Ticker

6/recent/ticker-posts

Ko da So... (Kashi na 5)

In kin karanta ki yi sharing please

Bayan sallar isha Abba yana zaune a falonsa sanye da tabarau yana duba takardun clearance din kayan su da za su iso nan ba da jimawa ba, Sadiq ya shigo dauke da sallama. Sai da Abban ya amsa shi sannan ya nemi wajen zama ya danyi shiru.

Kallo daya Abban ya yi masa yaga yana cikin damuwa. Ya san waye Sadiq ya san ba kasafai abu yake saka shi damuwa ba. Shi ne dan shi na biyu amma tamkar shi ne babban. Sadiq tun kafin ya kai haka yake da kamala da nutsuwa har ma fiye da mahaifin nasa. Haka kuma bayan Hafsah shi ya fi shakuwa da mahaifin nasa kuma yake da interest akan ko wanne business da mahaifin nasa yake yi banda na makaranta. Ya fi ganewa kasuwancin ma sama da boko duk da ya kammala jami’a da sakamako me kyau. Maimakon ya nemi aiki sai kawai ya nemi a ba shi jari ya fara juyawa.

Ganin haka ne ya saka Abban ya mika masa kula da harkar kasuwancin sa tun da tun yana secondary suke fita kasuwa tare. Babu yadda mahaifiyarsa ba ta yi ba akan zancen bin shi kasuwar saboda tafi so danta ya yi karatu ya zama likita. Abun mamaki gashi dai ya karanci course din da take so amma baya practicing.

“Abba jiya an shigar mana shago amma alhamdulillah ba a abun da aka dauka.” Ya sanar da mahaifin nasa don yau yana zuwa da safe ya lura da an taba wajen.

Nisawa Abban ya yi sannan jijjiga kai alamar abun baiyi masa dadi ba sannan ya ce, “bakomai kar ka wani damu Sadiq. Na san ba sakacin ka ne ya jawo ba. Tun da ma Allah ya sa masu leqe ne ai alhamdulillah. Allah ya tsare gaba.”

“Ameen.” Sadiq ya amsa yana sauke ajiyar zuciya. Ya san Abban dama ba zai taba tuhumar sa ba amma kuma ganin a cikin gidan da kaf kannen Abban da suke manya shi Abban ya zaba ya ba shi amanar shagon sa ya sa ya ji tamkar lefin daga gare shi ne. Shiru suka dan yi kamar ba wanda zai sake magana sai Abban ya mika masa takardun hannunsa.

“Ka adana mun su.” Da hannu biyu ya karba yana kara jin dadi a ransa don ya san Abba ya yi hakan don ya sake karrama shi ya nuna mishi babu komai kar ya sa damuwa a ransa.

Tashi Abban ya yi ya duba dining table ko zai ga abincin sa an ajiye amma wayam. Da ido Sadiq ya bi shi da kallo sannan ya yi murmushi.

“Ai yau sarakan shirita ne a kitchen. Kar ma ka sa ran cin abinci nan da awa guda Abba.” Dariya suka yi a lokaci daya saboda kowa ya san da wa ake yi.

“A’a kar ka yi wa auta ta sharri. Tashi ka tafi, sai da safe.” Da haka Sadiq ya tashi yana dariya sannan ya masa sallama cike da jin dadin yadda Abban nasu yake da saukin kai sosai.

Bayan minti sha biyar sai ga Mummy nan ta shigo da tray a hannunta. Kamar ko yaushe kamshin turaren ta me sanyaya zuciya ya cika falon. Fuskar nan tata a daure alamun ranta ya baci. Sallama ta yi, Abba ya amsa sannan ta samu wuri ta zauna tana shan kunu.

Sai da taga Abban ba zaice komai ba sannan ta yi tsaki. “Ni wallahi na gaji da shirmen yarinyar nan kai kuma ka dage sai an saka su aiki. Ka barni kawai na dauki me aiki da za ta dinga taya su. Hafsah ba za ta iya da hidimar nan ba. Kalli a ce mai gidana guda sai kusan goma zai ci abincin dare?” ta yi tambayar cike da kissa da dabarar son ya barta ta dauki me aikin kamar yadda mata masu aji irinta suke yi ba wai su dinga saka yaransu aikin gidan ba. Kowa tana da mai aiki banda ita.

Murmusawa ya yi. Ya san daman inda zancen ya dosa. “A’a in dai Hafsah za ta koyi aikin gida ko karfe daya aka ba ni abinci ba ni da damuwa. Maza miko min abincin yau a kasa zanci. Abunka da auta ta yi wa babanta girki.”

Haushi ya sa ko tanka shi batayi ba ta tashi ta dauko sannan ta zuba mishi. Fridge dinshi ta nufa ta dauko lemo da glass cup sannan ta kawo ta zuba mishi.

Ganin dai sam bai dauki zancen nata da muhimmanci ba ya sa ta saki fuskarta kadan ta gyara zaman ta a gefen sa.

Tuwo ta yi miyar agushi. Yana kallon miyar ya ji wata dariya ta taho masa amma haka ya rike ta. Watarana sai labari. Agushin ya yi hanya daban, ruwan miya ya ware sai alayyahu batso batso. Bismillah ya yi yana fatan Allah sa kar cikin sa ya baci.

Sai da ya juya miyar ta dan hade ya yi lomar farko. Babu lefi a baki amma a ido kam babu wanda tuwon zai ba shi sha’awar ci.

“Kuma baki ji dadi ba.” Ya fada yana kai wata lomar a ransa yana tunanin irin halin Hafsah wadda kwata kwata ba ta dauko mamanta ba sam. Dama haka Allah yake abunshi.

“Hmmm.” Kawai ta ce ta yi murmushi ganin yana kallonta.

“Yau yan hirar ba sa nan an taba miki miji ko? Toh ba gashi ina cin abincin ba? Haba gimbiya ta ayi min hira mana.” Ya tsokane ta wanda ya sa ta danyi dariya mai cike da raha da izza. Ko a gaban mijinta mace ce da take komai a lissafe.

“Toh yau dai sai ka gama cin abinci zan baka labari. Bari naje na dawo…” ta kalle shi fuskarta kawace da murmushi kafin ta mike tana yanga kamar sabuwar amarya. A hankali ta fice ta tafi dakinta.

***

Zaune Hajarah take tana ta faman karanta littafin Hausan da ke hannunta Mukhtar ya shigo. Sau uku yana sallama amma ba ta ji don ta yi nisa a karatun ta. Sosai take jin dadin littafin Ummu Hani haka ma jarumar sosai ta burge ta.

Sai da ya harareta sannan ya ce, “sana’a ce?” Yana fusge littafin daga hannun ta. A razane ta dago ta kalle shi.

“Haba Yaya da ya yage kuma fa?” Ta turo baki.

“Sai ma na yaga naga me zaki iya yi.” Ya fada yana juyo bangon yaga ko meye a jiki.

Cikin littafin ya duba ya karanta layin farko ya tabe baki sannan ya mika mata.

“Wahalar da kai. Ina Inna?” Ya tambaya yana daga labule ita kuma Hajara ta yi saurin ajiye littafin a gefenta don in ta ci gaba da dubawa sanda yake mata magana tsaf zai yaga shi ba ruwansa da arowa ta yi a wajen yar ajinsu wadda gwana ce wajen karanta littafan Hausa kuma tsabar samun wuri in ta siya littafi sai ka ba ta naira ashirin za ta ara maka na kwana daya. Itama Hajara kudin motar zuwa makarantar ta rage ta yi tafiyar kafa duk dan ta karanta wannan littafin da ake ta zancen sa.

“Taje gidan Kawu.” Girgiza kai ya yi kawai ya san ba komai ne ya kai Inna gidan Kawun ba sai dan kawai ta fada masa cewa Mukhtar ya samu aiki. Ya san halinta sarai.

Wuri ya samu ya zauna ya danyi shiru yana tuno yadda wani mutumi ya ci masa mutunci a wajen kafintan da yake tayawa aiki. Shi ke nan in Allah ya yi ka talaka ka yi ta ganin wulakanci kala kala daga mutane daban daban ke nan ya ayyana a ranshi.

“Yaya yanzu tafiya za ka yi?”

Da farko bai fahimci me take nufi ba ma saboda yadda hankalinsa sam yana kan lissafin yadda zai inganta rayuwarsa da ta yan uwansa ne.

Kwana biyar sukayi suna zuwa orientation da handing over a makarantar wanda shi bai taba jin inda ake haka ba sai akan makarantar nan. Jiya kuma suka kammala zuwa. za su fara shiga aji ne in an koma hutun session wani satin.

“A’a Hajara, ba zan iya biyan kudin shago ba yanzu gaskiya. Jeka ka dawo zan dinga yi kawai ko bakomai ina ganin ku kuna saka ni farin ciki.” Amsar tasa ta yi mata dadi sosai shi ya sa ta yi murmushi me sauti.

Kafin kowannen su ya yi magana wani yaro ya fado cikin gidan ba ko sallama.

“Wai ana sallama da Hajara, inji Garba.” Ya fada. Ras gabanta ya fadi ta sunne kai kasa kar ma yayan ya kalle ta su hada ido.

Ai kuwa da harara yake binta.

“Sai ki ba shi amsa ai.” Ya fada cike da bada umarni wanda ya sa jikinta ya fara rawa don ta san yau da kyar ne in bai da ke ta ba. Ya sha yi mata gargadi akan kula samari tun da ba ta kammala sakandire ba amma ba ta ji. A boye take soyayyar ta yadda ba zai gane ba.

“Kace ba..ba… ba ta nan.” Ta amsawa yaron tana i’inar tsoro da fargaba.

Sai da yaron ya fita sannan Mukhtar ya kalle ta. “Na sha gaya miki kina da zabi. In kin zabi soyayya sama da karatun sai a miki auren ai na dena asarar kudina kamar yadda yayarki ta yi.”

Girgiza kai ta yi hawaye na zuba a idonta. “Wallahi na dena Yaya.” Ta ba shi amsa tana tashi da sauri don tsoro da kunyar sa take ji. Da gaske tana son soyayya amma kuma tana kaunar karatun. Tana kallo yayarsu Bintu iya JSS ta yi aka mata aure saboda shi take so. Yanzu Bintun kamar ma ba ta taba yin karatun ba. Sai aikin gida da yara. Ita ba ta son kalar rayuwar Bintu. So take ta yi karatu me zurfi sannan ta yi auren ko ta kammala sakandire sannan ta yi auren ta ci gaba da karatun.

Burirrika gareta kuma Garba ya ce mata zatayi karatu a gidansa amma tana tsoron yayan ta. Kar ya zare hannun sa akan karatun ta…

Rubutawa

Aeshakhabir

Fadimafayau

Soyayya
Credit: LuckyTD

Post a Comment

0 Comments