Ticker

6/recent/ticker-posts

Hukuncin Yin Sallama Ga Wanda Yake Karatun Alkur'ani Ko Yake Cin Abinci

𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀

Mecece gaskiyar magana game da cewa wai ba a yin sallama ga mutumin da yake cin abinci ko yake karatun Alƙur'ani?

𝐀𝐌𝐒𝐀❗️

Alalhaƙiƙa sallama wani abu ne mai ƙima da kuma daraja a tsakanin 'yan'uwa musulmai, shi ya sa shari'a take kwaɗaitar da mu cewa mu riƙa yaɗa sallama a tsakanin mu, domin yawan yaɗa sallama yana ƙara soyayya da ƙauna a tsakanin 'yan'uwa musulmai kamar yadda Mαnzon Allαh() Ya ke cewa:

"لا تدخلوا الجنة حتي تؤمنوا، ولا تؤمنوا حتي تحابوا، أولا أدلكم علي شيء إذا فعلتموه تحاببتم؟ أفشوا السلام بينكم" (رواه مسلم)

MA'ANA:

(Annabi() Ya ce:) ba za ku shiga Aljanna ba har sai kunyi imani. Kuma ba za ku yi imani ba har sai kun ƙaunaci junanku. Shin ba na shiryar da ku zuwaga abin da idan kun aikatashi zai sa ku riƙa son junanku? Ku yaɗa (ku yawaita) sallama a tsakaninku:

Sannan kuma kamar yadda shari'a ta tabbatar da cewa fara yin sallama Mustahabbi ne amma kuma amsa ta wajibi ne, danhaka ke nan wanda ya fara yin sallama to ya fi wanda ya amsa ta yawan lada, shi ya sa Malamai sukace a cikin dukkan ayyukan Ibada duk abin da yake farilla ne ko wajibi to ya fi yawan lada akan wanda yake sunna ne ko kuma mustahabbi, to amma a ɓangaren sallama sai ya kasance mustahabbi ya fi farilla yawan lada.

Amma dangane da hukuncin yin sallama ga mai cin abinci ko karatun Alƙur'ani, an samu wasu daga cikin Malamai da suka ware waɗansu abubuwa kamar guda (14) ko sama da haka waɗanda suke ganin cewa makaruhi ne a yiwa Mutum sallama idan ya kasance a ɗaya daga cikin waɗannan abubuwa kamar haka:

1-Idan Mutum yana cikin cin abinci ko kuma wani abin sha.

2-Idan Mutum yana cikin yin zakiri kamar hailala, tasbihi, ko kuma karatun Alƙur'ani.

3-Idan Mutum ya shagaltu da karanta Hadisan Mαnzon Allαh() sukace shi ma makaruhi ne a yi masa sallama.

4-Idan Mutum yana cikin yin wata lakca ko tunatarwa.

5-Idan Mutum yana cikin karantarwa ko yana ɗaukan darasi kamar na ilimin Alƙur'ani ko Hadisi ko kuma Fiƙ-hu.

6-Idan Mutum yana cikin yin wani bincike na Ilimi to shi ma makruhi ne a yi masa sallama saboda kada a shagaltar da shi.

7-Idan Mutum yana cikin yin wa'azi ga Mutane.

8-Idan Mutum yana cikin yin muzakara (Mai-maita karatu) na ilimin da yaje ya koyo.

9-Idan Mutum yana cikin yin ƙiran sallah (Azan).

10-Idan Mutum yana cikin yin Sallah.

11-Idan Mutum yana cikin yin Alwala.

12-Idan Mutum yana cikin yin hira da wani mutum shi ma sukace makruhi ne a yi masa sallama don kada a katse shi.

13-Idan Mutum yana cikin biyan buƙatarsa kamar fitsari ko kashi.

14-Idan Mutum yana cikin yanayi na yaƙi da abokan gaba.

To sai dai kuma waɗansu daga cikin Malamai sukace gabaɗayan waɗannan abubuwa da su waɗancan Malamai suka ambacesu babu nassi ko guda ɗaya da suka dogara da shi a kansa wanda yake tabbatar da maganarsu. Danhaka ke nan maganar cewa makaruhi ne ba ta ma taso ba, danhaka waɗannan abubuwa su na nan a asalinsu na halacci (Mustahabbi) domin nassosin da suka zo sukayi magana akan hukuncin sallama (عام) ne

Kuma ba a samu wani nassi da ya yi (تخصيص) Na waɗancan abubuwan ba, sannan Malamai sukace wani Sahabi ya yiwa Mαnzon Allαh() sallama a ya yin da yake sallah, sai Mαnzon Allαh() ya amsa masa amma ta hanyar yin ishara da hannunsa (✋🏽), sai Malamai sukace idan kuwa har za a yiwa Mαnzon Allαh() sallama yana sallah kuma bai hana ba, to (من باب أولي) A yiwa mai cin abinci da kuma mai karatun Al-ƙur-ani sallama.

Danhaka dai magana mafi inganci ita ce ya halatta suma a yi musu sallama:

шαʟʟαнυ-тα'αʟα α'αʟαмυ

 Mυѕтαρнα Uѕмαи

 08032531505

Zauren Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...

𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇

https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G

𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇

Https://www.facebook.com/groups/336629807654177

𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇

https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi

ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ

**************************

Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.

Question and Answers in Islam

Post a Comment

0 Comments