Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Kwana A Daki Ɗaya Da Yara

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Shin Wai Babu Kyau Kwana Da Yara Aɗaki Ɗaya, Kuma Bai Halatta Sukwana Aɗaki Su Kaɗai ba Koda An Musu Addu'a.?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

الحمد لله أدبنا بالأخلاق الفاضلة.

Kwana ɗaki ɗaya dayara ko yaro wanda baya iya ban-bance komai kamar yaron da'ake shayar da shi ba a samu wani umarni na shari'a akai ba, babu wani hadisin Annabi akan hakan, sai wani asar kwaya ɗaya wanda ba hadisi bane, maganace aka ruwaito daka wasu daka cikin magabata daka cikin malikiyyah, wacce suka dogara da ita daka Umar bin khaddab yardar Allah takara tabbata agareshi, yaka sance idan zai yi jima'i da iyalinsa yana fitar da jariri daka ɗaki, dankaiwa makura wajan kunya da suturce kai, amma ba bayanine na hukuncin shari'aba, ko Umarnin da'aka dorawa mutane, babu laifi koyi da shi gawanda yakesan hakan, kuma gidansa akwai yalwa, baya kuma tsoran wata cutarwa gayaron idan yabarshi aɗaki shi kaɗai batare da yana ganinsa ba, amma lazimtawa mutane koda yaushe, bai halatta.

Yazo acikin mausu'ah fiqhiyyah ( 3/178)

" Wajibine mutum ya suturta daka yaro mai iya gane abu aɗakinsa shida matarsa, ko baiwarsa, ko waninsu kada sugansu, kada suji alamun abun da suke aikatawa, haka mafiya yawan malamai sukace.

An tambayi hasanul basari rahimahullah game da wanda yake da mata biyu agida ɗaya, ya ce: Magabata yana nufin sahabbai sun haramta yasadu da ɗaya daka cikin matan nasa ɗayar tana gani ko tana ji.

Malikiyya sukace: Ya suturta daka samuwar mai bacci aɗaki, bai halatta mutum yasadu da matarsa ko baiwarsa aɗakin da akwai wani acikin ɗakin, idansa biyu ko yana bacci, domin mai bacci zai iya farkawa yagansu awannan halin.

Mutum yasuturta daka samuwar yaro karami aɗaki, koda baya iya gane abubuwa koyi da umar ɗan khaddab, Umar yaka sance yana fitarda da yaro karami daka ɗaki idan yana san jima'i da iyalinsa.

Jamhurdin malamai suntafi akan cewa basai mutum ya suturta daka yaro karami wanda baisan komai ba, harda wasu daka cikin malikiyyar, saboda abun dake cikin hakan na wahala da takura, " madkal" Na ibnul haaj Almaliki ( 2/184).

Ibnu Usaimin acikin sharhin mumti'i(5/380) bugun misra ya ce:

" Abun da yake sahihi awananna mas'alar shi ne: haramunne saduwa wani yana gani, saidai idan mai kallan yarone wanda baisan me akeba, kuma bazai iya suranta maiya gani ba, wannan babu laifi, amma idan zai iya sifanta abun da yagani, bai kamata ayi jima'i yana ɗakin ba koda yarone, domin yaro yana iya fadar abun da yagani batare da ya nufaci fadar ba.

Amma wanda ake shayarwa wanda yake da wasu watanni, wannan babu laifi, domin shi baisan abun da akeba, saidai wanda yake da shekara uku, ko huɗu, bai kamata mutum yasadu da iyalinsa yana ɗakin ba, domin yaro dasafe yana iya bada labari.

Saboda haka aka haramta saduwa da iyali yaro na gani, koda baya iya ban-bance abubuwa, idan yana iya sifanta abun da yagani, kuma yana iya fahimta.

Saboda haka kwanciya dayara aɗaki halal ne, baya zama haramun ko abun zargi, sai in mace da mijinta za su biya bukatarsu, anan haramci ke shiga, shi ma sai idan yaron yakai yana iya gane me suke aikatawa kuma zai iya bayyana yanda yaga sunayi, anan kwana ɗaki ɗaya dayara ke zama abun zargi.

Amma dan kwanciya dasu haka siddan kamar mahaifinsu baya nan ko bamai zaman gida bane, babu laifi uwa takwana da 'ya'yanta mata aɗaki ɗaya koda suma sun balaga.

Cewa bakyau abar yara su kwana aɗaki su kaɗai koda an musu addu'a wannan kuskurene, babu wata aya ko hadisi ko maganar wani magabaci akai.

WALLAHU A'ALAM

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments