Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Sanya Rawani

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin mene ne hukuncin sanya Rawani a Shari'ance, Sunnane kokuma Al'adace kawai??

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alal-Haƙīƙa yā tabbata acikin Hadisai ingantattu cewa Mαиzoи Aʟʟαн() Yanā sanya Rawanī akansa, to Saidai Mālamai sun yi Sāɓāni Shin sanya Rawanī Sunnace da za ayi koyi da'ita kokuma Al-ādāce? Mafi yawa daga cikin Mālamai suntafine akancewa sanya Rawanī yana da cikin Al'ādu na Lārabāwā tunma kāfin a aiko Aηηαвι(), danhaka acikin al'ummar da Mαиzoи Aʟʟαн() yatāso acikinsu suna da al'ādar sanya tufāfi kamar irin su:

  Rīgā,

   Hūlā,

   Zane,

    Mayāfī,

     Rawanī,

      Alkyabba,

Dukkan waɗannan tufāfine da Lārabāwā suke amfāni dasu awancan lokacin, shi ya sa da Aηηαвι() yatāso acikinsu shi ma yake amfani dasu, kuma da Muslunci ya zo bai hana Mutāne suci gaba dayin amfāni dasuba, danhaka Aηηαвι() yana amfani dasune amatsayin kayansu na al'āda, kuma bābu wani Hadisi ko da guda ɗaya ingantacce da Mαиzoи Aʟʟαн() yanuna cewa wanda yaɗaura Rawanī yanada wani fifikon lāda a kan wanda bai ɗauraba, domin dukkan Hadisan da sukazo a kan falalar sanya Rawanī ba su ingantaba, Sannan Mālamai sukace idan da za ace sanya Rawanī Sunnane saboda kasancewar Aηηαвι() Yāsa, to sai ace ashe ke nan namiji yaɗaura Zane haɗe da mayāfi shi ma Sunnane, domin dukkansu Mαиzoи Aʟʟαн() Yāyi amfāni dasu,

 Wato dāma asali a Shari'ance dangane da abin da yashāfi sanya tufāfi shi ne, anāsone Mutum yarika sanya irin tufāfin da al'ummar dayake cikinta take amfāni dasu matuƙar dai ba su Sāɓāwā Shari'ah ba, kuma Mαиzoи Aʟʟαн() yāyi hani Mutum yasanya tufāfin da zaifita dabam acikin jama'ar dayake tāre da'ita, Misali kamar a Ƙasar-Hausa aga wani yāɗaura Zane da Mayāfi ajikinsa yanā yāwo dashi, sabod gālibin tufāfin Hausawā zāka sāmu kodai babbar riga da jampa da hula da Rawanī kokuma doguwar riga da wando da makamantansu, tare dacewa awata Ƙasar ko awata Ƙabilar za aga cewa ɗaura Zane ko ɗaura mayāfi yana daga cikin tufāfin Mazā, haka nan awasu Ƙasashen akwai waɗanda bāmā Musulmai ba ne amma za aga suna sanya Rawanī saboda yanā cikin al'ādunsu,

Danhaka magana tabbatacciyā kamar yada Mālamai sukayi bayāni ita ce, Sanya Rawanī ba Sunna bace Al'ādāce, domin kowacce irin Al'umma ko Ƙabila sunada nāsu irin tufāfin na al'āda dasuke amfāni dasu, danhaka abin da yake a Sunnah shi ne Mutum ya siffantu da irin tufāfin Al'ummar da yake tāre da'ita matuƙar ba su Sāɓāwā Shari'ah ba,

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

AMSAWA:

   Mυѕтαρнα Uѕмαи

    08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu. . .

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp. com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www. facebook. com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋��𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t. me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments