𝐓𝐀𝐌𝐁𝐀𝐘𝐀❓
As-Salaam Alaikum
Wa Rahmatul Laah. Miji ne duk lokacin da zai yi tafiya sai ya je gidan wacce ba
ranar girkinta ko kwananta ba don yin sallama. A can ɗin kuma sai ya sadu da ita duk da ya san
cewa ba kwananta ba ne. Haka ma idan ya dawo. Sannan idan matar ta nuna masa ba
haka ake yi ba, sai ya fara fushi. Menene hukuncin wannan a musulunci?
𝐀𝐌𝐒𝐀❗️
Wa Alaikumus
Salaam Wa Rahmatul Laah Wa Barakaatuh.
Al-Imaam Ahmad
da Abu-Daawud da Al-Haakim sun riwaito hadisin da As-Shaikh Sameer Az-Zuhairiy
(Hafizahul Laah) a cikin Ta’aliqinsa ga Buluughul Maraam shafi: 323-324 ya ce:
hasan ne, daga Ummul-Mu’mineen A’ishah (Radiyal Laahu Anhaa) cewa:
وَكَانَ قَلَّ يَوْمٌ إِلاَّ وَهُوَ يَطُوفُ عَلَيْنَا جَمِيعًا فَيَدْنُو مِنْ كُلِّ امْرَأَةٍ مِنْ غَيْرِ مَسِيسٍ حَتَّى يَبْلُغَ إِلَى الَّتِى هُوَ يَوْمُهَا فَيَبِيتُ عِنْدَهَا
Da ƙyar
wani yini ke wucewa face dai Manzon Allaah (Sallal Laahu Alaihi Wa Alihi Wa
Sallam) ya kewaya mu dukkanmu, sai ya kusanta ga kowace mace ba tare da saduwa
ba, har sai ya kai ga wacce ya ke yinin ta ne, sai ya kwana a wurin ta.
Wannan ya
nuna:
(i) Miji yana
iya shiga wurin matarsa da ba ita ce mai girki ba da rana, idan ya yi buƙatar
hakan ba domin bayar da kuɗin
cefane, ko binciken lafiyarta, ko warware wata matsala kaɗai ba.
(ii) Ya
halatta ya yi komai da ita a lokacin shigansa a wurinta, in ban da saduwa.
(iii) Bai
halatta ya sadu da wacce ba kwananta ko girkinta ba a lokacin da ya shiga
wurinta don wata buƙata daga cikin buƙatun da ambatonsu ya gabata.
(iv) Amma idan
tun farko ya samu amincewa da yardar matarsa mai wannan yinin ko kwanan a kan
hakan, to ya halatta.
(v) Malamai
suka ce: Idan da dare ne, bai halatta ya shiga wurin wacce ba kwananta ko
girkinta ba, sai in akwai wata larura mai ƙarfi da ta hukunta hakan.
Don haka, abin
da wannan mijin yake yi a lokacin fita tafiya da lokacin komowa daga tafiyar ba
daidai ba ne, domin ya saɓa
wa koyarwar wannan hadisin a fili ƙarara. Wajibi ne ya tuba ga Allaah, ya
nemi gafararsa, kuma ya nemi amincewar matan aurensa da ya fiyarsu a kan abin
da ya gabata. Sannan kuma ya komo ga bin koyarwar Addinin.
Allaah ya
shiryar da mu gaba-ɗaya
ga abin da yake so kuma yake yarda da shi.
WALLAHU A'ALAM
Sheikh
Muhammad Abdullaah Assalafiy
Zauren
Fatawoyi Bisa Alkur'ani Da Sunnah. Ku kasance Damu...
𝐖𝐇𝐀𝐓𝐒𝐀𝐏𝐏👇
https://whatsapp.com/channel/0029VaA8YpB42DcZdoRuCj3G
𝐅𝐀𝐂𝐄𝐁𝐎𝐎𝐊👇
Https://www.facebook.com/groups/336629807654177
𝐓𝐄𝐋𝐄𝐆𝐑𝐀𝐌👇
https://t.me/TambayoyiDaAmsoshi
ﺳُﺒﺤَﺎﻧَﻚَ ﺍﻟﻠَّﻬُﻢَّ ﻭَﺑِﺤَﻤْﺪِﻙَ ﺃﺷْﻬَﺪُ ﺃﻥ ﻟَﺎ ﺇِﻟَﻪَ ﺇِﻻَّ ﺃﻧْﺖَ ﺃﺳْﺘَﻐْﻔِﺮُﻙَ ﻭﺃَﺗُﻮﺏُ ﺇِﻟَﻴْﻚ
**************************
Wannan ɗaya ne daga cikin fatahowin Musulunci da aka gina su kan Ƙur’ani da Hadisan Manzon Allah (SAW) waɗanda ake samu a shafukan Tambayoyi da Amsoshi na Sheik Malam Khamis Yusuf a Facebook, Telegram, da WhatsApp. Za ku iya bibiyar shafukansa domin karanta ƙarin fatawowi.
0 Comments
ENGLISH: You are warmly invited to share your comments or ask questions regarding this post or related topics of interest. Your feedback serves as evidence of your appreciation for our hard work and ongoing efforts to sustain this extensive and informative blog. We value your input and engagement.
HAUSA: Kuna iya rubuto mana tsokaci ko tambayoyi a ƙasa. Tsokacinku game da abubuwan da muke ɗorawa shi zai tabbatar mana cewa mutane suna amfana da wannan ƙoƙari da muke yi na tattaro muku ɗimbin ilimummuka a wannan kafar intanet.