batun, cigaba da rawa sukayi bayan sun kunna kida.

Mamay Zaune a dakinta daga ita Kaka da Yasmin dan sosai ta ji sauki ta warware kamar ba ita ba, soma lissafin inda zata je take yii, bayan kotu ta koresu, cikinsanyin murya ta ke fadin.

" Kaka yanzu in har bamuyi nasara ba ina za mu je ne? "

Kaka cikin rawar murya ta ce " A'isha ai keko kike da wurin zuwa kedai bari akai karshen zaman kotun za mu samu mafita, wallahi mazan yaran nan suna da ƙoƙari wlh, saboda su muke cin abinci " ta karashe zancen cikin jinjina ƙoƙarin su.

Mamy cikin rashin walwala ta ce " ni a kotu zan sa a raba Aurena da Isah, in sha Allah aure zanyi dan Isah ya fita araina kwata kwata, kiyayyar da yake nuna min ya sa banko kaunar ganinsa " ta kai karshen zancen cikin damuwa.

Kaka da ke kallon Yasmin da ke shan garin kwaki da suga a kofi, cikin damuwa ta ce" Wallahi Isah ze. . . . . . . . . .

Kar ku Manta saura page biyu a gama free page kin hanzarta ki biya kar a yi babu ke.

Taku har kullum Kyauta daga Allah

[10/24, 9:30 PM] Kyauta Daga Allah: https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

Makauniyar Shari'a

 Sai a lahira

 NA

 IKILIMA ADAM

 (Kyauta daga Allah)

 09069080725 ko +22953726162

 Saura page daya kacal in gama free page wa'yanda ba suyi payment ku hanzarta, kada a yi tafiyar babu ku

Turo kudin ki kan asusun banki 3115484026 ikilima adam First bank

 Jarumai writ associations

SHAFI NA ASHIRIN DA HUDU

Cikin damuwa ta ce.

  Wallahi Isah sai ya yi kuka da idanunsa sai ya gwammace da mutuwa da. . . . " Mamy ce ta hanzarta dakatar da ita cikin raunin murya tana fadin.

 " A'a Kaka kar ki masa baki dan Allah wallahi duk da halinsa wani abun in yanayi sai in ga kamar tilasta shi ake, ke Mahaifiyarsa ce kina masa baki zeyi gaggawar kama shi ɗan Allah ki sassauta kalaman ki a kasan Please na roke ki " cewar Mamy cikin tsananin damuwa.

Kaka jan majina ta yi tana jinjina karfin kaunar da Mamy kewa Isah da be san darajarta ba, murya a shake ta ce.

". A'isha tunda baki so nayi shiru " tana kai karshen zancen ta mai da dubanta a kan Yasmin da ke kwance, bayan ta gama shan garin kwaki da suga, lumshe idanu take akai akai kamar me jin barci, Kaka gyara zama ta yi tare da gyara daurin zaninta, cikin shakewar murya ta ce".

" yanzu wa ze kalli Yasmin ya ce ba jinin Isah Sharifai nace" ta yi furucin tana kar kada kai.

Ahanzarce Yasmin ta bude idanunta tana kallon Kaka da ke kare mata kallo na tsanaki, yamutsa fuska ta yi cikin turo karamin bakinta ta ce.

" Ni fa dan Allah ku daina haɗani da Isah bana so " ta kai karshen zancen tana turo karamin bakinta.

Kaka murmushi ta yi cikinsakin fuska ta ce.

" Haba kishiyata to meye abun damuwa dan an ce kina kama da mijin uwarki kuma uban naki". Ta karashe zancen cikin yar zolaya.

Sosai ran Yasmin ya baci sanin Kaka ce ya sa bata tankaba dan sam bata son a danganta ta da Isah ko wani nashi ban da Kakar ta.

Barister Hadiza zaune daki tana tattara bayanai da ke cikin farar takarda, jin kiran Sallah daga massalaci ya tabbatar mata lokacin azahar tayi, tana ƙoƙarin tattara file dinta, Mijinta ya shigo ahanzarce da dukan alamu beyi nisa da gida ba, yana karasowa kallon tulin file din da ke gabanta yake cikin tsananin bacin rai, cike da takaici ya ce.

" Hadiza " ya kira sunanta da amon murya.

Cikin hanzari ta dago kai tana kallon sa fuskarta ɗauke da zallan mamakin yanda ya kira sunanta dan ba kasafai yake kiran sunanta ba sai yana cikin bacin rai.

Fesar da numfashi ta yi cikin hanzari ta ce.

" Na'am Baby" tana kallon yanda yake hura kofofin hancinsa.

 " Inace ni na sanyaki irin aikin da nake domin taimako al'umma da kuma taimaka min inhar aiki ya kankama" ya ƙarashe zancen yana ciza bakinsa.

" kwarai kuwa me gida kai ne ka sanya ni aikin nan kuma, ka ce in taimaki al'umma in kwatowa wanda aka zalunta hakkinsa na ga ban saba alkawari ba kai ma kasan aikin nan da nake ba dan kuɗi nake yin sa ba, kuma maganar aiki in ya kama muyi tare, ai na ga kamar kusan case daya muke aiki akansa ina nufin kana bangaren masu kara, ni kuma ina bangaren me kare wacce ake kara, yanzu meye laifina a nan?, kowa ya iya allonsa ya wanke " ta ƙarashe zancen fuska a sake.

Cikin tafasar zuciya barister Sani ya ce.

" Hadiza ni kike fadawa kowa ya iya allonsa ya wanke?".

 " Yi hakuri baby na, kai kasan kafi karfin in raina ka dan aljannata tana kar kashin kafarka, kuma ai abun alfaharinka ne kaga yau na taimakawa wa'yanda aka zalunta, kasan Allah ze baka lada dan saboda kai na zama wani abun a yau " ta ƙarashe zance cikin dacin rai.

 Dunkule hannayensa ya yi yana buga bubbuga su, ya dade yana nazartan kalamanta kana ya dan rage murya cikin fada ya ce.

" Ga Fili ga mai doki " ya karashe zancen tare da hanzarta shiga ciki domin dauro alwala.

Ita kuwa keyarsa take bi da kallo tana kwabe baki hade bin hanyar dakinta tana jîjina karfin hali irin nashi lokaci daya duk ya canza saboda kawai an bashi makudan kudade.

 

Kashe gari

Mansur ne ɗauke da jakar Laptop transparent a hannusa mai ɗauke da fararen file a cikin, sanye yake cikin maroon din shadda wanda ya dinki gun kwararre tela, cikinsakin fuska da murmushi yake kallon yanda Ridwaan ke sanye cikin irin suturar da ke sanye jikinsa har dinki da komai nasu iri daya, ganin yana fesa jikinsa da turaruka masu daddan kamshi ya sa shi lumshe idanu, kana murya a sanyaye ya ce.

 " Angon Amatullah, wannan haduwar duk na ganin Amarya ne dan ka ce sai mun fara zuwa gidanmu sannan mu je office din, aikin din Npower ne yau, filin bana yan sanda ba ne " ya karashe zancen cikin zolaya.

Ridwaan da ke gaban mirrow yana gyaran hular kansa, numfashi ya fesar, ya yi kamar sam be ji me Mansur din yake fade ba, a tsanake ya gama shirinsa tare da sanya takalminsa mai dan karen tsada. .

Yana daukar wayoyinsa kallonsa ya dawo da shi kan Mansur cikin muryansa ta dabi'a ya ce dan miko min katin invitation na bikin nan, dan za ka je rabawa, wajen aikin namu, kana ina sauka zan sanar da mamy yanda ake ciki " ya karashe zancen cikin halin ko in kula da me ze je ya dawo.

Mansur mika masa ya yi,

Babu bata lokaci suka fice daga dakin.

Mamy zaune daga ita sai Madina sosai suke shawara a kan jiran isowarsa Ridwan dan Malam ya ce yana fitowa da maganar auren Madina ze tare su, hakan ya sa Madina ta ci babban shadda gezner red colors, doguwar riga wanda yasha adon stone work, sosai dinki ya zauna mata, gwala gwalan da ke wuyarta na tsarka kara fito da ainahinta ya yi, sosai take ba za kamshi dan yau babu abin da take da buri illah ganin angonta Ridwan.

Mamy cikinsanyin murya ta ce " ai ga shi nan zuwa ina jin takun tafiyar sa. "

 Cikin hanzari Madina ta gyara zamanta tana kara goga turare ajikin ta.

Ridwaan da Mansur tun daga sama suke kallon Mamy da Madina zaune kamar masu jiran tsammani, make kafada Ridwan ya yi yana saukowa daga kan matakalan step din cikin dan sauri saurinsa haka ma Mansur din.

Dai-dai saitin da kujerar Madina yake nan ya tsaya yana kallon Mamy, cikin ban girma da ladabi yake gaishe ta, kana ya gaida Madina da ta juyo tana washe masa hakora har hakoran makkah da ke tsakiyar hakoranta ya bayyana, cikin hanzarinta ta amsa gaisuwar su, cike da iya bariki da son tabbatarwa da aikin Malam ta ce.

" Yawwa Rid yau ina zuwa haka na ga kamar kana cikin farin ciki duk da fuskar ka bata nuna ba amma kuma alamu sun nuna " ta karashe zancen cikin yauki.

Daga Ridwaan har Mansur kallon juna suka yi, Ridwan kallonta yake na siraran sakannni kana ya yi saurin fadin.

" Kullum cikin farin ciki nake ina ga kece dai ba kullum kike farin ciki ba, kuma Mama Madina kamar kin shiga cikina kin gano kamar ina da maganar da zanyi wa Mamy ". ya karashe zancen tare da kai dubansa a kan Mamy.

" Yawwa Mamy ina da kyakkyawan albishir da zan miki cikin yan kwanakin nan dan haka kawai ki fara shirin yin wannan surprise din " ya karashe zancen cikin tattabarwa.

" Ikon Allah " cewar Mamy. Ta kara da fadin.

 " Ridwan fada min mana tun yanzu in fara farin ciki" ta karashe zancen cikin shock.

 Ridwan kallonta yake yana kallon Mansur kana ya kai dubansa a kan Madina da ke fari da idanu tana kwarkwasa.

Kwabe baki ya yi yana jero tsaki akai akai.

" Mamy ki dai yi hakuri ai tunda na ce zan fada miki ke dai sha kurumin ki, sannan daman ina son in tambayeki cikin abokan abbana dan Allah ko kinsan Dr Abdullahi Malumfashi ".

 Cikin tsananin tashin hankali da fargaba Mamy ta ce.

" Alhaji Abdullahi kuma? ai. . . . wan. . nan. . . mutumin dan uwan. . . . . " girgiza kai ta yi tana rufe idanunta hoton Alhaji Abdullahi ke mata gizo a fuskarta. Cikin hanzarin ta bude idanunta ta sauke su a kan Ridwan, dan Mansur fita ya yi domin ba su wuri su gana da Mahaifiyarsa.

" Aaa Ridwaan ban sanshi ba" cewar Mamy cikin rawar murya.

Ridwan yanda ya ga tsoro tattare da ita ya sanya shi fesar da numfashi, kana yana kallon yanda tafukan hannayenta ke rawa.

duk ta fita hayyacinta.

Kauda zancen ya yi ta hanyar fadin.

" Mamy sai de na dawo dafatan su Anisa suna lafiya, Faisal kuma ya same ni wurin aiki ". ya karashe zancen tare da barin falon cike da izzarsa, tafiya yake tunaninsa da komai ya tattaru a kan son gano me Mamy take boye masa.  

Mamy tana ganin fitar Ridwan cikin hanzari ta yi hanyar dakinta, Madina ganin haka take mata baya ta yi dan ta san ba lafiya.

Tana shiga dakin iske Mamy ta yi tana kuka iya karfinta hawaye ne ke bin kuncînta, murya na rawa ta ce " kina jin tambayar da Ridwaan yake min ina ya san Dr Abdullahi, a ina ya hadu da shi " kama hannun Madina ta yi tana sheshekar kuka cikin kuka da tsoro ta ce.

" Madina ni da ke mun san waye Alhaji Abdullahi dan girma Allah kin bincika min inda za mu samu adress dinsa" ta karashe zancen tana safa da marwa cikin dakin.

Madina kam sosai take kwantar mata da hankali tare da nuna mata in Allah ya yarda zata samu informations a kan Dr Abdullahi.

Ridwaan ba su zarce ko ina ba sai gidan Mamy, tun a hanya su kalura kamar akwai motar da ke bin bayansu, hakan ya sa Ridwan yin taka tsantsan har suka iso gidan su Mansur lfy.

Suna parking motocinsu kai tsaye sashin Mamy suka nufa, ko da suka karasa babu kowa falon hakan ya sa shi da Mansur suka zarce za su shiga dakin Mama, cikin hanzari Ridwaan ke fadin kamar fa Abba ya dawo, dan ga takalminsa kofar daki " ya yi furucin yana dage gira.

Mansur cikin fara'arsa ya ce" wallahi shi ne ya dawo  ba suke nan surprise ya mana  ba suke nan shi ne ya ce yau yana son mu sanya kaya iri daya ".

Ridwan murmushin gefen baki ya yi cikin hanzari ya ce.

" aiko mu shiga daga ciki dan mune za mu fara zantawa dashi kafin Mama " cewar Ridwan cikin jin dadi.

Ƙoƙarin shiga dakin suke ya yi daidai da isowar Amatullah falon hannunta ɗauke da trey din lemukan kwali.

Ta sanya idanu a kan Ridwan ta fara zazzare idanu tana komawa da baya baya, hannunta na rawa, cikin zafin nama take shirin yin reverse, ta ji kakkausar muryansa cikin ɓacin rai yana fadin. . . . . .

Saura page daya free page ya kare in sha Allah hanzarta ki biya kudin ki.

Taku har kullum Kyauta daga Allah

[10/25, 10:09 PM] Kyauta Daga Allah: https://chat. whatsapp. com/KgIV8gvcWZi7LcGiwtpDPa

Makauniyar Shari'a

 Sai a Lahira

 NA

 IKILIMA ADAM

 Kyauta daga Allah

 

 09069080725

Last free page, fage na karshe, hajiya ki hanzarta biyan kudin ki, daga yanzu baki sake ganinsa yana tradin sai de na sata, domin biyan naki tura kan wannan asusun banki.

3115484026 ikilima adam First bank ki turo shaidar biyanki a kan wanyannan numbobi da ke kasa

09069080725 ko + 22953726162 ta whsap kaɗai za ki iya samuna

Jarumai writ associations

SHAFI NA ASHIRIN DA BIYAR

Ta ji kakkausar muryansa cikin ɓacin rai yana fadin.

 

 " Keee!!! " dakata cikin dan daga murya.

 Cak ta tsaya jikinta na bari kamar mazari, kasa juyowa ta yi dan tsananin tsoron hada idanu da shi, shi kuwa kallon Mansur yake da shi din ma shi yake kallo kana ya dan saisaita muryansa cike da takaici ya ce.

 " Ina za ki je da wannan trey din hannunki, kuma ɗan rashin ido ba za ki gaishe mu ba saidai ki juya kamar kinga dodanni " ya karasa zancen yana fesar da numfashi.

" Calm down abokina, Please wanna fa yarinya ce, harda rashin sabo damu da bata yi ba, kuma fa kar ka manta matarka ce a halin yanzu ya kamata ka sassauta fushin ka akanta " cewar Mansur cikinsanyin murya.

 Kallon Mansur yake yana sauke ajiyar zuciya, ɗauke kallon ya yi daga kanta tare da yin karamin tsaki, ganin duk abin da ya mata be sa ta gaishe su ba. Hakanan cike da takaicin ta da daukan alwashin gyara mata zama suka kama hannayen juna shi da Mansur tare da zarcewa dakin Abba.

Ita kuwa tana ganin sun shige soma sauke ajiyar zuciya take akai akai, kana tana kallon takalmansu da suka cire, cikin takaici da ma bata san ta iya fada ba, kila hakan ya samo asali ne da zaman da ita da Papy su kaɗai suna rayuwa cikin jejin Allah.

Ta tabbatar tana tsoronsa amma yau kam tana jin zata iya rama abin da ya mata, cikin hanzari da sauri saurinta ta kai trey din kan dinner table ta ajiye, gyara tsayuwarta ta yi tana tunanin yanda za ta yi ta rama wannan cin fuskar da ya mata, cikin dabara da karfin hali tunaninta ya zo a kan takalminsa da ke bakin kofar Abba, cikin hanzarinta ta karasa tana kallon takalmin da ya cire sai sheki yake yana shainin, murmushin gefen baki tayi, babu tunanin komi a ranta, ta sanya hannayenta duka biyun ta ɗauke takalminsa kafa daya tabar daya, tana ɗaukewa cikinsaurinta ta nufa conpound din Gidan, inda shuke shuken fulawa masu ban sha'awa, nan ta dan zauna cike da dabara dan kada mai gadi ya ganta ta ajiye takalmin ta ficewarta sadaf sadaf kamar wata munafuka.

Cen cikin dakin abba, Mansur da Ridwan, firan yaushe gamo suke yi inda gefen su Mama ce zaune cikin adon kasaita sanye cikin tsadaddan leshi mai daukar idanu, yellow color, Mansura ce zaune kasan carpet tana hadawa abba kayan break, duk abin da take sam hankalinta yana kan Ridwan da ke murmushi yana fira da Abba cike da jin dadi, a zuciyarta fadi take " ina ma ace yau din nan an daura mun aure da shi " jin muryan Mama tana fadin ya kamata Amatullah ta zo ta gaida abba ya sa Ridwan kwalalo idanu waje yana ciza labbansa. Mansura da ta gama hada komi cike da jin dadi ta ce " aiko wallahi gwamma ta zo dan yarinyar akwai nutsuwa sam babu ruwan ta da yawan magana " ta karashe zancen tana kallon réaction din Ridwan, shi kuwa lumshe idanu ya yi tare da mikewa tsaye dan be son ya kara yin tozali da ita a dakin abba, yana tashi Mansur ma ya tashi dan akwai ayyuka gabansu, cike da girmamawa su kayi wa Abba sallama kana suka kama hanyar fita daga dakin.

Mansura har ta mike zata bi sahun su, Mama na fahimtar haka cikin hanzari ta dakatar da ita ranta a ba ce, ganin abba yana wurin ne ya sa bata yi magana ba.

Ridwan cike da zallan mamaki yake kallon takalminsa kafa daya babu ɗaya a iya saninsa babu kananan yara a gidan bare ya yi zargin sune, babu wacce ta fado masa a rai sai Amatullah dan me aikin gidan dattijuwa ce, ya san aikin yara irinnsu Amatullah ne, ko ta yi kwallo da takalminsa wajen rawan kai, hakaɗai yake sakawa da kwancewa.

Mansur da ke mamaki ta yanda hakan ta kasance cike da kulawa ya ce.

 " Ko dai Amatullah ta share wajen nan ne?" ya yi magana yana yan dube dube.

 " Ba mamaki " cewar Ridwan rike da kugunsa yana huci sama sama abin da ya tsana a rayuwarsa shi ne jira.

" Amatullah !! Amatullah !! muryan Mansur ke ta shi da dan karfi.

Amatullah da ke zaune wani irin faduwar gaba ta ji, ta san tatsuniyar gizo bata wuce na koki, cikin hanzari ta tashi nan da nan ta ji tsoro ya lullube ta, jiki babu kwari ta ta shi domin zuwa inda ake nemanta.

Mansur jin takun tafiyar ta, hakan ya sanya shi yin shiru, dukansu ba za idanu suke ganin ta inda zata bullo. Ridwan da ke cike da ɓacin rai inuwar Amatullah ya hango tana tafiya sanda sanda nan da nan ya gane ta san abin da ake kiranta a kan sa. . .

 Koda ta karaso cikin barin jiki take fadin " gani " tare da dan matsawa gefen Mansur dan gani take Ridwaan yana iya daukar hannu ya bige ta a yanda taga yana mata wani irin kallo me cike da tuhuma.

 " Yawwa Amatullah ina takalmin Ridwan kafa daya ko dai kin share baki sani ba " ya yi mata tambaya tare da kafeta da idanu.

 Zazzare idanu ta yi cikin tsoro ta ce.

 " Ni fa ban yi shara ba, ban ma san in da ya ajiye ba, ku duba ko yana cikin dakin da kuka fito" ta karashe zancen tare da sauke idanunta kasa.

Mansur na jin haka har cikin dakin Abba ya koma yana ta dube dube, gayawa Mama da Abba ya yi suna neman warin takalmin Rid ya sa su ma suka taya shi yan dube dube har bayan kofa da kar kashin gado sai da Mama da Mansura suka leka, Abba fitowa daga dakin ya yi domin taya shi dubawa ko Allah zesa a gani a nan falon kicibus ya yi da Amatullah da kanta yake kasa, tana jin motsin fitowa daga daki, hakan ya bata damar dago kai tana kallon abba da ke tsaye gabanta, murya na rawa ta gaishe shi tare da kara sauke kanta, shikuwa Abba gabakida ya rikice lokaci daya daga kallon ta nan da nan ya fara zazzare idanu exactyl yarinyar ta yi kama da kanwarsa, kallonta yake na wasu dakiku, Ridwaan da mamaki yake kallon yanda Abba ya tsurawa Amatullah idanu babu kifatwa, ganin kallon ya yi yawa ne ya sa fadin.

" Abba zan sanya takalmin Mansur, kila yara ne suka tura lungu" ya karashe zancen yana ji fan Amatullah da kallon za ki sani ne "

Amatullah tsorone ya kamata dan tunda take ba'a taba mata kallo me ban tsoro irin wanda ya jefe ta da shi ba.

 Abba cikin jin dadi yake fadawa Mansura ta yi maza ta dauko takalmin Mansur dai-dai da irin wanda Ridwan din ya rasa kafa daya, Mansura kuwa cike da zumudi ta tafi dauko takalmin, Abba kallon Amatullah yake a karo na barkatai kana cikinsanyin murya mai daɗin saurare ya ce.

" Mansur ko wannan ita ce bakuwar gidan namu, a ina kuka samo ta " ya karashe zancen yana kallon ta.

" Abba zan maka bayanin komi yanzu muna sauri ne " cewar Mansur yana taune lip dinsa

 Kar kada kai Abba ya yi

 ya kara da fadin. .

" Yawwa yan mata ya sunan Mahaifiyarki da abbanki" ya yi tambaya yana kar kada kai.

Amatullah kuwa gyara tsayuwa ta yi cikinsanyin jiki ta ce " ni ban da mahaifiya haka aka gayamin, sannan mahaifina shi ne Papy" ta karasa zancen murya na rawa.

Nan da nan idanun abba ya kawo ruwa sosai jin wai bata da mahaifiya hakan ya tabo masa raunin da ke cikin zuciyar sa. Nan da nan muryansa ya canza cikin karyewar murya ya ce.

" Daman akwai wacce bata da mahaifiya ne? ai babu amma kuma da na so in ce wani abu amma bari mu samu zama da Ridwaan za mu tattauna" ya kai karshen zancen cikinsanyin murya.

Ridwan sosai yake nazartan kalaman Abba, barin wani tunanin ya yi tare da sanya takalman da Mansura ta dauko masa, cike da yauki ta ajiye agabansa, be bata lokaci ba wajen sanyawa tare da yi wa Abba da Mama sallama shi da Mansur.

Amatullah kuwa sosai ta ji dadin hakan, tana ganin fitarsu ta fice daga falon.

 

Bayan kwana uku da Ridwan zaune tsakiyar falon dakinsa, kallon TV yake da dukan alamu ya yi nisa acikin kallon da yake, daga shi gajeran wando da riga yar shot a jikinsa, kafarsa daya ya daura kan center table din, gabansa kuwa ruwan faro ne da lemun kwali da kofin glass, da cake, yana kalo ya dan taba cin cake din, jin karar bude kofar ya sa shi kai dubansa a kan me shigowa, da mamaki beyi zato ko tsammani ba, yaga Mamy da Madina sun shigo dukansu sanye cikin doguwar riga kala daya, ganinsu ya sanya shi ɗan gyara zaman sa tare da sauke kafarsa kasa, kallonsu yake kallon mai tarin tambayoyi, Madina samun wuri ta yi ta zauna tana mai kallon Ridwaan cikin idanu, shi ma ita yake kallo da mamaki, ganin Mamy ma ta zaune kujerar kusa da Madina ya sanyashi ajiye remote din da ke hannunsa yana mai tattaro nutsuwarsa a kan su.

Madina cikin rawar murya da mamaki ta ce.

"Ridwan muna ta jin jita jitan wai ka daura aure da wata yarinya, abun ya ba mu mamaki matuka da muka musa a kan ba gaskiya ba ne, shi ne aka ba mu wannan katin da ke hannuna kuma a katin sunanka nan baro baro a ciki, shi ne dalilin zuwan mu ba tare da neman izini, dan mu sanar maka anacen ana karya da sunanka cikin gari, kayi gaggawar daukar mataki" ta kai karshen zancen tana kallon Mamy da ke kar kada kai cikin damuwa.

 Kallon Madina yake tare da dan sanya yatsar sa daya a baki yana kara nazartan yanayinsu daga ita har Mamy, sauke ajiyar zuciya ya yi kana cikin halin ko in kula da maganganun su ya ce.

" Aure na daura" ya yi furucin idanunsa na kan Tv.

 " Kamarya aure ka daura Ridwan kasan abin da kake fade kuwa? " cewar Madina cikin rawar murya, Mamy ce ta karbi zancen daga bakin Madina tare da fadin.

 " Ridwan ban son shashanci ni mahaifiyarka ce taya zaka bada amsa gatsai a gabana babu kunya ko shakka" ta idasa zancen cikin fada.

 Sauke idanunsa kasa ya yi cikin dacin rai ya ce.

 " Mamy so kike na miki karya? aure fa nace na daura kuma aurennan daura min akayi ba ni nayi zabi ba, kuma ku shirya nan da juma'a taro dan dayan shashina da kika ga ana gyara a nan zata tare ko ince za mu tare, Mamy tunda aure nayi ai ba aikata haramci nayi ba " ya karashe zancen yana taune lip dinsa.

Wani Uban zufa ne ya karyowa Madina dukan sansan jikinta, cikin rudewa Madina ta ce

" Ridwan wannan wacece ita da ta samu zama matarka cikinsauki haka ba tare da shan wahala ba" ta karasa zancen tsananin rudewa.

" Mai rabo " shi ne amsar da ya bata kana ya yi shiru, yana mai daukar wayarsa da ke kan center table.

 Mamy a zafafe ta ce"

 " Ridwan mu ne kake fadawa me rabo ce ta aure ka daman ana aure babu sanin iyaye, yanda kayi auren nan ban sani ba, yanzu kuma zan baka umarnin kayi maza ka warware auren nan " cewar Mamy cikin fada.

Kallon kallo suke wa juna shi da Mamy

Bari mu waiwaya Cotonou ganin yanda Shari'a zata kaya tsakanin Isah da Sharifai da A'isha

Kowa ya hallara a kotun har alkali da ke zaune cikin shigarsa alkali

Yasmin da su Fauziyya kowannen zuciyoyin sakawa da kwancewa yake a kan yanda zata kaya a wannan zaman.

Me gabatarwa ne ya tashi cikin ban girma yake fadin

" ya mai girma mai Shari'a a yau Litinin ne za'a mu cigaba da sauraren karar Alhaji Isah sharifai da Uwargidansa A'isha" ya kai karshen zancen tare da kai file gaban Alkali.

Alkali gyaran murya ya yi cikin dattako ya ce.

Lauyan me kara " Bismillah" ya yi magana cikin tsare gida.

Lauyan me kara ne ya tashi yana mai hararan Barister Hadiza da ke kallonsa .

Kana cikin shu'umin murmushi gefen baki ya tashi tare da gabatar da kansa, ya kara da fadin

" Ya mai girma mai Shari'a ina son A'isha ta fito gaban kotu dan amsa min wasu tambayoyi " ya karashe zancen yana mai kallon A'isha da ta mike tsaye.

Alkali cikin hanzari ya ce.

Aisha Bismillah " ya karashe zancen yana mai cire gilashin da ke fuskarsa.

A'isha cikin kuzari da hanzarinta ta karasa inda ake tsayuwa a kotun, kana ta tsaya cikin takaici da bakin cikin da take ji ba zata iya yafewa Isah da Basma ba.

 Barister Sani ne ya karasa gaban A'isha cikin takunsa mai daukar hankali, yan zaman kotun, Isah Sharifai da Matarsa murmushi suke ganin A'isha zata amsa tambayoyi masu zafi daga bakin Barister Sani.

Barister Sani cikin tsara kalamai ya ce. . . . . …

Kuyi following dina a arewa book a kan wannan sunan (kyautadagaAllah10) pls masoyana mu hade acen za ki samu complete din Makauniyar Shari'a.

Duka a nan ne na kawo karshen free page din Makauniyar Shari'a

Me son cigaba ya neme ni a kan 09069080725 ko + 22953726162 ta Whatsapp kaɗai ban da kira.

Dari biyar kacal

3115484026 Ikilima Adam First Bank

Tura shaidar biya a kan wannan lambar (09069080725) ko kuma kati kuna iya turawa ta wannan number.

Siyen nagari mai da kuɗi Gida

Jarumai writ association marubuta masu aiki da jarumta wajen Fadakar da Al'umma. 📚📚


Post a Comment

0 Comments