Ticker

6/recent/ticker-posts

Babu Zaman Lafiya Tsakanina Da Mijina

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Assalamu alaikum malam ina jin daɗin nasiharku Allah ya qara wa malam basira da lafiya. Malam wallahi ina cikin damuwa da rudani, ni da mijina bama zaman lafiya se ya zama yana zargina, ni kuma da naga haka sai na gaya wa qanwar mahaifiyata ta kaini gurin wani malami akatsina. Saboda wallahi malan alokacin zuciyata se na ji bana son zama da shi nacewa malamin ya raba mu. Ya ba ni wasu takardu ya ce insa wani a masai wani kuma in kona duk nayi, Kuma muka rabu yaranmu biyu da shi kuma Walahi malam bayan mun rabu abun ya dameni naso yadawo amma Allah be qaddara ba, ina cikin jimami se wani bawan Allah ya kirani dana ganema manufarsa akaina nace masa ina cikin idda kar yaqara kirana amma se yake turo min da kati, ya zo yana ba almajirin gidanmu sako yana kawowa aba ma 'yata duk ina cikin idda. ka san rauninmu nikuma se na fara daga masa waya muna magana kafin in gama idda har munyi maganar aure. Da na gama idda aka sa mar sadaki aka ɗaura mana aure. malam bari intaqaice maka labari shi ma Tun da mukayi aure babu kwaciyar hankali Malam. meye matsayin aurenmu?. Gaskiya malam labarin metsawo ne yanzu haka muna kotu da wannan sabon mijina kuma wallahi ba don Kuɗinsa ya sa na aureshi ba. asali ma tsohon mijina ya fishi sukuni. Wannan kwatakwata bai da kishi, be san hakkin iyalinsa ba. Matarsa tana yin abun da taga dama bai iya yimata magana ga rashin kula da iyali. Ina zargin kaina saboda abun da na aikata malam dan Allah meye abunyi? inata istigfari mlm ka taimakeni wallahi ina cikin damuwa.

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Wa alaikis salam wa rahmatullahi wa barakatuhu.

Tabbas ke kin aikata kurakurai masu yawa acikin wannan abin da ya faru. Tun daga zamanki agidan mijinki na farko, zuwa wannan na biyun:

1. Aikata abin da zai kawo zargi azuciyar mijinki.

2. Rashin neman hanyar da zaku daidaita dashi.

3. Zuwa wajen malamin duba.

4. Jefa ayoyin Alqur'ani acikin Masai.

5. Shirya maganar aure tun baki kammala iddah ba.

6. Rashin zaman lafiya da Mijinki na biyu.

7. Kaiwa Qararsa kotu.

Waɗannan laifukan gaba Ɗayansu manya ne. Amma Kaba'irori daga ciki sune zuwanki wajen boka, yarda da abin da ya fada, da kuma jefar da Takardar nan acikin Masai (shadda). Sai kuma shirya maganar aure acikin iddah.

Watakila wasu laifuka kike aikatawa irin na zargi, shi ya sa har Mijinki na farko yake zarginki ɗin. Sannan zuwa wajen boka, Manzon Allah ya ce: "DUK WANDA YAJE WAJEN BOKA KO ƊAN DUBA, KUMA YA YARDA DA ABIN DA YA FAƊA, TO HAKIKA YA KAFIRCE MA ABIN DA ANNABI MUHAMMADU ya zo DASHI". (Muslim ne ya ruwaito).

To kinga anan kalmar kafircewa ta hau kanki. Sannan kuma jefa takarda acikin Masai, wacce watakila tana kunshe da Basmalah ko kuma wasu ayoyi na Alqur'ani, Shi kam kafirci ne tsantsa.

Malamai sun ce duk wanda ya wulakantar da Alqur'ani ko kuma wani sashe daga gareshi da gangan, to wannan ya kafirta, ya yi ridda.

Hakanan shirya maganar aure acikin lokacin iddah, ana kirga wannan acikin manyan laifuka. Watakila alhakin waɗannan manyan laifukan ne ya janyo miki rashin samun dacewa acikin sabon auren da kikayi.

Shawarar da zan baki anan ita ce:

1. Ki tuba zuwa ga Allah (SWT) cikakkiyar tuba irin wacce Allah yake so.

2. Ki gyara halayenki yadda zaki iya zama lafiya da kowanne Miji.

3. Idan da hali kije ki nemi yafewar Mijinki na farko ɗin nan domin hakika kin chutar dashi.

4. Ki dena yawan yin shawara da 'yan uwanki mata. Musamman wannan Qanwar mahaifiyarki ɗin nan. Domin lallai za ta rika jefaki acikin hallaka ne.

Daga karshe muna yi miki fatan Allah ya gafarta miki damu baki ɗaya. Allah ya daidaita miki lamuranki. Ameen.

WALLAHU A'ALAM.

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments